← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 180

Sashe 131

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata yi mashi musu ba, dan tasan dokansu, dan haka sai ta karɓi cup ɗin ta miƙe tare da yi mashi godiya ta nufi hanyar fita. Cigaba da yin hiransa da auta ya yi suna ta sakin murmushi, duk auta ta ƙosa ya dawo, Abu Abdussalam kuma ya hana shi komawa, sai fakewa da ciwonsa Abu Abdussalam ɗin yake yi yana kara rike shi, baya son rabuwa da shi ne, shi ma kuma King Zuhair yaki hakura ya bar mashi guyson ɗin, dan bayan auta ba wanda yafi so biyun Omar, yana kaunarsa, amma ya zai yi? Dole ya hakura ya cigaba da lallaɓa yayan nasa har ya yarda ya barshi ya dawo, shi kuma King Zuhair ɗin yaki barinsu twin's su dawo, ga shi yanzu an buɗe school nasu this week, so ya zama dole su dawo, shiyasa King Zuhair duk ya bi ya damu sosai, Abu Abdussalam kuma yaki kula shi.

Har Leesharh ta kai tsakiyar parlourn sai kuma ta juyo, cike da tsoro ta ce. "Yah Omar me yake damunka ne?".

Kansa na'a duke kan laptop É—in ya É—ago da dara daran idanun nan nasa. "Ciwon ciki nake fama da shi since ina da two years a duniya, amma ina taking drugs yanzu da sauki, and Yah Raj yana treating É—ina very very well". Ya bata amsa fuska ba yabo ba fallasa.

Addu'a sosai ta yi mashi na Allah ya bashi lafiya, sannan ta wuce zuciyarta a cike tab da tunani, Allah sarki ciwon ciki tun yana ƙarami, Allah yasa dai ba da shi ma aka haifesa ba, ashe dole ya yi kuka, ciwon ciki waje ƴa mace ma mugun muni garesa bare kuma namiji, ciwon cikin ɗa namiji ai babban haɗari ne ba kaɗan ba, suna shan bakar azaba sosai, wani ma nan take yake kashe shi, amma Alhdulillah shi Omar nasa tana jimawa bata tashi ba, sai ya kai wata shidda bai ji ciwon ba, sai dai idan ta tashin mashi kuma kamar ba zai rayu ba, Dr Raj ne likitansa, shi yake kula da shi sosai da sosai, shiyasa basu yarda su yi nisa da shi sosai, dan a kowani lokaci ciwon tana tashi, shiyasa suke lallaɓa shi suna kula da shi sosai, komai yake so suna yi mashi ba ɓata lokaci, shi kuma yana da kirki sosai, kusan halinsa ɗaya da Zunaira, sai dai shi baya taɓa yarda ace mashi bai iya abu ba, idan kana son ka yi faɗa da shi to ka ce ka fishi iya abu, yanzu zaku ɓata, shi dai gani yake jarumi ne shi ya iya komai ato.

Sosai ya ji matuƙar daɗin addu'oin da ta zuba mashi, harta auta da ta kasan kunne tana sauraronsu ta ji daɗin addu'ar, sai ta ji ta kara son Leesharh ɗin sosai, ita dai tana kaunar mai son ƴan uwanta.

Tas Leesharh ta shanye cappucinon da ya bata, sai ta ajiye nata pina colada da ta ɗauko, ta ji nasa yana da wani irin shegen daɗi sosai, kamar a kara mata ta ji, sai tunani take yi ko waye ya haɗa mashi wannan gaɗaɗɗen haɗin haka? Bata san shi guyson in dai ba Ummie ce ta girma mashi abu ba to ba zai ci ba, sannan shi abincinsa ba kamar na sauran ƴan gidan yake ba, dan shi yana kan tsarin magani, so abincinsa ya banbanta da nasu, Ummie da kanta take haɗa mashi komai da zai buƙata.

