← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 180

Sashe 116

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan muka koma muka yi duba da abin da yake a tsakaninta da su maman Haidar nan ma ita ta jawa kanta, domin kuwa ita ce nan tun farko ta sakewa Haidar ya san komai ɗinta da har yake kwasan sirrin gidan yana kaiwa kakarsa da kuma mahaifiyar tasa. Kunga ita ma maman Haidar ɗin ba samun jin daɗin nan wajen mijinta take yi ba, baban Zainab ɗin ne ma mai ciyar da ita, saboda mutuwar zuciya irin na mijinta, ai dole ita ma zata ji haushin bata samun abin da maman Zainab take samu, dole ta yi mata hasada da bakin ciki, shiyasa take zuga kakan su Khadijah dan kawai ta takurawa maman Zainab ɗin kuma ta ƙuntata mata. Yaushe zaki bari har familynsa su san irin kyautatawar da yake yi maki? Ai a irin haka ne ma wata daga cikin family zata maƙale ta ce idan ba shi ba ba zata yi aure ba, haka kina ji kina gani za'a sanya ya aurota kamar dai yadda kuka ga aya a kan maman Zainab. Ai ko mijinki ya ɗauko kaninsa ya kawo maki ki rike, sai ki san ta yadda zaki zauna da shi baki cuce shi ba kuma baki bari ya cuceki ba, kada ki yarda ki bari yasan cewa ga abin da yayansa yake yi maki, ki koyawa mijinki ko abu zai baki to ya baki tun daga cikin bedroom ba sai anzo parlourn bama bare har a kai ga tsakar gida. Fatana dai my people's kun ɗauki darasi na farko a kan maman Zainab?.

Sosai baban Zainab ya rarrashi Hauwa, sai kukan makirci da kisisina take yi, ita kuma maman Zainab tana can tana ƙoƙarin haɗiyar zuciya kofa yaki buɗewa. Tana ji tana gani baban Zainab dai ya saka Hauwa a gaba suka bar gidan, sai lallaɓata yake yi. Dama kun san shi ya iya sosai..........😅

Suna fita gidan Haidar kuma ya fito daga cikin nasu É—akin, dukar kofar parlourn da maman Zee ke yi ne yasa ya farka, sai dai bai yi nasarar ganin menene ya faru ba, baban Zee ya ja Hauwa sun yi gaba. Ko da ya fito waje bai ga kowa a harabar gidan ba, ita ma Maman Zee a lokacin ta dai'na buga kofar parlourn ta kwasa a guje ta nufi cikin bedroom É—inta, dan taga tafiyarsu ta window, sun riga sun fita, ko ta buga kofar ba amfani, dan haka sai ta kwasa da gudu ta yi cikin room É—inta.

Jikinta har wani irin kerma yake yi saboda bakin ciki, wani irin zufar wahala yana tsastsafo mata a gabaÉ—aya face É—inta, kuka take yi hawaye bibbiyu, idanunta sun yi jajir kamar wata Æ´ar shaye shaye. A gigice ta É—auko wayarta, har wani yana yana take gani a cikin idanunta, bata ganin screen É—in wayar da kyau saboda kuka.

Number mahaifiyarta ta fara kira a haukace, sai yanzu ta tuna da cewa ta kira mahaifiyar tata, da can duk bata tuna ba, sai da abu ya kwaɓe mata.

Bugu biyu mamar tata ta É—auka. Cikin kuka ta fara faÉ—in. "Nashiga uku mama, na mutu na lalace Hauwa ta cuceni".

A gigice Æ´ar tsohuwa ta ce. "A'isha lafiyarki kuwa? Babu sallama sai ihu haka? Menene yake faruwa? Me Hauwa É—in ta yi maki?". Da gaji maganar tsohuwar nan kasa ta firgice, baiwar Allah maman Zee ta É—aga mata hankali babu shiri.

"Mama Hauwa ta cuceni, ta kaini wajen boka, da kai'na kuma tasa na bawa baban Zainab maganin da zai sota, da kuɗina kuma muka karɓo maganin, yanzu shikenan sonta yake, ga shi can ya ɗauketa sun tafi, na shiga ukuna, mama ki taimakeni kada na mutu". Yadda take maganar zaka fahimci cewa tabbas ba'a cikin hayyacinta take ba, bata ma san me bakinta yake faɗa ba, kawai sambatun surutai barkate take yi.

Ƙara rikicewa ƴar tsohuwar nan ta yi, sai cewa take yi. "A'isha ki nutsuwa ki yi mun magana a nutse ta yadda zan fahimta, yanzu ni bana iya gane komai da kike faɗe". Ita ma tana magana tana haɗe words, saboda a rikice take, kun san irin wannan call ɗin ma sai mai dakiyar zuciya yake iya jurewa baya suma, amma a kiraka irin haka ana kuka ga shi ba gari ɗaya kuke ba, baka san halin da ake ciki ba kuma baka san kan zance ba, in fact bata ma taɓa kiranka ta ce maka tana cikin wata damuwa ba, rana tsaka kawai ayi maka irin wannan kira ai dole bawa ya rikice, idan akwai abin da ya fi rikicewa ma yi zai yi.

Sai sambatu maman Zee take yi ta kasa iya nutsuwa, a haka dai ta kwashe duk abin da ya faru tun daga farko kan auren Khadija da Haidar har izuwa yau ta gayawa mamar tata, tana yi tana kuka hawaye bibbiyu.

