← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 180

Sashe 174

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kina mamakin ya aka yi nasan burinki ne Aunty? To bari ki ji ranar da kika je gida ina jinki ke da mama kuna magana a kan ke dama ba Yah Abbas kike so ba, King Zuhair kike so, dan burin mulki kike da shi, kuma ko za'a mutu ko za'ayi rai, ko rai nawa zaki iya salwantarwa domin ki auri King ki haifi maganin Crown of Kingdom of power!!".

Kara zaro idanu sosai Mammie ta yi, bata taɓa tunanin bayan mahaifiyarsu akwai wadda tasan da wannan magana ba, sirrinta ne kuma burinta!.

"Aunty ki dai'na yin mamaki fa, kuma ki dai'na ƙoƙarin hanani mallakar abin da zuciyata take so, Crown na kingdom of power rawani ne da kowani basarake yake burin samunsa, kujerar mulkin kingdom of power kujerace da jiga jigan sarakuna masu karfin iko suke fatan su zauna a kansa, masarautu ba adadi ne a ƙarƙashin wannan masarauta, duk wani karfin ikon mai karfi a faɗin ƙasar nan dama maƙota ƙasashe duk a ƙarƙashin King Zuhair suke, a haka kike son nayi wasa da wannan dama? Sanin kanki ne fa shiga in da King Zuhair yake ma ba ƙaramin abu bane, ke kanki kin san ko da yatsa ka nuna gate na farko na shigo cikin masarautar nan sai an datse maka hannu, duk wani karfin iko da isa tana nan! Wlh kamar yadda kika ce ko rayuka nawa zaki iya salwantarwa domin ki mallaki King, ni ma hakance, zan iya aikata komai dan na mallakesa, dan haka da ni dake lokacin buga wasa a tsakaninmu ya yi, kowacce ta gwada sa'arta kawai....." E lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!.

Tana kai karshen maganar ta miƙe fuuu abayar jikinta na ja a ƙasa ta nufi waje, bata zame ko'ina ba sai family part ɗin King, kai tsaye wajen mummy ta nufa, dan ita mummy ƴar baruwa na ce, kowa nata ne, kowa ya zo gidan hannu bibbiyu take tarbansa, shiyasa suke sonta, tana da hakuri haɗi da kawaici, ainahin mahaifiyarta ƴar Nigeria ce, kuma ita ba yar kowan kowa ba ce, tana da taimakon mutane da kuma saukin kai sosai, ba kamar Mama da Momma ba, ku kunsan Momma tana da kyan zuciya, wargi ne kawai bata ɗauka! Iadan ka kawo mata ba dai'dai ba yanzu zata nuna maka cewa jinin Modarawa ne yake gudu a jikinta. Mama kuma sai ka rasa me matar nan take so a duniya, sai bala'in masifar tsiya, ga ɗan banzan kishi na masifa.

Da kallon mamaki Mammie ta bi Aliyah har ta kurewa ganinta, mamaki da al'ajabi ya hanata yin magana, tunani take yi wai yaushe Aliyah ta girma da har take cewa su ƙara ko wacce tata ta fisheta?. Ita ma fa Mammien ba wata babba bace take wani cewa yaushe Aliyah ta girma, Aliyah ɗin ce fa mai bi mata a wajen haihuwa, kada ku manta Sarina ce ƴarta ta farinta, so ita ma ba wata babbar mace can can bace, iyayi ne kawai.

Wayarta ta ɗauka tare da miƙewa ta nufi cikin bedroom ɗinta tana faɗin. "Dani kike yi Aliyah, yaushe ma aka haifeki da har zaki ce mu ƙara akan muradina? Ke har kin isa ina son abu kuma a yunwace nake da na cinma burina a kansa ki ce kema kina son shi? Wlh ba'a haifeki ba! Tsab zan gyara maki zama, zan gwada maki banbancin shekaru..."

Ta kai karshen maganar tata tana zama a gefen bed É—in nata, dai'dai lokacin kuma wadda take kira a waya ya É—auki kiran. "Misalin karfe 1 dare mu haÉ—u a in da muka saba haÉ—uwa". Shi ne abin da ta gayawa wanda ta kira É—in. Tana gama faÉ—in hakan ta katse kiran tare da buga uban tagumi tana tunani.

(Ni kam na ce uncle Abbas da King sun ga ta kansu, shi yanzu uncle Abbas kenan ya Mammie zata yi da shi tun da ta ce yayansa take so? Shi kuwa King yaga ta kansa kowa son shi yake yi, bawan Allah bai ma san ana yi ba, momma ki shirya ga kishiyar karfi da yaji na dole nan Aliyah tana zuwa, zaki tashi daga amarya 😅 Mama kuma kishi zai karu😅 family part ɗin King zai kama da wuta, 🔥 mummy baiwar Allah dai babu ruwanta, da rabon za'ayi yaki ba kaɗan ba, da rabon su Ramish zasu yi kisan kai ko na ce kashe kashe😅 hmmmm KINGDOM OF POWER kuma yanzu nasu wasan zai fara🔥 ina commander ZAFAR sai ku shirya, ni dai bari na tafi Nigeria gidansu Zainab dan jin ya ake ciki).

GIDANSU KHADIJAH 😥💔

Hakura maman Zainab ta yi ta karɓi wannan ɗaki da Hauwa ta zaɓa mata, a ciki ta kwana, bakinciki kamar zai kasheta, ta fara danasanin zuwanta sabon gidan nan, dan bakinciki kala kala Hauwa take kunsa mata, tsabar mugunta dan ta kuntata mata ma da daddare tasa baban Zainab ya sanyata ta yi masu girkin dare, har da gaya mata kalar abincin da take son ta girka masu Hauwar ta yi.

