← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 180

Sashe 121

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bai san lokacin da ya miƙe tsaye a dubu ba time da ya ji kumbusa kumbusar kitson da rigimammiyarsa Pretty ta yi mashi. Yau ya shiga uku! Wani amsa zai bawa Mamma kenan? Me zai ce yau kuma? Ya mance da kitson ne da tun a hanya zai warwareta........

(Kamran fans yau ba zata yi maku ta daɗi ba😅 baku da amsar da zaku bawa Mamma, kuna tsaka mai wuya, Pretty ta kai ku ta baroku 😅 ku daɗi soyayya ba? To yau zaku ga soyayya kuwa😅)

Readers me kuke tunanin Mamma zata ce mashi? Wani action zata ɗauka? Shi ma wani action zai ɗauka dan kare kansa kada a raba shi da Pretty? Ga shi ya bayyanawa Pretty ɗin soyayyarsa, ya kenan zata kaya?. To ni dai bari na leƙa KINGDOM OF POWER na dawo, wata kila kafin nan Kamran ya samowa kansa mafita.

𝗞𝗜𝗡𝗚𝗗𝗢𝗠 𝗢𝗙 𝗣𝗢𝗪𝗘𝗥💪🔥

HaÉ—e gabakiÉ—aya family suke a saman dining table dake dining room É—insu na part É—in King. Kuyanga Zubaida ta yi serving É—insu, cikin nutsuwa suke cin abincin nasu. Kowa yana saman table É—in amma banda Yah Jawad, Yah Jaish and Gimbiya Chuchu dake cikin part É—in Akka, taki fitowa, Akka ta fito daning room ta barta kwance a saman gado, wai sai anjuma kaÉ—an zata sha complex or coffee ko dai wani abin mara nauyi, dan bata jin yunwa a yanzu.

Obaid and Omaid duk suna a saman haÉ—aÉ—É—iyar dining table É—in, abincinsu kawai suke ci cikin natsuwa, sai ka rantse da Allah babu su a cikin room É—in, auta duk ta damu na rashin ganin gimbiya Chuchu a room É—in, ita kuma Sarina sai faman hararar Aneesa take yi sarakai waÉ—an da basa shiri, sai mayar mata da martanin hararar Aneesa É—in ma take yi.

Obaid and Omaid dai har yanzu suna nan suna shirya kalar azabar da za su yi wa Mama, basu janye wannan kuduri nasu ba.

King ne ya ɗan yi gyaran murya tare da fara yin magana kamar haka. "Omar dai uncle Abu Abdussalam ya ce ba zai dawo this week ba, na yi na yi amma ya ce wlh na fita idonsa na bar mashi guyson ɗinsa ya kara mashi hutun koda na one month ne kafin ya dawo ya cigaba da karatu, so mummynsa sai ki yi hakuri da shirya mashi walimar sai next month, ku kuma Obaid and Omaid sai next week zaku koma, dama saboda Omar zai dawo ne yasa na yarda zaku koma, to tunda an sake riƙe mun shi nima bari na sake riƙeku a nan kaɗan tun da ma ku baku koma school ba, ke kuma Sarina ina son ki mayar da hankalinki da kyau, kada na kara ji ko ganin wani bako ya zo wajenki, nasa a saki su Yusuf bayan Zafar ya horasu da kyau". Ya kai karshen maganar yana kallon Mommar Zunaira.

Momma É—in dai bata ce komai ba, domin yayanta ne Abu Abdussalam É—in, kuma shi ya hana Omar dawowa, ya zata yi da ya wuce ta yi shiru, bata da ta cewa, ita kuma mummy sai cewa ta yi. "Kai gaskiya uncle Abu Abdussalam ya yi hakuri ya bar nana Guyson É—in mu ya dawo, muna kewarsa sosai fa".

Mama ce ta wani ɓalle masu kallon banza tare da turɓene fuska kamar wadda taga wani abin kyamar.

"Daddy please ka barni mana na je wajen su Uncle É—in, ba sai mu dawo a tare da Yah Omar É—in ba". Cewar auta, ta yi maganar tana turo baki.

"Wani zuwa kuma bayan an buÉ—e school?" King ya bata amsa.

Turo baki kawai ta yi, ta ji babu daÉ—i, tun kafin a buÉ—e makaranta take ta son zuwa, amma aka hanata.

"Bari na dubo Aunty Chuchu". Cewar autar, ta yi maganar tare da miƙewa ta nufi hanyar fita daga room ɗin. Sauri sauri ta yi ta fita dan ma kada daddyn nata ya ce ta zawo sai sun ƙarisa cin abinci, dan Akka ta gaya mashi cewa Chuchu ta ce tana ƙoshe bata jin yunwa da ya tambaya.

Kai tsaye part ɗin Akka ta nufa, dan tasan a can zata sameta, bata jin daɗi ne a duk lokacin da take waje ba tare da Chuchu ba, sun yi matukar shaƙuwa.

