Sashe 119
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa kitsa mashi su ta yi kamar yadda mummynta ta koya masu, sannan ta nannaɗe jelar gashin nasa ta cusa mashi a ƙarƙashin kitson kafin ta mayar mashi da hularsa ta rufe mashi kan nasa.
A ta gabansa ta dawo ta zauna tare da kwantowa a jikinsa ta kai hannu ta karɓi abin busar. "Kawo bari na busa mana". Ta faɗa cikin sanyin murya.
Ba musu ya miƙa mata, dan shi ma yana jin daɗin busar tata sosai. Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a saman shoulders ɗinta a in da ya zuro da su ta gaba ya kara jawota jikinsa yana faɗin. "Rocky fa yana nan zuwa?".
Kai abin busar É—an bakinta ta yi tana girgiza kai, kafin ta fara busar ta ce. "Yazo nan sai na mare shi, gara mashi tun wuri yasan in da dare ta yi mashi". Cikin tsiwa ta yi maganar, dan fa ita bata kaunar Rocky, sam jininsu bai haÉ—u ba, har yau har gobe razana take yi idan ta ganshi.
ÆŠan murmushi kaÉ—an ya É—an yi wadda ba za'a iya kiranta da murmushi bama, dan sam bata fito ba, sannan ya sauke hannunsa É—aya daga saman shoulder É—in tata izuwa saman É—an shafaffen cikinta. "Rocky fa baya da faÉ—a, kece nan kike sawa yake baki tsoro".
"Ko baya da faɗa bana sonsa, kuma ba zan taɓa sonsa ba". Tana kai karshen maganar ta fara busarta cikin kwarewa, a yanzu ta iya busar sosai da sosai, ga shi kala daban daban ta iya rera busar, har wani lumshe idanu suke yi daga ita har shi idan tana busa masu. Akwaita da ƙwaƙwalwa, cikin ƙanƙanin lokaci take iya koyan abu ta haddace, akwai su da baiwa twin's ɗin nan sosai.
Yanzu ma tsabar daÉ—in busar yasa suka lumshe idanu su dukkansu, ta kara lafewa a jikinsa tana mai cigaba da busawa.
Wajen ya yi shiru tsit, sai karar sautin zubar ruwa da kuma kukan tsuntsayen dake shawagi a wajen zaka ji, a hankali hankali sautin busar tata yake tashi a arear wajen, hakan ba ƙaramin daɗi da ƙawa ya yi ba, a yanzu akwai wata busa da suke yi wa junansu, wanda Kamran ɗin shi ne ya koya masu, idan suka cutsa cikin daji yawo, da wannan busar suke kiran juna, wani lokaci idan suka je yawon nasu Kamran da Sweetie suna zama a ƙarƙashin bishiya suna hira, ita kuma Pretty yawo take tafiya abinta, so idan Kamran zai nemota sai ya ciro abin busarsa ya fara busawa, idan tana kusa da shi zata mayar mashi da martanin irin wannan busar da tata abin, shi kuma zai bi sautin karar busar tata har zuwa in da take.
Idan kuma ta ji shiru bata mayar mashi da martani ba to ta É—an yi nisan zango, sai ya kara gaba har sai ya samota.
Wani kyakkyawan parrot ne ya sauka a kusa da Pretty da ta lumshe idanu tana aikin busa mai kwantar da hankalin mai sauraro.
Cikin dabara Kamran ya shammaceta tare da shammatar parrot É—in ya damko shi. Tana jin alamar hakan ta yi maza ta waro idanunta waje tare kuma da dakatawa daga busar tata.
Aikuwa tana yin ido biyu da wannan parrot ɗin ta fara yunƙurin miƙewa a guje dan ta bar wajen, dama Kamran yasan za'ayi hakan, shiyasa ya shammaceta ya kama parrot ɗin, yasan idan ta ji saukar shi a kusa da ita haukace mashi zata yi, kaɗan daga aikinta kenan sarkin tsoro.
A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Zauna ki ji".
Bata ankaraba sai ji suka yi parrot É—in ya maimaita abin da Kamran É—in ya faÉ—a na zauna ki ji, sai dai maganar akun bata fita sosai. Hakan na nufin akun mai magana ce, kun san akwai waÉ—an da basa magana, to shi wannan yana yi, sai dai maganar bata fita.
Wani irin zaro idanu waje Pretty ta yi na jin yadda wannan Parrot É—in ya maimaita maganar Kamran, waÉ—an nan olive eyes É—in nata kamar zasu faÉ—o kasa saboda zarosu da ta yi, cike tab da mamaki ta ce. "Kamran magana fa na ji ya yi......"
Ai bata kammala rufe É—an bakin nan nata ba Parrot É—in ya maimaita abin da ta faÉ—a na cewa Kamran magana fa na ji ya yi, still dai maganar bata fita sosai, amma ana iya gane me ya ce.
"Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?...."
"Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?......" Parrot É—in ya maimaita abin da ta faÉ—a.
Ina ai a dubu ɗari ta yunƙura zata tashi, dan ita bata taɓa ji ko gani ba, ta dai san dabbobi basa magana. Kamran dai sai kallonta yake yi, dama da gangan ya kama parrot ɗin, dan kawai ta sanya shi yin nishaɗi, yana jin matuƙar nishaɗi idan yana kallon wannan kyakkyawar face ɗin tata cikin tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take karawa ba, sai ma ta zaro idanun nan nata, sai ka ji kamar ka yi ta kallonta kada ka gaji, hakan yasa wani lokaci har Allah Allah yake yi ta tsorata ya kalleta da kyau yana nishaɗi.