Sai tanɗe baki take yi, da haka ta kwanta zuciyarta cike da tunanin kirki irin na Guyson, ga shi fuskarsa ba yabo ba fallasa, ga shi kuma ya iya murmushi mai kara mashi kyau sosai, ta wani ɓangaren kuma idan ta tuna yadda taga Dr Raj sai ta ji gabanta ya yi wani irin bugawa, tsoro ya kamata, da haka dai barci ɓarawo ya saceta.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥

Mammien Yah Jawad.

Zaune take a saman wani irin shinfiɗa ta alfarma irin na gidan sarauta mai kwalliya da gashin jimmina, shinfiɗar ta haɗu sosai da sosai, tana cikin alkyabbarta, ta zuba gwala-gwalai ɗin nan a hannu da wuya dam kamar ba za'a mutu ba, daga samanta har kasa dukiya ne aka narka. A in da take zaunen nan cikin minti ɗaya idan ta buƙaci kuɗi sama da 100 million a take za'a bata, kada ku manta Rizwan ɗan farinta ne, ga Yah Jawad shima yana da nasa company's ɗin, uncle Abbas ba'a magana, kuɗi ta ko'ina, amma ita fa duk basu a cikin plan ɗinta, sai ka rasa me take nema a duniyar nan to.

Ta É—aura kafa É—aya biya É—aya, ta baza alkyabbar nan tata a wajen gabaÉ—aya, ta wani dake sai É—age hanci sama take yi, tana zaune ne a wajen shan iskan uncle Abbas da yake a cikin part É—insu, uncle Abbas É—in kuma baya nan, ga wasu Æ´an matan kuyangu biyu a kusa da ita, É—aya tana zaune ta gefenta na dama, É—ayar kuma tana zaune a gefenta na hagu, ga wasu uban tulin kayan marmari dake a cikin wani kyakkywar kwando da suka jibgemata a gabanta, very fresh kayan marmari ne, sai wani fadanci take yi kamar ita ce Queen of the Kingdom É—in na ainahi, ko mummyn Gimbiya Chuchu uwar gidan King Zuhair bata irin wannan fadanci sai ita.

A hankali iskar bishiyoyin dake wajen suke kaÉ—ata, ga kuyanga É—aya tana yi mata fifita da maficin gashin jimina, an kawata in da take zaune É—in da luntsuma luntsumar throw pillows masu girma.

Wata Kuyanga ce ta shigo cikin wajen, sai sauri take zubawa kamar zata kife kasa, da alama an É—ebo gulma fal ciki, shiyasa ake sauri kada ciki ya fashe gulmar ta zube a hanya.

A gaban wannan shunfuÉ—a ta zo ta zube gwiwowinta tare da fara zuba kirari na girma ga Mammie É—in. Kara dakewa ta yi cikin alkyabbar nan tata. Sai da ta É—auki a kallah minti biyar tana sauraran wannan kirarin kafin ta É—agawa kuyangar hannu alamar ya isa haka ta dakata, sannan cikin nuna isa ta yi wa kuyangun dake wajen nata umarni da su bata waje zata yi magana da wannan kuyanga da ta shigo a yanzu.

Cikin hanzari suka miƙe suka fice daga wajen. Akwai sadaukan yaki biyu dake gadin kofar shigowa wajen shan iskan, dan tsaro.

Ko da suka fita sai da ta sake É—aukar good two mins kafin ta ce. "Bintu meyafaru kika shigo da sauri haka?".

Ƙasa ta ɗan yi da kai kafin ta ce. "Allah ya kara maki tsawon rai, farar mace mai farar zuciya, Allah ya ja da ranki wlh yanzu ne ma Yah Jawad yake ƙara kula Gimbiya Chuchu sosai, daga majiya mai karfi na jiyo cewa har yanzu bai dai'na kulata kamar yadda kika hana shi ba, yanzu ma sai abin da ya cigaba sosai". Cikin girmamawa ta yi maganar.