Cikin tsananin tashin hankali mamar tata ta ce. "A'isha kin tabka baban kuskure da gyara shi zai yi matukar wahala a yanzu, da hankali da tunaninki har wata zata kaiki wajen wani boka? Shin bana duniyar ne da ba zaki kirani ki sanar da ni ga abin da yake faruwa ba? Ga halin da gidanki yake a ciki? Tun farko ma ban hana ki yin shawara da wata ba? Tun kuna yara na yi na yi na rabaki da Hauwar nan, amma kika ki rabuwa da ita, yanzu ba ga shi ta kai ki ta baroki ba, to ita ina ma mijinta yake? Da auren nata ta biyo baban Zainab ɗin kenan ne ko yaya?". Ta yi maganar cikin maƙurar ɓacin rai!.

"Mama bansani ba, ban san ina aurenta yake ba, ni dai kawai nasan dai tana da miji da yara, ni ba zuwa gidanta nake yi ba, nafi wata 8 ban leƙa gidanta da ƙafafuna ba, mama nashiga ukuna".

A ɗan fusace mamar ta ce mata. "Ai baki shiga uku bama tukun nan A'isha, ba dai shirka haɗa Allah da wani kika yi ba, laifi mafi girma a duniya, ai kin rinƙa shiga masifu kala kala kenan Allah ya kiyaye ba baki nake yi maki ba, amma wlh kin tabka baban kuskure, kuma abin da zan gaya maki a nan yanzu shi ne tun wuri ki fara istigifari kafin abin ya yi nisa ki fara fuskantar fushin Ubangiji, kin taɓa ganina da ko da sassaken itace na jiƙa na sha ne da zaki kama hanyar zuwa wajen boka? Wato duk nasihar da nake yi maki kullum abanza yake ko? Kishi haukace? To tun wuri ki yi gaggawar tuba, ki nutsu ki koma ga Allah, hankalinki ya dawo jikinki kafin mu san abin yi". Ta kai karshen maganar ranta a matuƙar ɓace sosai.

Kuka ne da ya ci karfinta yasa ta ƙasa iya amsa maganar maman, danasani ne kawai a cike a cikin ranta, nadamar sanin Hauwa a rayuwarta ne kawai ya cika mata zuciya. Sam bata san lokacin da mahaifiyar tata ta karaci yin faɗarta ta katse kiran ba. Ita dai ta luluƙa duniyar tunani mafita, a wajen ta sulale ƙasa ta kwanta tana mai cigaba da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Shi kuwa Haidar dama can kun san ba shiri da ita yake yi ba, dan haka ko da ya ji kukanta ma tsaki ya ja ya koma cikin É—aki abinsa, ya je ya haye gado ya cigaba da yin barcinsa, dama lokacin tashinsa bata yi ba, kawai sun tashesa ne.

Baban Zainab kuwa da yake ba yin kansa bane, abin hawa ya tara masu shi da Hauwa suka nufi gidanta, da alama ya manta da cewa tana da aure.... Tirƙashi, akwai cakwakiya kam ba kaɗan ba wlh.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🌼DUBAI🌼

Ɗaki mai matuƙar kyau aka kai Leesharh, tamkar ba ɗakin ƴar aiki ba, ya ji komai na more rayuwa, ga bed ɗinta ma katafare da shi, yana shinfiɗe da shinfiɗa ta alfarma, ita kaɗai ce a room ɗin, ba'a haɗata da kowa ba, ta ji matuƙar daɗin kasancewar ita kaɗai ga kuma room ɗin ya ji komai, ga wani haɗaɗɗen sanyin Ac dake ratsa jiki gwanin daɗi.

Ai tana shiga cikin room ɗin bayan Radia da Fadila sun fita, saman gadonta ta kwanta tana mai da numfashi, sai yanzu ta samu damar sauke nannauyar ajiyar zuciya, godiya ta yi wa Allah da ya kawota cikin irin wannan daula, addu'a kawai take yi da Allah ya bata nasara ta kammala aikinta cikin ƙanƙanin lokaci ta koma wajen babanta. Nan take kuma face ɗinta ya canza, tunawa da ta yi da irin aikin da ya kawota, duk sai ta ji ta shiga gagarumin damuwa, yanzu da gaske haka zata yi wannan aiki na leƙan asiri Ramish? Tukun nan ma waye shi? A ina kuma yake? Shi ma a wannan part ɗin yake ko yaya?.

Jin motsin an shigo mata cikin room É—in nata ne yasa ta yi saurin kai kallonta zuwa bakin kofar shigowa. Fadila ce ta dawo É—auke da akwatinta, ta je ta É—auko mata ne.

Sannu da hutawa ta yi mata kafin ta ce mata ga akwatinki nan. Nagode Leesharh ta yi mata tare da binta da kallo, daga haka basu sake ce da juna ko sannu ba har ta ajiye mata akwatin ta fita waje.

Barci mai shegen daÉ—i ne ya É—auki Leesharh, ba ita ta farka ba sai wurare karfe 1 na rana, kasancewar yanayin gidan baka iya gane rana ko dare ya yi sai dai ka duba time, sai ya zamana bata iya gane cewa wani lokaci bane a yanzu.

Miƙewa ta yi cikin kasala irin na mai barci ta nufi cikin toilet. Haɗaɗɗene toilet ɗin nata, ita a nata ganin sai take ga kamar wannan room ɗin ai dai'dai yake dana ƴar gida, saboda ta ga ya haɗu ne sosai, da alama ta mance a gidan waye take da har take ƙoƙarin haɗa room ɗinta dana ƴar gida, tab bata san duk wannan haɗuwa na room ɗin nata su shi suke kallo a matsayin na masu aiki ba, kila idan ta shiga bedroom na ƴar gida sumar tsaye zata yi dan haɗuwa.
Chapter 116 · 0% Book details