← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 180

Sashe 145

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefensa, dan shi kansa ayabar ta burgesa, kamar zai tambayeta a ina suka samo ayabar, sai kuma bakinsa ta yi mashi nauyi ya kasa iya tambaya. Shi dai yasan ba shi ya kawo masu wannan ba, wanda yake kawo masu ba irin wannan bane, red banana yake kawo masu, su ne suka fi yawa ta wannan yankin, wannan da ta bashi kuma green ne.

"Pretty yau Kamran É—in kike gudu ko? To ni dai ban apple É—aya bari na sha na kwanta na yi barci, malam Kamran yau dai Pretty na gudunka". Cewar Sweetie.

Yake ya ɗan yi mai kama da murmushi kamar Sweetien tanan kallonsa, sannan ya ce. "Bani take gudu ba, snake take gudu, ni bari na je zan dawo yanzu ba jimawa, zan duba tekun nan ne". Ya kai karshen maganar tare da ɗaukar ayabar da ta bashi ya miƙe tsaye.

"Kamran". Pretty ta ambaci sunansa a hankali. Zuba mata ido ya yi ba tare da ya amsa ba.

"Kuma tafiya zaka yi?". Ta tambaya ita ma tana kallonsa, kun san idan ya zo tafiya dama bata son rabuwa da shi, kuma tana jin tsoron rakasa, zai ta fi shi kaÉ—ai kuma tana jin kamar ba zata iya zama ya tafi ya barta ba, bata son ya matsa daga kusa da ita ko nan da can.

Da e ya amsa mata, shi kansa baya son matsawa daga kusa da ita kun san haka, amma kuma neman hanyar da zata ɓulle masu abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesa, so dole ne ya je domin neman mafita.

Narai narai da ido ta yi mashi zata yi kuka, ga gwandar daji a rike a hannunta ta sha rabi bata ƙarisa sha ba.

"Please Pretty don't let your tears to come out, zaki sanya zuciyata ta yi mun zafi, yanzu fa zan dawo". Ya yi maganar cikin wata iriyar murya wadda da ka ji ta zaka san shi ma baya cikin jin daɗi, dan sun shaƙu sosai har ta kasance in sun haɗu suka zo rabuwa zuciyarsa kuka take yi, ita kuma Pretty kuka a zahiri take yi, Sweetie ma kukan zuci take yi bana zahiri ba idan zasu rabu, Pretty ce sarkin hawaye mai yi a fili kowa ya gani.

"To Kamran ka bari mana sai zuwa gobe sai ka je ka yi checking na abin da zaka duban, now ka zauna da mu please". Cewar Sweetie da a kullum kaunar Kamran ɗin karuwa yake yi a ranta, mutumin da bata san shi ba, bata taɓa ganin face ɗinsa ya yake ba, bata san ya zuciyarsa na ainahi yake ba, ta iya yiwuwa a wajensu ne yake mutumin kirki, a bayansu ba haka yake ba, duk bata san wannan ba, ita dai zuciyarta na sonsa, shi kuma zuciyarsa na son Pretty, son da yake yi wa Pretty ma ai ko kansa baya yi wa hakan, ta zama tamkar bugawar numfashinsa, komai yake yi yana tunaninta, tun ranar da aka haifeta, ya ɗauketa tana tsallara wannan ihu, tun da lokacin ta shiga cikin zuciyarsa, sau da dama idan zai yi tunaninta yana tunaninta ne a ranar da ya ɗagata tana jaririya ko cibiya ba'a yanke mata ba, ya ɗauketa ya kudunduneta a cikin rigar da ya cire daga jikinsa, tana ta tsallar ihu da wannan red lips ɗin nata suna ta kerma saboda sanyi, tun da lokacin ta dasu mashi a cikin zuciyarsa wanda cireta kuma ba abu ne mai yiwuwa ba, sai dai idan za'a haɗa da zuciyar tasa dukka a cire. To fah, babbar magana kenan, akwai cakwakiya ba kaɗan ba.

"Sweetie ba zan jima ba zan dawo kin ji? Kada ku damu".

Da okey kawai ta amsa mashi, amma daga jin yadda ta amsa kai kasan rai bai so ba, kawai ta amsa ne dan bata son ja in ja da shi.

Ita kuwa Pretty tuni idanunta sun ciko da kwallah, tasan cewa idan ya je zai É—an jima kafin ya dawo, idan kuma ya dawo ba zai wani jima a wajen nasu ba zai ce masu zai koma, shikenan yau ba zasu jima a tare da shi ba, zai tafi ya barsu da kewa, in ya tafi kuma sai yamma zai dawo, wannan dalilin yasa duk ta ji babu daÉ—i.

Kawar da kansa ya yi tare da ficewa da sauri, dan baya son ganin kukanta, kuma shi gaskiya yana son sanin hanya cikin ƙanƙanin lokaci, dan a gaskiya ya gaji, yana son ganin duniya ya take.

Zuciyarsa sai yi mashi kuna take yi, amma a haka ya sa kai ya wuce hannunsa rike da ayabar da ta bashi.

Ita kuwa Pretty goge hawayen face ɗin nata ta yi tare da ture kayan cimar da suke a gabanta gefe guda, sannan ta miƙe ta koma kusa da ƴar uwarta tana faɗin. "Sweetie sam sam i don't want Kamran to go anywhere ya bar mu, am not happy at all, and am feeling very very bad mood idan baya nan". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya ta tada kai da laps na Sweetien.

