← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 180

Sashe 155

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsananin ruÉ—e autar ta fara yin magana. "Aunty Chuchu na shiga uku, wani abin ne ya fito mun a kirjina, wanka na je yi sai na jishi ya fito mun kamar dutse, ko dai asiri aka yi mun ne? Dan na ji ance ana iya yi wa mutun asiri kala kala". Tana magana hawayen suna ganganro mata a saman fuskarta.

Hakika akwai shaƙuwa mai karfi a tsakanin Zunaira da Chuchu, duk abin da yake damun Zunaira ba zata tinkari kowa ba sai ta fara tunkarar Chuchu ta gaya mata kafin ma ta gayawa Mommarta, basu ɓoyewa juna komai, yanzu haka abin da Yah Jawad ya yi wa Chuchun jiya auta tana nan da shi a ranta zata gayawa Chuchun bata manta ba, abin da yasa jiyan bata sami damar gaya mata ba barci ne ya ɗauketa, lokacin da suka dawo daga wajen yawon nasu, suna shigowa cikin gida suka isko su Sarina a parlourn, shi ne suka zauna yin hira da su har lokacin cin abinci ya yi, ita kuma Chuchu ta shiga ɗaki ta canza kaya, bayan sun ci abinci ne suka wuce ɗakin Chuchun da nufin in sun je auta zata gaya mata ga abin da Yah Jawad ya yi mata a gidan zoo da kuma sauran guraren da suka je, to suna shiga cikin ɗakin kuma Yah Jawad ya kawowa Chuchu wayarta, bayan ta karɓa sai ta ce ya bata number Yah Rizwan, ba musu ya bata, bai kuma kawo komai a ransa ba dan yayansu ne ai, ita kuwa ta sanya number a wayarta ta kira Rizwan ɗin, bai ɗauki call ɗin ba a lokacin, hakan yasa ta ajiye wayar ta nufi toilet dan yin wanka.

Ita kuma auta tana kwance a saman gado tana jiran ta fito ita ma ta shiga, yau a ɗaki ɗaya zasu kwana. Bayan ta fito ta yi shirinta cikin kayan barci masu kyau da tsada, sannan ta haye gado, ita kuma auta ta miƙe ta shiga toilet ɗin da nufin idan ta yi wanka ta yi shirin kwanciya sai tazo su yi hira ta sanar da Chuchun.

Sai dai ko da ta fito daga wanka sai ta tarar da Chuchun tana waya da Yah Rizwan, hakan yasa da ta gama shiri ta zo ta kwanta a kusa da chuchun, tun tana sauraron hiran da suke yi da Yah Rizwan É—in har barci ya yi awon gaba da ita, washegari da safe kuma suka tashi da batun rashin lafiyar mama, wannan dalilin yasa autar bata samu damar gaya mata ba. To mu koma kan labarinmu.

"Menene ya fito maki ɗin in gani?". Chuchu ta faɗa tana zaro idanun nan nata waje kamar zasu faɗo ƙasa, ta tsorata ita ma tun kafin tasan menene.

A hanzarce auta ta fara zuge zip ɗin rigarta ƙasa tana faɗin. "Ga shi nan ki kallah". Ta yi maganar tana sauke wuyar rigar tata kasa tare da nunawa Chuchun breast ɗinta.

Wani irin dariya ne ya kubcewa Chuchun, dariya ta shiga yi har da rike ciki. Baki auta ta saki tana kallonta. Sai da taga dariyar tata ba mai karewa bane yasa ta fasa mata kuka mai É—an sauti wadda hakan yasa dan dole Chuchu ta tsayar da dariyar tata.

"Yanzu me kuma abin dariya a nan? Kina ganin abu ya fito mun amma kike mun dariya". Autar ta faÉ—a cikin kuka.

"To auta ba dole na yi dariya ba".

A kule ta ce. "To idan kika tsaya kina dariya na mutu fa?".

Murmushi kaÉ—an Chuchun ta sake yi kafin ta ce. "Ba zaki mutu ba, ai ba wani abin bane, girma ne ya zo maki, ke baki yi mamakin ya aka yi ni da su aunty Aneesa muke da breast manya ke baki da shi ba? To kema naki ne ya fara fitowa, sai a dai'na wasa da su Hoorain, a dai'na yi wa maza magana, yanzu an girma, eyee autarmu ta girma ta fara kirgan dangi". Tana magana tana guntse dariya.

Sai yanzu auta ta fahimci menene, nan take ta ji wani irin kunya ya kamata, da sauri ta mayar da rigarta tana turo baki, danasanin meyasa ta nunawa Chuchun ma ta fara yi, har da wani cewa da tasan haka ne ai ba zata gayawa kowa ba, da farko ma Yah Jaish ta so fara zuwa ta gayawa kafin ta gayawa Chuchun sai ta gayawa Mommarta, ashe Allah ya taimaketa ma da bata je ta gayawa Yah Jaish ta kuma nuna mashi ba.

Nima na ce amma da ta je ta gaya mashi zan yi mata dariya kam, yanzu ma n yi mata, Chuchu ta kalle mata tula tulanta da suka fara fitowa😅😅😅😅😅 bye my people's sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu.....

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 5/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________46🔥

"Meyafaru our Auta?". Ta tambayeta tana É—an murmushin.

"Babu komai Aunty Chuchu". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, ta kuma yi maganar tana sanya hannu ta goge kwallar da yake a saman face É—inta.

