Sashe 118
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙasa kaɗan ta ɗan yi da kanta kafin ta amsa da tana yi. Kasancewar muryarta baya fita sosai yasa Radia bata iya gane me ta faɗa ba, sai kawai ta mayar da kallonta a Tv da suke kallah. Ko a iya kan masu aikin gidan kawai ya isa yasa ku fahimci shi Abu Abdussalam bin Badeen shugaba ne adali, duba kuga yadda masu aikin suke shanawarsu, idan sun kammala aikinsu suna da damar zuwa part ɗinsu su yi wanka su sha kwalliya kamar ƴan gida, su kunna Tv da Ac su samu waje su zauna suna kallo. Akwai emergency phone a gidan ta ko'ina wadda duk wanda yake buƙatar wani abin daga wajen wata ƴar aiki koma a hawa na nawa yake zai iya kiran emergency phone ɗin nan, cikin ƙanƙanin lokaci masu aikin zasu bayyana su kawo mashi abin da yake buƙata, sam Abu Abdussalam bai ƙasƙantar da ƴan aikinsa dake a ƙarƙashinsa kamar yadda saura suke yi ba, ya basu jin daɗi da hutu suma kamar ƴaƴa, har sun dai'na jin kansu a matsayin ƴaƴan talakawa marasa gata, ga shi a duk karshen shekara yana basu dama su je ganin iyayensu bayan ya cikasu da alkhairai dayawa, zai basu abubuwa da dama su kaiwa iyayen nasu, a kaisu da mota a kuma dawo da su, ita ma Ummie ta kara masu, Sharifat da Omar ma wato Guyson ba'a barsu a baya ba, suma in dai masu aiki zasu je ganin gida sai sun basu kyauta mai tarin yawa su ce su kaiwa ƴan uwansu, Sharifat yarinyar kirki, haka zalika shi ma Omar ɗin Gimbiya Zunaira, yana da kirki shiyasa suke shiri da Sharifat sosai, duk gidan su biyun nan ne suke shiri sosai, bayan shi Sharifat bata shiri da kowa, ko sauran brothers ɗin nata, dan basu wasa da ita, kallo ma bata ishesu ba, amma fa suna bala'in kaunarta over, kawai dai basu wasa da ita ɗin ne.
Fadila ce ta dawo cikin parlourn baki a É—auke da sallama, ta kai kayan abincin cikin kitchen ne ta dawo. "A'isha muje ki ga yadda abubuwa da kuma dokokin gidan suke ko? Daga nan sai na nuna maki parlourn da zaki yi aiki a ciki".
Da mamaki Leesharh ta ce. "Dama ba'a parlourn da muka shiga É—azun zan yi aiki ba?".
Kallonta da kyau Fadila ta yi tana mamakin yadda take magana, ta ji voice É—inta baya fita sosai, abin sai ya bata mamaki. Amma sai bata ce komai a kan yanayin maganar tata ba. Sai ta ce. "Wannan parlourn ai na hutawar Ummie ne, ainahin babban parlourn gidan mai É—auke da part na kowani É—an gida yana gaba dana Ummie, muje zaki gani".
Ba musu ta miƙe, Fadila ta ɗan yi gaba kaɗan ta na ce da Radia ko zata zo su je ne. Sai kun dawo Radia ta yi mata alamar ba zata je ba kenan.
Fitowa suka yi Fadila tana nuna mata komai daki daki tare da yi mata bayanin yadda komai yake dallah dallah.
Sosai Leesharh ta kasa kunne take naÉ—an komai da ake gaya mata tare da hanyoyin da suke bi. A haka har suka isa izuwa babban parlourn, sai dai sun É—an sha tafiya sosai daga part É—insu zuwa parlourn, sannan ne suka isa.
Ai a nan ne Leesharh ta zama cikakkiyar ƴar kauye sosai, ko a film bata taɓa ganin parlourn mai girma da haɗuwar wannan ba, gari guda, ya haɗiye sofa set kala kala har set biyar, ya ƙawatu iya ƙawatuwa kamar parlourn shugaban ƙasa. A nan ne part ɗin kowane ɗan gida yake wadda shi ma akwai ɗan madaidaicin parlourn a cikinsa kafin sleeping room ɗinsu.
Ganin yadda Leesharh ta saki baki tana karewa parlourn kallo ne yasa Fadila ta ɗan yi dariya kaɗan kafin ta ce. "A'isha wannan parlourn zaki rinƙa gyarawa, amma ba ke kaɗai bane, Ummie ta gaya mun ke kaɗai ba zaki iya ba, ta ce na rinƙa tayaki, sai kuma part ɗin Aunty Sharifat wanda ga shi can shi ne na tsakiya, na Guyson shi ne a kusa da nata, su ne zaki rinƙa gyarawa ke kaɗai, parlourn kuma zamu gyara a tare".
Jinjina mata kai kawai Leesharh ta iya yi, amma ta kasa yin magana, haÉ—uwar wannan parlourn ya ruÉ—ar da ita.
Ta yi shiru tana kalle kalle ne can idanunta suka hango mata wani katafaren frame na hoto, yana da girma frame ɗin, an ƙawata shi ya yi kyau sosai. Wani irin zaro idanu waje sosai Leesharh ɗin ta yi a lokacin da idanunta suka sauka a kan hoton da yake a jikin frame ɗin, a hanzarce ta runtse idanunta ta sake warosu a kan hoton. Sam Fadila bata lura da yanayin da Leesharh ɗin ta shiga na ganin wannan hoto ba, hankalinta ita yana can kan yi mata bayanin lokutan da zata yi aiki, bata san Leesharh kam bata a tare da ita ba.