Shiru Mammie ta É—an yi kafin ta ce. "Shikenan je ki ki cigaba da yin aikinki, ki saka ido sosai, sannan kada ki kuskura ki kawo mun maganar da ba haka ba, ki tabbatar da ingancin magana kafin ki kawo mun".

"In Sha Allah ranki shi dade, Allah yaka maki girma da ɗaukaka". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi waje.

Da kallo Mammie ta bita har ta fita, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Bintu tana fita sai ga kuyangu biyun can sun dawo ciki. Wajen zamansu suka koma suka zauna, suna zama wayarta dake saman throw pillow dake kusa da hannunta ne ta fara ruri alamar shigowar kira.

A hanzarce ɗayar kuyangar dake ta wannan bangaren ta yi sauri ta ɗauko wayar ta miƙa mata. Sai da ta sha kamshi kafin ta karɓi wayar.

My son, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen É—in wayar, ajiyar zuciya ta sake saukewa kafin ta É—auki kiran.

Sallama ta yi cikakke. Daga ɗayan ɓangaren Rizwan ya amsa mata cikin girmamawa tare da ɗaga mata gaisuwa.

"Lafiya lou Alhdulillah my son, ya aiki?".

Da Alhdulillah ya amsa mata kafin shi ma ya jefa mata tambayar ya gida ya kowa da kowa.

"Kowa yana nan lafiya, amma ka tambayeni kowa baka tambayeni ya matarka ba?".

Cikin nuna halin ko in kula ya ce. "Wacece kuma matata?".

"Wai kai Rizwan kullum sai ma na tuna maka wacece matar taka ko? Ya yi maka kyau, ka cigaba da yi mun kamar ni kakarka ce".

"Kai Mammie bafa haka bane, duk lokacin da zaki gaya mun wacece hankalina yana kan wani abin ne, but yanzu gaya mun zan rike ba zan manta ba".

Shiru ta É—an yi kafin ta amasa masa. "Jannat mana ko in ce Chuchu tun da da shi kuka fi saninta, tana ta kara girma, yakamata fa ka kawo mana ziyara, ni kam yanzu fa kun kai almost 12 to 14 years haka rabonku da masarautar nan fa ko? To yakamata ku zo gaskiya, matarta ta girma kuzo ku yi aure sai ku koma".

Chuchu kuma?! Tashin hankali to me Mammie take nufi? ta dai san Yah Jawad yana son Chuchu, kenan dama da gangan take hana shi kulata dan Rizwan take sonwa? To amma menene banbancin Rizwan ɗin da Jawad ɗin da zata hana kanin ta yi wa yayansa sha'awarta? Akwai matsala babban kuwa in dai haka ne, domin kuwa in dai tasa Rizwan ya fara son Chuchu shi kuma Jawad fa? Wai ni kam me Mammie take so ne a duniyar nan? Ita sam bata son zaman lafiya! Ba'a taɓa gane ina ta dosa sam sam! Mata kamar wata aljana ko shaiɗaniya! Sai iya haɗa makirci da faɗa! So take ta kashe Jawad ne ko me? Bawan Allah shekara kusan 11 yana dakon soyayyar Chuchu? Anya wannan abin ba zata tarwatsa mashi zuciya ba? Yayansa uwa ɗaya uba ɗaya, tashin hankali akwai rikici kam ba kaɗan ba, Mammie da alama zata kashe ɗanta da hannunta, ko me dalilinta na yin hakan kuma? Mu dai je zuwa, sannu a hankali komai zai warware. Hmmm ga shi shi kuma Jawad bai sani ba, yana ta wahalar da Chuchu har yasa ta fara tsanarsa, akwai rikita rikita ba kaɗan ba kuwa a nan gaba! Da alama nan gaba kaɗan kingdom of power zata kama da wutar bala'i, kai tabɗijam!!!.
Chapter 131 · 0% Book details