← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 180

Sashe 31

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

And one thing about Damusa, basu shiga cikin ruwa, akwai waÉ—an da suke shiga cikin ruwan, sai dai masu shiga cikin ruwan basu da yawa, normal Tiger daji kamar sauran dajuka basu shiga cikin ruwa, bawai ba zasu iya shiga bane, no zasu iya, kawai basu shiga ne, dan idan ruwa ta yi yawa tana tafiya dasu.

A dubu ɗari Kamran ya ƙariso wajen, da gudu Rocky ya nufesa, wani irin harara ya wurgawa Rockyn kafin ya yi tsalle ya faɗa cikin ruwan shima, Rocky ya bashi haushi ba kaɗan ba.

Tsayuwa a wajen Rockyn ya yi yana wani girgiza, shi a dole ransa ya ɓaci bai ci nama ba, sam bai damu da harararsa da Kamran ɗin ya yi ba, shi dai nama kawai yake tunani........😅

Da kyar da suɗin goshi Kamran ya iya ceto yarinyar nan daga cikin ruwan, amma ta sha ruwa sosai kam, Allah ma yasa bata ƙarisa faɗawa cikin ainahin tekun ba ya kamata, da ta faɗa sai wani labarin ba dai nata ba, kasancewar ruwar tana ganganrawa ne yasa Kamran ya sha bakar wahala wajen iya fitowa daga wajen, da ace ruwan yana tsaye ne to da sauki, amma tana gudu kuma ganganra, kuma kunsan ba dan ya saba da shiga cikin ruwa ya kuma iya ruwa sosai ba, ai da daga shi har ita sai sun faɗa cikin tekun nan, kuma suna faɗawa shikenan, sai dai Mamma ta rungumi sorry ta kurɓi ruwan ganye shayi, dan Kamran kam da ya tafi kenan, dan ma Allah yasa duwatsu ne a wajen sosai, ya yi ƙoƙari wajen kakkamasu har ya samu ya hauro sama daga gangarar ruwan, kuma ya yi sa'a yarinyar karama ce, bata da wani nauyi, hakan tasa ya ɗauketa a saman shoulder ɗinsa kamar ƴar baby.

A bakin ƙoramar ya kwantar da ita, da gudu Rocky ya ƙariso wajen yana wani numfashi mara daɗin ji, alamar huci yake fitarwa na ransa ya ɓaci.

Shinshinar yarinyar ya fara yi kamar wani tsohon maye, cikin wannan yaren nasu Kamran É—in ya ce mashi. "Rocky ka kyaleta mana, ka sa ta faÉ—a cikin ruwa ma bai isheka ba sai ka zo kana wani shinshinata ko? To cinyeta zaka yi ne?".

Yana magana yana ƙoƙarin haɗa hannayensa dukka biyu waje guda, dan ya danna mata cikinta ta amayar da ruwan da ta sha.

Cigaba da shinshinata Rocky É—in ya yi, ya yi kamar bai ji me Kamran É—in ya ce ba, kunsan dama dabbobi irin wannan haka suke yi wa mutun, sai su yi ta wani shinshinasa kamar wasu mayu. Sai da Kamran É—in ya sake yi mashi magana ne, sannan ya koma gefe guda ya kwanta yana wani zuro harshe waje yana lashe bakinsa.

(Tab da Kamran bayana nan fa da yanzu Rocky ya cinye mana wannan kyakkyawar halitta...💔😭 Amma da mun yi asara😅)

Daddana mata cikinta a hankali hankali ya fara yi, nan take ta fara amayar da ruwan da ta sha.

Cigaba da danna mata ya yi har sai da ya tabbatar ta amayar da ruwan da ta sha tas, sannan ya zame hannunsa daga saman lallausan fatar cikin nata yana mai cigaba da kallon face nata.

Shiru shiru bata farka ba, ga dai ruwan ta amayar da shi, amma bata farfaÉ—o ba.

Ganin hakan yasa ya matso kusa da ita sosai tare da matso da kansa izuwa saitin kirjinta, kunnuwansa ya kai saitin kirjin nata, dan ya ji shin kirjinta yana harbawa ne ko dai ta mutu?.

Ba shakka kirjinta yana harbawa fat, fat, fat, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ji daÉ—i sosai da ya ji tana raye.

Zuba mata idanu kawai ya yi yana ta kallonta, ta jima sosai a haka kafin ta fara motsawa, duk kuma wannan jimawa da ta yi Kamran na tsare da kallonta, kamar zai cinyeta da ido.

Kyawawan fararen kafafunta ta fara motsawa, kun san dama idan mutun ya tsorata ta dalilin haka har ya suma, to farfaɗowarsa akwai wuya, bare kuma ita da ta faɗa cikin ruwa, tana faɗawa kuma ta farfaɗo saboda ruwan da ya taɓata, ta sha ruwa ta sake suma, ai tama yi ƙoƙari da ta iya farfaɗowa a yanzu.

A wani irin razane tana kurma ihu ta farfaɗo, a zabure ta miƙe zaune tana ƙoƙarin tashi ta gudu, da alama ba'a cikin hayyacinta ta farfaɗo ba, ta tsorata ne ainun.

Da sauri Kamran É—in ya rikota, dan idan ya barta zata je ta afka wani wajen ta cutu ba tare da ta sani ba, dan bata a cikin hayyacinta.

Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi, idanuwanta a rufe ruf, burinta kawai ta gudu, a tunaninta ma damusar ce ta riketa, hakan yasa ta sake zunduma ihu mai sauti, sai ƙoƙarin fusgewa take yi.

Da hannu É—aya Kamran É—in ya riketa, amma ta kasa iya kwace kanta, ga shi taki buÉ—e idanun taga a hannun waye take.