Kara janyota jikinsa ya yi tare da matso mata da parrot ɗin kusa da ita, ƙasa ƙasa ya fara yi mata magana bayan ya ɗan sunkuyo da kansa a dab da kyakkyawan razanannen face ɗin tata.
"Tsuntsaye basa magana Pretty, amma shi parrot yana magana sosai ma, kada ki ji tsoro babu abin da zai yi maki". Yana maganar yana kallon face É—inta.
Ai kuwa yana rufe É—an bakinsa Parrot É—in ya maimaita abin da ya faÉ—a mata shi ma.
Sanya idanunta cikin nasa ta yi da kyau. Calmly ta ce. "Kenan ba aljani bane?". Yadda ta yi maganar a kusa da shi sosai hakan yasa sai da ya ji wani iri, ga shi kuma ta yi maganar tana zaro mashi waÉ—an nan dara daran idanun nata masu rikitar da shi, sannan tana magana kyakkyawan lips É—inta yana É—an kerma, dan already ta rigada ta razana tun farko.
Kafeta da idanu ya yi ya kasa iya bata amsa, shi kaÉ—an yasan a wani hali yake shiga a duk lokacin da zata yi magana kusa da kusa da shi har haka, bare ace maganar ta haÉ—u da tana cikin firgici ta yi sa tana zaro idanun nan, ai abin ba'a magana.
"Kuma ba zai cinyeni ba Kamran?". Ta sake jefa mashi tambaya tana mai cigaba da zaro idanun nata alamar mamaki abin ya bata.
Sam bai san lokacin da ya saki parrot ɗin nan ya tashi sama abinsa ba, ya luluƙa duniyar sama jannati na kallon ƴar diramarsa.
Ganin ya saki tsuntsun ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa jikinsa tana hamdala ga Allah daya sanya Parrot ɗin bai cinyeta ba. Sam bata lura da duniyar tunani da kuma kallonta da Kamran ɗin ya afka ba. Ita dai da ta ga ya saki parrot ɗin ya tashi sama sai ta juya ta cigaba da busar da take yi. Wannan shi ne yana yi bata san yana yi ba, ita dai babu ruwanta da wani abu wai soyayya, yo Allah na tuba dama nawa take? Ga rashin nutsuwa a tattare da ita, ita kanta Sweetie nutsatsiyar ma yaushe ta san menene soyayya bare wata Pretty, ai ita Pretty bata da wata damuwa a rayuwarta da ya wuce ta ci abinci, ta yi wanka ta kuma yi sallah, dan suna yin sallah a kan lokaci kam, kuma da rana suke auna lokaci, wani lokaci kuma da yanayin garin suke auna lokaci kamar yadda mum ɗinsu ta koya masu, bayan sallah kuma shikenan sai Kamran ya kaita yawo, iya abin da ta sani a duniyarta kenan ƴar albarka.
Sweetie ita ce mai zama ta yi tunani a kan gobensu da kuma makomarsu, wani lokaci har tana gayawa Kamran cewa tana ji a jikinta tabbas wannan dajin ba iya shi kaɗai bane a duniya, akwai wani waje, sannan shi ma wajen tana ganin kamar mutane suna rayuwa a ciki. Tun Kamran baya wani ɗaukar maganganunta da mahimmanci har abin ta fara shiga zuciyarsa shi ma, hakan yasa shi ma ya fara tunanin ƙure wannan dajin a wajen tafiya ko zai iya ganin makamancin abin da Sweetien take hangowa na wasu mutane da suke rayuwa a duniya........ Tirƙashi, lallai Sweetie tana son ɓallowa Mamma ruwa, dan kuwa idan ya fita wannan dajin dai kunsan zai haɗu da mutane, idan kuma ya haɗu da mutane ku da kanku readers kun san labarin dole ya canza salo, dan kuwa ba karamar dirama zasu buga shi da Mamma ba, idan ma ya dawo a kan lokaci kenan, akwai fa cakwakiya idan har Kamran ya yarda da wannan hasashe na Sweetie, zai iya cewa ma Mamma munafurtarsa take yi ta ki gaya mashi bayan wannan dajin akwai wata rayuwa ta daban, kuma ina da tabbacin zai ce ba zai cigaba da zama a wannan daji ba, dan kowa dai baya son wahala sai dole, bare shi da yake bai yi kalar ƴan kauye masu duhun kai ba, da wayonsa da kuma iliminsa dai'dai gwargwado, kunga kuwa ai dole zai so canjin rayuwa, akwai cakwakiya, Sweetie ta zo da wata al'amari mai girman gaske wanda zai iya tarwatsa zuciyar Mamma, domin kuwa da ni da ku dukka mun san Mamma bata da kowa a duniya sama da Kamran, tana kaunarsa fiye da yadda take son kanta, kuna dai ganin yadda take kula da shi, ko nan da can bata son taga ya matsa, ace rana tsaka ya fita cikin wannan dajin, sannan ya dawo ya ce mata shi ba zai sake zama a nan ba wajen mutane zai tafi ya yi rayuwa? Kuna tunanin zuciyarta ba zai tarwatse ba? Hmmmm akwai case!.
"Pretty". Ya ambaci sunanta a hankali, ƙasa ƙasa kuma a ta cikin kunnuwanta.
Dakatawa da yin busar ta yi tare da juyowa gare shi. "Kamran lafiya ka kirani?". Ta yi tambayar tana riƙo hannayensa dukka biyu. Abin busar ta sanya mashi a hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ta ɗaura shi a saman a shoulder ɗinta ta ɗan kwanto a saman kirjinsa.
"Pretty kin san menene soyayya?".