← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 180

Sashe 164

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan zaro idanu ta yi na jin ya ce wacece kuma Akka da kuma ba zai ji kunyar daddy ba sai Mummynta.

"Yah Rizwan ni kuma na fi jin kunyar daddy a kan Mummy fa". Ta faɗa tana sauƙowa ƙasa daga saman gadon.

"To bana son gimbiyata ta zauna da yunwa, jeki ki ci abinci ki ƙoshi sosai, hirarmu ba zata kare ba, idan kin dawo zan baki wani labari kin ji ko?".

Da okey ta amsa mashi tana ƙoƙarin katse kirar ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa yana faɗin. "I love u my sister, ki kula mun da kanki, i will going to miss this your sweet voice wadda idan kina magana yana sanya na rinƙa jin mamar barci zai ɗaukeni, bana........" Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon shigowar Ramish da Bilal cikin room ɗin nasa.

Ita kuwa jin ya dagata yasa ta mayar mashi da kalmar i love u too tare da katse kiran ta nufi waje.

Kai tsaye dining room ta nufa. A saman kujera kusa da Auta ta zauna, ya zama suna fuskantar juna ita da Yah Jawad É—in, shi kuma daddy da kujerarsa take a gaba yana iya ganin fuskar kowa, a side É—in kujerarsa ce kawai a wajen.

"Meya hanaki fitowa ki ci abinci?". Jawad ya tareta da wannan tambayar.

Gaisuwa ta fara É—agawa daddyn nasu, bayan ya amsa ta gaishe Akka sannan su Momma haÉ—e da Akka, sannan ta bawa Jawad É—in amsa da tana waya ne, da yake bata iya karya ba, amma bata gaya mashi da waye take yin wayar ba. Bayan ta bashi amsarsa ne ta É—agawa su Sarina gaisuwa a matsayinsu na sister É—inta.

Cikin nutsuwa suke cin abinci. Kuyanga Zubaida ta zubawa Chuchun abin da take buƙata. Room ɗin ya yi tsit kamar ba mutane, sai sautin spoon ɗai ɗai zaka ji yana tashi.

A hankali Chuchun ta É—auki cup mai shake da pina colada zata kai É—an bakinta, tana jin ra'ayin shansa kaÉ—an ba dayawa ba.

Bata ƙarisa kai shi bakin nata ba ta ɗan yi ƴar ƙara tare da sakin kofin ya faɗi a saman table ɗin.

A hanzarce gabaÉ—aya kowa dake saman dining É—in ya É—ago da kansa tare da kai kallonsa kanta. Auta ta riga kowa tambayarta lafiya me ya sameta?.

Autar bata rufe baki ba King ya jefo nashi tambayar. Nan take kowa ya fara jefo nasa tambayar, sun tsura mata idanu suna jiran amsa.

A hankali ta ɗan ɗago idanunta ta saci kallon Jawad da suke fuskantar juna, ya yi wani yin ƙasa da kai kamar babu shi a room ɗin. Bin in da take kallo da kallo King ya yi, ganin Jawad take kallo yasa ya cigaba da cin abincinsa ya fita shirginsu, dan yasan in ya biye masu ma shi zai ji kunya a banza.

Su Momma sai tambayarta suke yi ta ƙasa yin magana, kowa ya ruɗe yana ta cewa lafiya kuwa? Amma ina ta ƙasa magana.

King ne ya ce. "Wai ku ku rabu da ita mana, Zubaida ki sake zuba mata wani pina colada domin ta sha dan naga shi take ra'ayi".

A hanzarce kuyanga Zubaida ta zo ta fara kwashe wanda ya zube ta gyara wajen, sannan ta zuba mata wani ta turo mata shi gabanta.

ÆŠauka ta yi tana ta kallon fuskar yayan nata. Shi kuwa kamar babu shi a wajen.

Tana ƙoƙarin kai cup ɗin bakinta a karo na biyu ya sake yi mata abin da ya yi mata ɗazun yasa ta zubar da wancan pina ɗin, ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. Ba komai yake yi mata ba face babbar yatsar kafarsa yake zurowa ta ƙasar table ɗin yana ɗan yi mata kamar tafiyar tsutsa a kafafunta, da yake doguwar riga ce a jikinta, ta ƙasar rigar yake zura kafar tasa yana taɓa mata tata. To da ya yi mata na farko tsoratata ya yi, dan bata yi expect na jin hakan ba, ta tsorata.

Yanzu ma a hankali ya sake zuro kafar tasa ya fara yi mata kamar É—azun. Still yanzu ma ta tsorita, sai dai bai kai tsoron da ta ji É—azun ba, É—an lumshe idanunta ta yi tare da kai cup É—in É—an bakinta.

Bata cire cup É—in daga bakin nata ba ta waro idanun nata a saman fuskarsa, a lokacin shi ma ya zuba mata idanu yana kallonta, wani irin kyau ta yi mashi lokacin da ta lumshe idanun nata, sai ya ji ta gama tafiya da shi mai gabaÉ—aya, da babu kowa a room É—in ba abin da zai hana shi rungumota.

Cigaba da yi mata tafiyar tsutsa a kafar tata ya yi yana mai cigaba da kallonta, ita ma tana shan pina ɗinta tana kallonsa tana ɗan murmushi. A hankali ya gangaro da kafar tasa izuwa dai'dai sai tin tata, sannan ya sanya ƴatsun kafafun nasa ya riƙo nata babbar yatsar kafar yana wasa da shi.

