← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 180

Sashe 133

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwance a jikinsa ta amsa da. "Ai na dai'na komai ma, amma dai tom gaya mun sai na kara dai'nawa".

Shirmenta ya fara saka shi farinciki da murmushi, wai komai ma ta dai'na, ita da bata san ainahin dalilin da yasa a kullum suka haɗu sai sun sami saɓani da shi ba, amma wai ta dai'na, har da wani zata kara dai'nawa.

Murmushi kaɗan ya ɗan sakar mata kafin ya ce. "To promise me that za'a rinƙa sanya ɗan'kwali one! Two kuma za'a rinƙa sanya hijab idan za'a fito da sleeping dress!".

Ita dai tun da babu zancen punishment a yanzu ai shikenan, dan haka sai ta ce "I promised you ba zan sake yi ba dukka".

Kara rungumeta da kyau ya yi. "Yah Jawad to hoto fa?".

Ƙasa ƙasa ya amsa mata da. "Ki cigaba da ɗaukar kayanki, ba zan takura maki ba, dan kada ki sake tsanata".

Ƴar dariya ta yi tana faɗin. "A'a ba zan kara tsanarka ba ai".

"Promise?". In a low voice sosai ya yi maganar.

Da sauri ta gyaÉ—a mashi kai alamar e. "Okey tom shikenan jeki shirya sai kizo ki rakani wani waje, amma kada ki bari kowa fa yasan cewa zaki rakani wani waje, kawai idan kin gama shi sai ki kirani a waya zanzo mu tafi".

Cike da murna ta zaro idanu tana faÉ—in. "Yah Jawad wajen Kingdom zamu fita?".

Basu taɓa fita waje haka wai yawo ba, sai dai idan Dubai zasu tafi, shi kuma Dubai daga cikin gida idan suka shiga mota sai airport kai tsaye, shi ma Dubai suna jimawa sosai, school nasu ma kunga a cikin kingdom ɗin yake, ba su taɓa leƙa waje su ga gari ba, suna son zuwa yawo suga gari, amma ba hali, ko shopping za su je yadda kuka san menene, a mota za'a kaisu, a jira su ɗauki abin da suke so, sannan a dawo da su har cikin gida, basu fita ko nan da can, su ko irin taro na sarakuna da ake yi kowa ya je da iyalensa King baya yarda, baya son yaga suna yawo cikin mutane, shi King ai sai dai a zo a same shi a cikin kingdom ɗinsa, ba kowani taro yake zuwa ba bare ma har ya je da ƴaƴansa, yana da doka mai tsaurin gaske ne shi ɗin, ga bala'in ji da kai kamar me, baya ɗaukar rai'ni ko wargi.

"Wajen Kingdom kike son mu je?". Yana magana yana cigaba da shafa arab hairnta.

A hanzarce ta É—ago kai daga kirjinsa tana faÉ—in. "E ina son mu fita waje naga ya yake?".

"Tom shikenan jeki shirya, kada dai ki bari kowa yasan zamu fita".

Tana ƙoƙarin miƙewa sai kuma ta dawo ta ce "Harda auta kada na gaya mata?".

Ya fahimci bazata iya ɓoyewa auta komai da ya danganceta ba, so ko ya hanata ma sai ta faɗa mata koda a sace ne, is better for him da ya kyalesu a yadda suka taso kada ya ce zai yi ƙoƙarin sakawa lallai sai chuchu ta ko ɓoyewa auta wani abin nata, idan ya ce zai yi hakan to tabbas zai haifar da matsala a tsakaninsu, gara ya kyalesu kawai, akwai gaɓar da idan anzo wajen da kansu ma zasu ɓoyewa juna wani abin ba sai an ce masu sirrinsu bane. So dan haka sai ya ce.

"Ki ɓoyewa kowa amma ban da auta, kin manta ke da ita ɗin hanta da jini ne? Ai bazama ki iya ɓoye mata ba na sani, da wani ɗan bakinki a wajen kamar da gaske idan na ce kada ki gaya mata ɗin ba zaki faɗa ba, ni da nasan ko a ɓoye sai kin gaya mata".

Ƙara shigewa jikinsa ta yi tana dariya kamar bakinta ba zai rufu ba, ya harbo jirginta, domin kuwa dama ko ya ce kada ta gayawa auta sai ta faɗa mata koda a ɓoyene kamar yadda ya faɗa ɗin, so sai abin ya bata dariya.

A haka auta ta shigo ta samesu, a kusa da chuchu ɗin ta zauna tare da miƙo mashi wayoyinsa kamar yadda ya ce ta ɗauko mashi. Karɓa ya yi ita kuma Chuchu ta tashi daga jikinsa tana mai cigaba da murmushi.

"Aunty Chuchu dariyar me kike yi?". Auta ta tambaya.

"Yah Jawad ya ce zamu je wani waje".

ÆŠan zaro ido autar ta yi tare da kai kallonta kansa. "Yah Jawad waje zaka kai mu?".

Gera kawai ya ɗaga mata yana ƙoƙarin kunna hasken screen ɗin wayarsa. "Zunaira jeki ki fara shiryawa ba ɓata lokaci kinga yamma ta yi". Ya faɗa yana kan bin screen ɗin wayarsa da kallo, miss call ɗin Yah Rizwan ya gani har uku a wayar tasa.

Da sauri autar ta miƙe ta nufi waje, sai murna take yi. Miƙewa ita ma Chuchun ta yi zata nufi waje da ɗan saurinta. Yana ƙoƙarin kiran number Rizwan ɗin ya riƙo hannunta da hannunsa ɗaya. Juyowa ta yi tana kallonsa, da ido ya nuna mata wajen da ta miƙe a kan ta koma ta zauna.