ÆŠan rungumota kaÉ—an Chuchun ta yi tare da É—an bubbuga bayanta alamar rarrashi tana É—an tsokanar.

"Sai ki sanar da Yah Omar ko?". Cikin zolaya ta yi maganar.

"Allah Aunty Chuchu ki bari mana bana so". Ta yi maganar kumatu a kumbure kuma cikin shagwaɓa.

"To na bari, amma kin manta ke da Yah Omar akwai amana ne? Bafa ki ɓoye mashi komai shi ma kamar yadda baki ɓoye mun, wannan ne yanzu ba zaki iya gaya mashi ba? Lallai Auta kenan yanzu babu amana da nuna kauna? Kin manta yawan gaya mashi da kike yi cewa shi ne pleasurenki? Tun ba'a je ko'ina ba an fara ɓoyewa pleasure abubuwa". Still cikin zolaya ta yi maganar.

"E ɗin Aunty Chuchu na ɓoye mashi ɗin, kuma kema Allah da ban nuna maki abuna ba".

Wani irin dariyar iyashege ta tuntsure da shi, cikin dariyar take faÉ—in. "Kai menene kuma abunki É—in to? Bashi da suna ne".

A ƙule Autar ta raba jikinta dana chuchun tare da ɗaukar wata jibgegiyar pillow da ta sha rigar bedsheet mai matuƙar tsada da nufin ta fara dukan Chuchun da shi.

Ai da gudu Gimbiya Chuchu ta sauka daga gadon tana faÉ—in. "Bari ma na je na gayawa su Aunty Sarina har da Aunty MieMie cewa Auta ta fara kirgan dangi, ta girma".

Da gudu Autar ta biyota tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan barki ba kuma mun ɓata, kada ki sake yi mum magana, babu ruwana dake daga yau". Tana magana tana binta da gudu.

Kai tsaye part É—in King Chuchu ta nufa sai dariya take yi kamar wata zararriya, yau Auta na neman kasheta da dariya.

Tana gudu tana waigo Autar taga ko ta kusa isota har ta shiga parlourn King, sai waigowa take yi bata ankaraba ta ji fa bugi faffaɗar kirjin mutun. Baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa tare da ƙoƙarin dakatar da dariyarta da yake shirin zama kuka duba da yadda ta yamutsu fuskarta, da alama ta bugu sosai saboda gudu take yi.

Wuyar doguwar rigar jikin nata ya riƙo tare da janyota gaba ya tsayar da ita a kan kafafunta bai bari ta faɗi ƙasa ba.

Auta ko a jikinta da gudu ta ƙariso wajen ta fara sauke mata wannan pillown a gadon bayanta tana faɗin. "Kuma ko na dakeki ba zan huce ba, mun ɓata kenan, tabbas mun ɓata da gaske!".

A hanzarce Jawad ɗin ya sanya hannunsa ya tare dukar da Autar take kawo mata ba kakkautawa. Saura kaɗan Chuchun ta kifa a kan kirjinsa saboda dukan da Autar ta yi mata ta baya da pillown na ƙarshe yasa ta yi gaba kamar zata kifa, shi kuma a lokacin yana sanya hannunsa zai tari pillown kenan, hakan yasa ta kusa kifawa a kirjin nasa.

"Sorry our Auta tuba muke yi". Yah Jawad ya faɗa yana riƙo pillown da hannunsa ɗaya.

"Allah ya Jawad ni na zan yi sorry ba, yau mun ɓata da Aunty Chuchu baram baram!". Tana magana tana kwaɓe fuska tare da turo baki.

Cike da iya shege da tsokana tana murje gaban goshinta ta ce. "Yah Jawad to ka tambayeta me nayi mata da zata kama dukana haka?". Tana kai karshen maganar wani dariyar ne ya so kubce mata duk da turɓune fuska da ta yi lokacin da ta buge da kirjinsa, maganar a tambayi Autar yasa ta ji dariya ya zo ya kori kukan da take ƙoƙarin yi wa yayan nata.

Kuka Autar ta sanya masu tare da juyawa zata bar wajen dan ta ji cewa Yah Jawad ya tambayi me Gimbiya Chuchu ta yi mata. A hanzarce ya riƙo hannunta bai bari ta bar wajen ba. Cikin sanyin murya ya ce. "Zo Autarmu, zo ki gaya mun me ta yi maki in rama maki yanzun nan".

Habawa me Chuchu zata yi face dariya, shi Yah Jawad fa bai san tambayar me Chuchun ta yi mata bane yasa zata gudu ya zo yana wani tambaya shi ala dole zai rarrasheta kuma ya rama mata.

Hawayen gaske ta fara yi mashi bata ce komai ba, sai wani irin harara da take wurgawa Chuchun da waÉ—an nan dara daran idanuwan nata. Shi dai Jawad ya rasa gane me matsalar, sun saka shi a duhu.

"Ki faÉ—i me na yi maki Yah Jawad ya rama maki ya ce". Chuchu ta faÉ—a ita ma tana jefa mata hararar.

Bakinciki kamar Auta ta sanya hannu a kai ta kurma ihu. Faɗawa jikin Yah Jawad ɗin ta yi tana ɓoye fuska tare da fara yin hawayen gaske, dan ranta ya ɓaci sosai, Chuchu ta kureta.

Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Yah Jawad É—in ya jefawa Chuchun kafin ya sassauta muryarsa kasa sosai. "Me kika yi mata Jannat?".
Chapter 155 · 0% Book details