Duk abin da suke yi King yana kallonsu, amma ya cigaba da cin abincinsa tamkar bai ga komai ba, tunanin abin da zai yi kawai yake yi a ransa, tunanin kalar hukuncin da zai yanke masu yake yi.

Matse mata babbar yatsar kafar tata ya yi a cikin tsakiyar nashi yatsun. Har sai da ta ɗan yamutse fuska alamar zafi, ɗan turo mashi baki ta yi tare da ajiye cup ɗin pinan nata, kamar zata sanya mashi kukan shagwaɓa.

Ganin hakan yasa ya É—an sakar mata Æ´atsun nata, yana saki ita ma tasa nata wai zata kamo nashin ta matse ya ji idan da daÉ—i. Amma ina Æ´an yatsunta ba za su iya kama na shi ba, ya yi mata girma. Kamar zata yi kuka take binsa da kallo tare da turo baki.

Wani siririn cool murmushi ya sakar mata wanda ya sanyata sauke ajiyar zuciya, sannan ya kashe mata ido É—aya. Plate É—in abinci da kuyanga Zubaida ta zuba mata ta jawo ta fara ci tana sakin murmushi, tana jin daÉ—in kasancewa da Yah Jawad a yanzu, saboda yana sakar mata fuska kuma yana mata wasa sosai, so tana jin daÉ—in kasancewa a tare da shi sosai da sosai.

Bayan sun kammala cin abincin ne ya janye kafarsa daga kusa da tata, a hankali ya miƙe tsaye. "Jannat ki kawo mun wayata da na baki room ɗina". Yana maganar unexpect again kallonsa ta sauka a kan King, tun ma daddyn nasu bai yi wani yunƙurin ba ya sakar mashi murmushi tare da sa kai da sauri ya wuce.

Sai dai kafin ya fita muryar King É—in ta daki dodon kunnuwansa da cewa. "Ka sameni a room É—ina yanzu Jawad".

Da okey kawai ya amsa sannan ya fice. Da É—aiÉ—ai da É—aiÉ—ai kowa ya watse a room É—in.

Akka tana shigowa cikin room ɗinta wayarta dake saman bed ya fara ruri. A hanzarce ta ƙarisa ta kai mashi agaji.

Picking ta yi tare da hayewa saman gadon mai gabaÉ—aya.

Daga can ɓangaren Rizwan ya fara tsantsara mata sallama tare da ɗaga mata gaisuwa.

Sai da ta zage shi kafin ta amsa, wai yau kuma wani munafurcin yasa ya kirata? Dan rabon shi da kiranta tun last year sallah da ya kirata ya yi mata happy sallah, to yanzu kuma gulmar me yasa ya kirata?.

Hakurin ya fara bata tare da rarrashi yana gaya mata aiki ne ya yi mashi yawa. Tatas ta zage shi daga shi har su Ramish É—in gabaÉ—aya kafin ta saurare shi, Akka akwai dirama tsohuwar nan.

Cikin zumuÉ—i ya sanar da ita dalilin kirata, ya kira ne ya sanar da ita ya samu mata kuma ba kowa bace face Chuchu, dan haka ta taya shi kafin ya zo.

Wani irin matuƙa fari tas ɗin farinciki ne ya mamaye mata cikin zuciya. Haƙiƙa ta ji daɗi kuma ta yi murna, amma sai ta ɓoye murnar tata, ta fara zazzaga mashi masifa a kan ai dama tasan yanzu ma buƙatar kansa ne yasa ya kirata, to dan haka ya sani ba zata bashi Chuchu ba, kuma dai yasan ita ce mai zartar da hukuncin a kan komai.

Lallaɓata ya fara yi yana magiya tare da marairace murya, yasan Akka ita ce nan take da iko da su da iyayensu, yasan idan ta bashi Chuchun to fa babu uban da ya isa ya hana, haka zalika idan ta hana shi, wannan dalilin ma yasa ya biyo ta wajenta kai tsaye bai je wajen daddy ba, dan ko ya je ga daddyn ma zai ce mashi sai abin da Akka ta zartar ne, so shiyasa ya fara bi ta wajenta, kuma Mammaiensu ce ta bashi wannan shawara, ta ce kai tsaye ya tunkari Akka, kuma kada ya wani ɓata lokaci wajen jira, ya yi saurin tunkararta ya gaya mata, hakan yasa ya gaya mata ɗin.........

Lallai da gaske Mammie ta shirya raba Jawad da soyayyar Chuchu karfi da ya ji, domin kuwa hanyar da ta biyo mai karfi ne wanda ya fi na Jawad karfi, tun da Rizwan ya gayawa Akka shikenan kuma, Akkar zata tambayi Chuchun tana son yayan nata ne ko bata sonsa, idan har ta amsa da tana son shi fa shikenan babu wanda ya isa ya sa a fasa wannan aure sai mutuwa sai kuma wani ikon na Allah. Ku ma dai kun san Chuchu dai tana son yayan nata, dan haka da e tana son shi zata amsa. Akwai cakwakiya ba kaÉ—an ba, akwai tashin hankali.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

Nutsuwa sosai Leesharh ta yi tana sauraron abin da yake faÉ—a. Daga yadda yake fitar da word's É—insa kai kasan nutsatsen mutun ne mai ji da izza haÉ—e da class, ba karya jinin King Zuhair yana gudana a jikinsa.
Chapter 164 · 0% Book details