A hanzarce ta koma ta zauna sai sakin ƙayatattcen murmushi take yi. Murza ƴan yatsun hannunta a cikin nasa ya fara yi dai'dai lokacin da Rizwan ya yi picking na call ɗin.

"Assalamu alaikum Yah Rizwan". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a saman face ɗinta. Murmushin nan nata yana ƙayatar da shi matuƙa.

Daga ɗayan ɓangaren ɗan uwan nasa ya amsa mashi da. "Jawad ina ka yasar da wayar taka kuma tun ɗazun nake kira baka ɗauka ba?".

"Sorry yaya na barota a É—aki ne ina wajen Akka, amma lafiya kuwa?".

Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "E to kusan hakan dai, É—azun na kiraka mu yi magana baka É—auka ba, but yanzu ina yin wani aiki idan na gama zuwa dare sai mu yi magana".

"To amma Yaya lafiya dai ko? Ko dai na zo ne?".

"Kazo kuma?". Ya jefo mashi tambaya a takaice. "E mana yaya nazo idan da wata matsala".

"Ni nace maka da wata matsala? Ba zan kiraka mu yi magana ba sai idan da akwai wata matsala?".

A'a ya amsa mashi da shi.

"Okey tom babu wata matsala, nima ai na kusa kawo muku ziyara, Mammie wai ta yi mun mata, kuma wai dole na zo naga matar ido da ido, ka dai san halinta idan ta sako mutun a gaba, bani da lokacin yin aure a yanzu, amma zan zo ɗin kamar yadda ta buƙata, dan farincikinta kuma nasan ma ba kyaleni zata yi ba idan ban zo ba, ta rinƙa takura mun kena, idan na yi wasa ma sai ta shirya mun abin da ba haka ba, akan ta yi mun abin da zai sani ɓacin rai na har abada gara dai na bi umarninta a hankali mu rabu lafiya".

Guntun murmushi Jawad ya saki kafin ya ce. "Wlh gara kazo ka yi abu da kanka, idan ba haka ba kana can Mammie zata iya sanyawa a aura maka yarinyar da baka ma santa ba, kuma dole ka karɓa ba yadda zaka yi da ita, kaga kuwa idan hakan ya faru kana cikin ƙunci, so is better kazo kaga matar idan bata yi maka ba sai ka ce ta duba maka wata....."

Tarar numfashinsa Rizwan ɗin ya yi da cewa. "Ai kasan zaɓin Mammie ba yadda na iya da ita, dole zan karɓa, kuma nima ai ban isa in ce bana son matar ba ai, a cikin yaran daddy wai ta yi mun mata, kuma dai yarinyar like zata yi dai'dai da ra'ayina duk da cewa ban wani kalli pic's ɗinta da kyau ba, muna hira da Ramish lokacin da Mammie ta turo mun hotunanta, amma dai zuwa anjuma idan na nutsu zan sake duba hotunan da kyau, ko a iya yanzu naga yarinyar like ba laifi".

"Awww wai dama a cikin yaran daddy ta yi maka mata? Tab to ai wannan zaɓi babu canji kenan, baka isa ka ce baka so ba, dole ka karɓa, shikenan Allah ya kawo lokacin yin aurenka na yi farinciki sosai da hakan, amma kasan me yaya?".

A'a Rizwan ya amsa mashi da shi. ÆŠan murza yatsun hannun Chuchu dake cikin nasa da É—an karfi ya yi, hakan yasa ta É—ago kanta tare da kallonta izuwa kansa tana mamakin wai dama yana magana har haka? Bata san sai dai idan basu haÉ—u ba, ko shi da Jaish suna hira sosai idan suka zauna.

"Ina ga idan kazo tare kawai za'a haÉ—a auren namu ayi a wuce wajen". Yana magana yana kallon face É—inta.

Ita ma ta lula duniyar tunani tana kallon face ɗinsa a zahiri, a baɗini kuma tana duniyar tunani tare da mamaki a kan yau dai ɗaya ta ji yayyunta suna maganar aure, abin da bata taɓa ji ba a bakunansu.

"Kai Jawad a ina ka samu mata kuma? Ko dai kaima Mammie ta yi maka irin abin da ta yi mun ne? Ita ta zaɓa maka ko?".

Girgiza kai ya fara yi kamar yana a gaban É—an uwan nasa, sannan ya saki hannun Chuchun tare da É—an rungumo shoulder É—inta, ya dai'dai nutsuwarsa kafin ya cigaba da yin magana.

"Babu wanda ya zaɓa mun ita, ni da kai'na na zaɓota, ita ɗin ta daban ce".

"E lallai Jawad ba shakka kana cikin soyayya, to dai shikenan zamu yi waya anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff, da alama yana yin wani abin ne.

Shiru shi kuma Jawad ɗin ya yi yana jin wani irin a cikin zuciyarsa, haka kawai yau tun da suka fara waya da yayan nasa yake jin babu daɗi a cikin zuciyarsa, yanzu kuma Rizwan ɗin yana katse kiran sai ji ya yi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, bai taɓa jin irin hakan a tattare da shi ba.

Hasbunallahu wani'imal wakil ya furta a cikin zuciyarsa tare da sakin shoulder ɗinta, ya miƙa mata ɗayar wayarsa yana faɗin. "Wayarki babu caji ta mutu, ki rike wannan nawan idan kin gama shiri sai ki kirani da ita, bari nima na je na duba daddy sai na je na shirya yamma tana yi".

Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye tare da nufar hanyar fita haka kawai yake jin zuciyarsa babu daɗi tun da suka yi waya da yayan nasa.
Chapter 133 · 0% Book details