Idan ran maman Zainab ya yi dubu to ya ɓaci, amma haka ta daure ta yi girki tare da taimakawar su Khadija, ita kuwa Hauwa tun yamma da ta gaya mata ga abin da zata yi masu, suka ci wanka ita da baban Zainab ɗin suka nufi kasuwa, ta tasa shi a gaba wai sai dai su je ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq, haka ya shirya suka tafi, maman Zainab ta yi girki tare da su Khadija.

Sai can wuraren karfe 9 na dare su Hauwar suka dawo, a lokacin maman Zainab sun kammala girki ta zubawa su Khadija sun ci nasu, ita ma ta É—an tsakuri kaÉ—an ta ci, bakinciki ya hanata cin abincin na kirki, so kaÉ—an ta tsakura.

Tana gama cin abincin bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ta wuce É—akinta ta kwanta, su Khadija ma suka wuce nasu da Hauwa ta basu suka kwanta, Zainab ta yi addu'ar barci ta kwanta, ita kuma Khadija ta É—auro alwala, dan kwanciya bai ganta ba iyayenta suna cikin masifa.

Maman Zainab tana kwanciya sai ga kiran Sadiq ya shigo cikin wayarta, haka kawai ta ji gabanta ya faÉ—i da ganin kiransa. ÆŠauka ta yi cike da fargaba. A hankali ta yi sallama kamar mai jin tsoron wani abin ko wadda bakinta yake ciwo.

"Assalamu alaikum Maman Zainab na manta ban gaya maki ba ni fa ina hanyar Kaduna, da farko massages naso in tura maki, amma sai dai nace bari kawai na kiraki". Cewar Sadiq É—in.

A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar gadon, zaro idanu waje ta yi. "Sadiq me zaka je yi a Kaduna? Kuma sai ka tafi baka sanar da ni ba? Yanzu da ka tafi ya kake son na yi da rai'na? Da waye zan yi shawara? Waye zai rage mun raɗaɗin da yake damuna a rai'na?! Ina kake son na sanya rayuwata na ji daɗi? Mutuwa kuke son nayi ne?". Tana magana wasu zafafan hawaye suna biyo ƙuncinta.

"Ki yi hakuri maman Zainab, dole ce tasa na tafi, amma kinsan ni ma ba zan so rabuwa dake a irin wannan hali da kike ciki ba, shiyasa nace maki da farko sms naso in yi maki ba kira ba, saboda kada na ji kukanki, da ina turo maki sms zan kashe wayata, amma ki yi hakuri Allah yana tare da ke!!".

"Sadiq to me yayi zafi da zaka tafi ka barni? Kana da wata Æ´ar uwa a duniyar nan biyu na ne? Ko dai ka dai'na sona ne". Cikin raunin murya haÉ—e da karyewar zuciya ta yi maganar.

"Ko ɗaya maman Zainab, ban dai'na sonki ba, yama za'ayi na dai'na sonki? Ai ba zai yiwu ba, yanayi ne yazo da dole na yi nisa dake, idan ba haka ba zan iya aikata kisan kai wadda kema kanki ba zaki so na yi hakan ba, ba zan iya jurar cin kashin da suke yi maki ba, baban Zainab ya zo kasuwa da yamma, ya karɓi komai da komai nasa, mun yi lissafi da shi da Hauwa, komai ya fita yadda yakamata, kuma mun yi a rubuce yasa hannu na sa hannu a kan na mayar mashi da komai ɗinsa, shi ne naga ya dace na koma gida in je in kula da mama".

Magana ta gaskiya ba hakance tasa Sadiq ya bar garin Kano ya kama hanyar Kaduna ba, abin da yasa shi ne, wani irin mummunar cin mutunci baban Zainab da Hauwa suka yi mashi a kasuwa, ga lissafi sun yi dallah dallah amma Hauwa ta ce da baban Zainab karya ne ya saci wasu kuɗaɗen, wai ba zai yiwu ace iya wannan ribar kawai aka samu a shagon ba, gudun irin haka fa yasa Sadiq ɗin yake ciyar da su maman Zainab ɗin da kuɗinsa, harta su maman Haidar idan suka zo kasuwa a kan basu da abincin ci daga aljihunsa yake cire kuɗin ya basu, duk dan kada ya taɓa naira biyar ɗin baban Zainab, amma da yake Hauwa makirace, kuma tana jin haushin marin da ya yi mata, sai da ta sa baban Zainab ya ci mutuncinsa a bainan nasi, ya yi mashi kaca kaca, shi kuma Sadiq ga shegen zuciya kamar ɗan kuturu, hakan yasa ya haɗa kayansa ya nufi gidan iyayensa in da zai bugi kirji yace ya isa a can, har police Hauwa ta ce baban Zainab ya kira su zo su tafi da Sadiq ɗin, da kyar masu shagunan kusa da su suka bata hakuri ta hakura, mata kamar wata kanwar shaiɗan. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru a tsakaninsu da yasa Sadiq ɗin ya bar Kano, yaki gayawa ƴar uwa tasa gaskiya ne kawai dan baya son ya ɗaga mata hankali, baya son kara mata zafi a kan zafi, shiyasa ya ce mata sun yi lissafi lafiya lou!!.

Sosai maman Zainab ta rinƙa kuka, sai hakuri yake bata ita kuma tana yi mashi magiyar ya dawo dan Allah, daga shi sai su Khadija take gani ta ji daɗi a rayuwarta, sune kaɗai suka rage mata, sune kaɗai farincikinta a yanzu.
Chapter 174 · 0% Book details