"Same here Pretty, ina jin kuna a cikin rai'na idan zai tafi".

Shiru ta É—an yi kafin ta ce. "But Sweetie why not mu fara neman mum da kanmu? Maybe fa tana a cikin Forest É—in nan kusa da mu".

"E kince wani abu, let Kamran come back sai mu gaya mashi, zai tayamu nemanta, maybe tana nan wani abin ne ya riƙeta, kinga idan muka ganta zata rage mana kewa, idan Kamran ya zo tafiya ba zamu damu sosai ba".

Allah sarki bayin Allah, ai ko dan kasancewarsu su kaɗai a cikin wannan ramin ma dole su rinƙa kuka idan Kamran zai tafi ya barsu, abin akwai taɓa zuciya, babu uwa babu uba, babu wani ɗan uwa, babu motsin halittar ɗan adam sai dai na dabbobi su tsuntsaye da sauransu, babu gida gaba babu gida baya, su biyun nan suke rayuwarsu kafin Allah ya kawo masu Kamran, gwanin ban tausayi sosai, dole ma su sha kuka a duk lokacin da zai tafi wajen Mammarsa, Allah sarki.

Cigaba da hira suka rinƙa yi suna neman mafita a tsakaninsu, da haka har barci ya ɗauke Pretty, ya rage Sweetie kawai da ta kasa yin barcin, tunanin mafita ta shiga yi tana ɗan shafa kyakkyawar gashin kan Prettyn wadda yake a saman laps ɗinta, tana matuƙar kaunar ƴar uwar tata, ita ma Prettyn tana matuƙar kaunarta, su biyun nan su ne duniyar juna, ita ce duniyar Pretty, Prettyn ma Sweetien ne duniyarta, komai nata, so suna tsananin kaunar juna.

Kamran kuwa tafiya ya yi wajen wannan teku na jiya dan ya duba ko akwai wata hanya mafi kusa ta gefe gefen tekun.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

After some days.

A cikin waÉ—an nan kwanaki da suka shuÉ—e dai maman Zainab ta yi nasarar samun sa'a wannan asiri na jikin Zainab dai ya karye, ta tsaya ne tsayin daka wajen ganin ta yi wannan haÉ—in maganin da mamanta ta gaya mata, so Allah da ikonsa Zainab ta dawo normal. Sai dai kuma wani tashin hankali shi ne tun ranar da baban Zainab ya fita gidan a tare da Hauwa bai sake dawowa gidan ba, su maman Haidar sai nemansa suke yi, amma ina basu gansa ba, sosai maman Zainab ta shiga damuwa maras misaltawa, ta yi mummunar rama sosai da sosai, kamar ba ita ba, har duhun wahala da damuwa sai da ta yi, sun dawo yin rayuwa daga ita sai su Zainab da Sadiq, Haidar ma yanzu sai gefi gefi yake shigowa gidan, watarana a gidan kakarsa yake kwana.

Ga wani bala'i da hajiyarsu ta taso masu da shi shi ne wai auren Khadija and Haidar za'a yi shi kafin ta rubuta Exams É—in, sun fasa bari sai ta rubuta, saboda Haidar ya matsa masu sosai, shi fa sam bai damu da rashin sanin in da babanta yake bama, bai wani damu da halin da suke ciki ba, ko a jikinsa, abin da yake gabansa kawai yake yi.

Maman Zainab ji take yi kamar ta kwashi Æ´aÆ´anta su koma wajen mahaifiyarta, Sadiq kuwa ya ce mata a'a ta yi fito na fito da su ta gaya masu Khadija bata son Haidar, dan haka ba za'ayi wannan auren ba, idan sun ki sun ce sai anyi aure to ta shigar da su kara ga hukuma a kwantar ma yarinya hakkinta, tun da yanzu baban Zainab ma ba ta su yake yi ba, dan haka ta tsaya ta kwatarwa Æ´arta yanci.

Ta É—auki kwanaki tana tunani a kan zance Sadiq É—in, daga karshe dai ta kira mamarta a waya ta sanar da ita ga wani lukutar masifa da suke ciki, sannan ga shawarar da Sadiq ya bata.

Da yake mahaifiyar tata dattijuwan arziki ce sai ta ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi ki rinƙa kallon Mamarsa tamkar ni ce, ki girmamata kada damuwa ko ɓacin rai or zuciya haɗe da shaiɗan ya ja ki ki yi mata wani abin da ba zaki iya yi mun ba, kada ki manta zamanku da ɗanta a baya, na baki izini ki kwatarwa ƴaƴanki yanci, amma kada ki wuce gona da iri, uwa bata fi uwa ba, mahaifiya dai mahaifiya ce, kada ki riƙi hujjar cewa hankalinsa baya a kanki ki ce zaki walaƙanta mahaifiyarsa, ki sani in shi baya nan Allah yana nan, kada ki yi wannan kuskuren, komai zaki yi ya kasance tsakaninki da Allah zaki yi, baki san me gobe zata haifar ba, Allah ya kyauta ya saita maki al'amuranki, ki cigaba da yin addu'a tare da yin azzumi komai ya kusa warwarewa In Sha Allah".

Sosai Ouumar tata ta yi mata nasiha mai ratsa jiki, daga karshe suka yi sallama. Tana ajiye wayar ta É—aura É—amarar rusa wannan aure ta Haidar da Khadija koma ta yaya ne.
Chapter 145 · 0% Book details