Hoton wani kyakkyawan matashi ne number ɗaya, kyakkyawa ne sosai ɗan wanka, ya sha wanka da idan ka gansa sai ka so ka sake ganinsa, ya fita iya fita a hoton, kamar ka kirasa ya amsa, kansa na sunkuye a ƙasa ya ɗago da dara daran fararen idanunsa, yanayin smooth skin ɗinsa kamar madara, dark black arab hairnsa kamar wadda aka kifawa hula har gaban goshinsa, yana da ɗan ƙaramin lips sosai, hasken fatarsa tasa launin lips ɗinsa ya kara fitowa sosai, a shekaru ba zai wuce 15 to 16 years ba, ya sanya wata ƙatuwar Bluetooth a kunne, da alama dai ɗan gayun ne na gasken gaske, ko kaki ko kaso daga ganinsa kasan ya ci sunan da suke kiransa da shi wato Guyson, dan fa guy ɗin ne da gaske.
So ita Leesharh ba wai kyansa ne ya ruɗata ko kuma wankar daya ɗauka ba, dukka ba wannan ba, abin da ya ruɗa ta shi ne yanayin kamaninsa, tabbas yana kama da wancan matashin da ta gani a gidansu masu nukaf wanda ya je ranar, duk da bata sami damar ganin face ɗinsa da kyau ba kasancewar kansa na kallon ƙasa, amma tabbas a yadda Guyson ya duƙar da kansa ƙasa tare da ɗago waɗan nan kyawawan idanun nasa ba makawa sun yi yanayi da wancan guy ɗin, tabbas sun yi mata kama, wannan shi ne abin da ya ruɗar da ita.
Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye tare da fara tunanin wanene ma Guyson ɗin nan tukun nan? Idan har da gaske ne abin da idanunta suka gaya mata na yanayin kamanceceniya a tsakanin Guyson da wancan matashi hakan na nufin kenan already dama makashin Ramish yana nan a tare da shi? Ko dai yaya abin yake ne? To amma idan har makashin nasa yana a tare da shi meyasa za'a turota leƙen asirin motsinsa? Kai ina hakan ba zai yi wu ba.
Wani tunanin ta sake yi a kan to anya wancan matashin da ya je gidansu mai nikaf É—in nan yasan da abin da suke shiryawa kuwa? To wannan wani irin al'amari mai bala'in rikitarwa ne?.
Ya ilahi ya lilliahi, shi ne abin da Leesharh ta furta a cikin zuciyarta tare da dafe kanta da yake yi mata barazanar tarwatsewa. Sai magana Fadila take ta yi mata, amma ina ko kalma É—aya bai shiga mata cikin kunnenta ba. Haka Fadila ta gama surutun bayanan nata abanza, ta ce su tafi. Ta yi maganar tare da wucewa gaba.
Ganin tana tafiya ne yasa Leesharh ta rufa mata baya, yadda kuka san wadda kwai ya fashewa a ciki haka take jan kafafunta, duk jikinta ya yi sanyi, sai tunani take yi a kan masu nikaf ɗin nan, faɗi take yi a cikin ranta anya masu nikaf ɗin nan basu da wata alaƙa da wannan gida kuwa? Anya ba ƴan uwan juna bane?.
Nima dai PRINCESS TEEMA an jefani a cikin ruɗani, dan haka bari na bar part ɗin su Leesharh ɗin nan kada su sanya ƙwaƙwalwata ta tarwatse, bari na je na sha Maltina mai sanyi sannan na leƙa mana su Kamran, wata kila kafin na dawo ƙwaƙwalwata zata ɗan huta na samu na cigaba da kwaso maku labarai a kan Leesharh tamu... Amma dai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!.
ðŸžï¸FORESTðŸžï¸
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 14/8/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________35🔥
🕊ï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼
ðŸžï¸FORESTðŸžï¸
A zaune suke wajen ƙoramar nan, Kamran yana zaune a saman dutse mai ɗan faɗi ita kuma Pretty tana tsaye a bayansa tana ta famar yamutsa mashi kyakkywar gashin kansa, sai busa mai daɗi yake yi masu da abin busarsa. Sweetie kuma tana cikin raminsu tana barci, bata fito ba yau, ta ce zata kwanta ta huta.
Kayan sakar da ya kawo masu Pretty ta sanya a jikinta, ta yi matuƙar kyau over, sai ta zama kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta kara zama ƴar karama da ita, kamar dai kullum kyakkywar dark black curly hairnta a ɗaure kashi biyu, ta saki jelar gashin har bayanta, sket ɗin kayan ya tsaya mata a iya gwiwarta.
Sai watsa mashi gashin kansa take yi kamar an aiketa, wai zata É—aure mashi irin yadda mum É—insu take É—aure masu nasu, haka take É—aurewa Sweetie ma nata, to shi ne wai shi ma zata É—aura mashi nasa. Ta yi mamakin ganin yadda gashin nasa yake da yawa bakin kirin da shi, ya yi baki sosai kamar tata.
Sai fama take yi, gashin ya fi karfin ƴan hannayenta, shi kuwa sai busa yake yi masu. Da kyar ta iya samu ta raba gashin nasa gida biyu, kitsa mashi ɗayan ta fara yi, sam bai san me take ta faman yi mashi ba, shi dai har cikin ransa yana jin matuƙar daɗin wasa da gashin nasa da yake yi, dan a tunaninsa wasa da shi take yi, so hakan daɗi yake yi masa.