Ta zo wucewa ta part ɗin Yah Jaish ne Yah Jawad ya fito daga ciki, bayan ya yi sallolin da suke a kansa ne ya yi wanka ya yi shirin barci sai ya nufi part ɗin Jaish kamar yadda suka saba, a nan suka ci abincin dare suka ɗan yi hira kaɗan, kasancewar yana da aikin da zai yi sosai shi ma kuma Jaish ɗin akwai wani bincike da yake yi a kan wata ma'aikata da suke zargin tana haɗa kwayoyin cuta da kwayoyin magunguna na shan al'umma, suna watsa cutar ta wannan hanyar, a matsayinsa na babban ɗan jarida ya kuma samu information sosai a kan ma'aikatan, shi ne yake ƙoƙarin bincikarsu ya tabbatar da abin da jama'a suke zargin gaskiya ce kafin ya fitar da bayanan, wannan dalilin yasa yau suka yi sallama da juna da wuri, saboda duk suna da tulin aiki a gabansu.

Yana fitowa suka ci karo da auta. "Good evening Yah Jawad". Ta faɗa tana ƙoƙarin wucesa.

"Zunaira ina zaki je kike sauri haka? And then ban hanaku yawo da kayan barci babu hijabi haka a cikin gidan nan ba?".

Dakatawa ta yi daga tafiyar da take yi, É—an turo baki kaÉ—an ta yi kafin ta ce. "Kayi hakuri ba zan sake ba, na manta ne".

Shiru ya É—an yi mata na Æ´an sakani kafin ya ce. "To ina zaki je haka?".

"Wajen Aunty Chuchu zan je, bata zo dining room bane, tana part É—in Akka, shi ne zan je in dubota". Ta bashi amsa.

"Idan kin je ki ce ta zo ina son ganinta, ta same ni a part É—ina". Yana kai karshen maganar yasa kai ya wuce abinsa. Ita ma cikin sauri ta wuce izuwa wajen elevatorn da zai kaita part É—in Akka.

Kwance ta isko Chuchu a saman bed, tana sanye cikin kayan barci riga da dogon wando masu kyau launin maroon color, kayan barcin yana da hula mai kyan gaske, so ta sanya hular a kanta, sai latsa wayar Akka take yi dan Yah Jawad ya kwace mata nata wayar idan baku manta ba.

Saman bed É—in auta ta haye tare da cewa. "Aunty Chuchu shi ne baki nemeni ba ko? To Yah Jawad yana kiranki".

Zaro idanu waje Chuchu ta yi tare da miƙewa zaune. "Nashiga ukuna! Me kuma na sake aikatawa Yah Jawad da yake nemana?! Ni wlh Allah sai na kai shi kara wajen daddy in dai ya sake bani punishment, kuma sai na gayawa Akka ma, na gaji da shan wannan bakin azaba, haba wai ni kaɗai ce a gidan?". Cikin tsiwa ta yi maganar.

Kwanciya ita dai auta ta yi tare da jawo pillow ta rungume haɗe da karɓar wayar Akka dake hannun Gimbiya Chuchun, sannan ta ce. "Allah ni ban san meyasa Aunty Chuchu kike ganin laifin Yah Jawad ba, yana da saukin kai fa, kuma yana da kirki".

Duka ta kaiwa autar a baki tana faÉ—in. "Tun wuri ki yi istigifari, dan Yah Jawad kam sam bai bi hanyar da saukin kai ya bi ba, mugu ne na karshe, kuma wlh sai na gayawa uncle Abbas duk muguntar da ya yi mun, Allah har na fara tsanarsa sosai, amma fa kada ki gayawa kowa na ce na tsanesa fa".

Hannu auta ta kai ta toshe É—an bakinta da shi tare da zaro idanu waje. "Yah Jawad É—in kika tsana Aunty Chuchu? Yayan mu ne fa, innalillahi". Tana magana tana zaro idanu!.

"Ke zaki yi mun shiru ne ko dai kina gaya mun yayan mu ne? To ni dai bana son shi, mugu ne, kuma idan kika faÉ—awa wani ko wata nace hakan daga yau mun bata".

Girgiza kai auta ta fara yi tana faÉ—in. "Ba zan gayawa kowa ba, amma dan Allah Aunty Chuchu ki dai'na cewa kin tsanesa, please, wlh ni bana son jin wannan kalma".

Ƙoƙarin sauka kasa daga saman bed ɗin ta yi tana faɗin. "Zan daina faɗa, amma dai ba zan cire tsanarsa a rai'na ba, sai ya yi ta azabtar da mutane dan mugunta, Allah bari na je na amsa kiransa, idan ya bani wata punishment ɗin kamar a gaban uncle Abbas aka yi, sai na gaya mashi, kuma in gayawa Akka da daddy dukka". Tana kai karshen maganar ta sauko kasa, sai turo baki take yi ta nufi waje, haushi yasa ta manta da cewa kayan barci ne a jikinta kuma bata ɗauki hijabi ba, haka ta nufi part ɗinsa tana kunkuni a cikin ranta, sai faɗi take in dai ya ci zalinta yau to wlh sai ta kai kararsa wajen uncle Abbas, sai dai ya yi duk abin da zai yi mata mugu kawai.

Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo part ɗin nasa. Daga jin yadda ta yi sallamar kasan a ƙule take da bakinciki har wuya.

Babu kowa a parlourn, kuyangu masu yi mashi gyara ma sun kammala aikinsu sun fice. Kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa. Ƙasa ƙasa ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga ba tare da jira izininsa ba, dan ita fa haushin da take ji yasa ta manta ma a ina take tukun nan, sai kunkuni take yi tana tsine mashi a cikin ranta.

Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya..................

Lokacin shan Maltina ta yi🥱

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 15/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
Chapter 121 · 0% Book details