Cikin yaren nan nasa dai ya yi mata magana a kan ta nutsu. Sai dai ina, sam bata ji me ya ce ba, sai cigaba ma da ƙoƙarin kwatar kanta da ta yi dan ta gudu.

Ganin haka yasa tunanin Mum twins ya faÉ—o mashi a cikin ransa, ya tuna ranar da ya fara yi wa mum twins magana da yarensa, sam bata ji, sai turanci kawai take ji, hakan yasa sai ya yi wa yarinyar ma magana da turanci a kan ta yi shiru ba Tiger bane, shi ne nan ya riketa.

Jin sautin muryarsa yasa ta É—an nutsu, sai dai ta kasa iya buÉ—e idanuwanta, dan tana ganin kamar idan ta buÉ—e idanu fa waÉ—an nan garma garman hakwaran Rockyn zata sake gani, hakan yasa taki yarda ta buÉ—e idanuwanta.

Shiru Kamran ɗin ya zuba mata idanu yana ta kallonta, shi dai a duniya bai taɓa ganin kyakkyawa haka ba, bare ma fatar jikinta, a hankali ya mayar da kallonsa izuwa saman wuyarta, tana da abin da ake cewa gurun wuya, ga shi gurun wuyar tata mai balai'n kyau, bai yi irin cika sosai ɗin nan ba, ya yi dai'dai da jikinta, namar wajen ya ciko dai'dai, hakan ba kamamin kyau ya yi mata ba.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa ta fara motsa idanuwanta a hankali tana son buÉ—esu.

Sai dai kash, tana buÉ—e idanun nata ta yi rashin sa'a a in da ta sake yin ido biyu da Rocky da ya iso wajen yanzu, dan ya kalli Kamran É—in ya sankare waje guda yana ta kallon face nata ne yasa Rockyn ya kariso wajen shi ma yaga me yake kallo haka.

Wani irin mahaukacin ihu ta sake zundumawa tare da fara ƙoƙarin kwace kanta daga hannunsa ta gudu.

Ganin hakan yasa ya yi saurin juyar da kansa dan ya ga me ta gani daga buÉ—e idanuwanta ta sake ruÉ—e mashi haka.

Gamin Rocky ne yasa ya yi ƙoƙarin gaya mata cewa ta nutsu Rocky babu abin da zai yi mata, idan ta gudu ne ma zai bita, dan zai yi tunanin ta yi wa Kamran ɗin wani abin ne ta gudu, so zai bita ya kamata ya dawo da ita wajen Kamran ɗin, rufin asirinta kawai ta nutsu.

Amma ina ita ai ta kasa yarda ta nutsu, gani take tsab Rocky zai cinyeta idan ta tsaya. Da iya karfinta take ƙoƙarin kwace kanta.

Ganin da gaske take yi zata kwace kanta ta gudu ne yasa Kamran É—in ya jawota jikinsa sosai, ya riketa da kyau yana mai cigaba da ce mata ta nutsu babu abin da Rocky zai yi mata.

Kankame shi ta yi tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tun da take bata taɓa kallo Tiger a wajen ba, da alama babu Damusa ko kaɗan a yankin nan nasu, kuma da alama basu shigowa wajen, dalili kuwa shi ne yashi (kasa) ta yi yawa sosai a wajen, sannan kuma akwai teku a wajen, Damusa kuma bata son waje irin haka sam, shiyasa ma basu leƙowa arear wajen, dan tekun da yake wajen ma ba irin kogin da namun dawa suke zuwa shan ruwa bane, babban teku ne wanda suke tsoron zuwa wajen, dan kar ruwa ya tafi da su.

Wani irin kuka take yi wadda duk wanda ya ji sautin sai ya ji ta ratsa mashi zuciya sosai. Haka shi ma Kamran ya ji sautin wannan kukan nata tana ratsa mashi zuciya, hakan yasa ya kara rungume sosai yana mai cigaba da gaya mata ta yi shiru babu abin da Rocky zai yi mata, har da gaya mata ya yi cewa Rocky fa abokinsa ne, dan haka ta kwantar da hankalinta.

Ina ta jima tana wannan kukan zuci a kusan kafin Kamran ya samu ta yi shirun da kyar, sai sauke ajiyar zuciya take yi.

Sun ɗan jima a haka kafin ta ɗan ɗago kanta daga saman kirjin nasa, cikin tsananin tsoro ta ɗan ɗago idanunta tana leƙo da kai tana leƙen Rockyn, shi dai yana tsaye yana ta kallon ikon Allah.

Ganin sai kallonsu Rockyn yake yi ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai yanzu ta yarda da zancen Kamran ɗin na cewa babu abin da Rocky zai yi mata, yanzu kam ta yarda, tun da ga shi yana tsaye shiru yana kallonsu bai cinye su ba, hakan yasa ta yi ƙoƙarin barin jikin Kamran ɗin, tana cigaba da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Bai hanata barin jikin nasa ba, sai ma binta da kallo da ya yi, sai a yanzu da ta nutsu sosai ne kamanninta ya kara bayyana, kuma a yanzu kusa da kusa yake ganinta.

Ɗan kara zaro idanuwan nasa ya yi yana kallonta sosai, ko mutuwa ya yi ya dawo ba zai taɓa mantawa da kamanin mum twins ba, domin lokaci guda matar ta yi wani irin shiga mashi cikin ransa sosai, bayan Mammarsa da kuma Rocky bai taɓa kaunar wani abin a duniya ba kamar yadda ya kaunaci mum twins da twins nata, kullum suna cikin tunaninsa.
Chapter 31 · 0% Book details