Sashe 114
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai musa mata ba ya jata da hira har wuraren karfe 10, sannan ne ya ce ta tashi ta shiga ciki. Ba musu ta miƙe ranta a sake, fuska ba yabo ba fallasa ta wuce ciki tana yi mashi zai da safe. Shi ma sai da safe ya yi mata kafin ya miƙe ya koma cikin room ɗinsu a in da ya sami Haidar yana riƙe da wayarsa yana kallo, ko shakka bayayi fina finan batsa yake kallo duba da yadda ya takure jikinsa waje guda, kuma yasha kamasa yana kallon fina finan batsa dama, sau da dama yasha yi mashi nasiha a kan hakan babu kyau ya daina, amma ina ya yi nisa baya jin kira, hasalima idan bai kalli batsan ya samarwa da kansa nutsuwar hankalinsa da ya ɗaga ba baya iya yin barci, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake son taɓa jikin Khadija sosai, shi bai kima ta dawo kwana a ɗakinsu ba, ɗan iska saboda yana kalle kalle batsa kullum yana cikin ɗagawa kansa hankali, dole ya yi ta ƙoƙarin latsa ƴar mutane. A kullum idan Sadiq ya fara yi mashi nasiha a kan ya dai'na kallon film irin haka, to wlh faɗa ne yake biyowa baya, basu wanyewa lafiya, hakan yasa Sadiq ɗin yanzu bai ci bi ta kansa ba, ya sharesa kawai tun da baya ji kuma ai ba yaro bane shi, ya fi Sadiq ɗin shekaru da shekaru biyu, kamata ya yi ace shi yake yi wa su Sadiq ɗin faɗa da nasiha, amma ina, ina ma yaga hankali ne wannan kam, sai dai Allah ya kyauta.
Yanzu ma girgiza kai kawai Sadiq É—in ya yi tare da nufar nasa gadon, already da alwalar barcinsa a tattare da shi, dan har ma ya kwanta mamarsa ta kirasa ya tashi ya fita, so yanzu yana dawowa addu'ar barci kawai ya yi tare da kashe wayarsa ya kwanta, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
A ɓangaren Khadija ita ma bayan ta yi sallar nafila raka'a biyu kamar yadda kawun nata ya ce, sannan ta rufe da shafai da witiri, hankalinta ya kara kwanciya sosai, ta ƙara samun nutsuwa sosai da sosai in da ta zo ta haye gadon ta kwanta, cikin ƙanƙanin lokaci barci ya ɗauketa, dama ita Zee already ta yi barci abinta.
Mamarsu kuwa, cikin kuka ta sanar da Aunty Hauwa halin da ake ciki. Hakuri Aunty Hauwar ta bata tare kuma da ce mata ta kwantar da hankalinta gobe da safe zata zo gidan, kada ta ji ta wani damu zasu yi maganin baban Zainab. Da haka dai ta rinƙa rarrashinta har ta hakura a nan barci ya yi awon gaba da ita, in takaice maku labari dai bata yi sallar mangariba bare isha, a haka barci ya saceta saboda kukan da ta sha.
(A gaskiya ina jin labarin gidansu Khadija tamkar true life story, wato tamkar gaskiya, wlh duk idan na zo rubuta part ɗin ji nake yi kamar gaske, saboda abu ne da yake faruwa yau da gobe a zahiriya sosai da sosai, Allah dai ka ƙara tsaremana imaninmu ka rabamu da ƙawaye jahilai.)
Washegari da safe kamar yadda suka saba haka Maman Zainab ta tashi tare da biyan bashin sallolin da suke a kanta na tun jiya, sannan ta nufi kitchen da nufin ta yi masu girki, kasancewar farar shinkafa da miya ta dafa masu daren jiya wadda basu ci ba, sai ta É—auko shi ta sake É—umama masu, saboda bai yi komai ba, kuma yana da yawan da bai kamata su zubar ba, so sai ta sake mayar da shi wuta ta É—umama, shi ta sanyawa su Khadija a kulolin makarantarsu.
Suma su Khadijah suka yi wanka suka shirya kamar yadda suka saba, baban su ne kawai yaki fitowa, da yake dama sai maman Zainab ta haÉ—a mashi ruwan wanka sannan take tashinsa daga barci, to jiya dai ya rufe room door É—insa da key, koda ta kammala shirya masu komai kamar yadda ta saba ta nufi room É—in nasa dan ta tashesa, sai ta ji kofar a rufe da key.
Kamar zata yi knocking, sai kuma ta hakura ganin cewa su Khadija suna nan, kuma tasan halinsa tun suna saurayi da budurwa, damone sarkin hakuri over, amma kuma idan ya zuciya wlh abin da zai sanya shi ya sauko ba karamar abu bace, kuma duk yadda yakai ga kawar da kai ga abu idan fa ya zuciya tura ta kai bango to fa mantawa yake yi da wata kawaici ko makamancin haka, yanzu haka a yadda yake cikin fushi sosai É—in nan yana iya yi mata faÉ—a tatas sosai koda a gaban su Khadijah É—in ne, zai manta da wani tarbiya.
Tuna hakan yasa ta fasa yin knocking na kofar ta juya izuwa nata room ɗin, bata sake bi ta kan su Khadijah ɗin bama ita ma. Bayin Allah da suka ga lokaci na ƙurewa zasu yi latti ga Khadijah suna dab da fara rubuta Exams, sai suka fito suka nufi wajen kawunsu Sadiq, dan ya kai su school kamar yadda ya saba, yau dai sun hakura da yin sallama da baban nasu tun da bai fito ba.
Knocking suka yi masu Sadiq a kofar É—akin, ba'afi second ashirin ba sai ga Sadiq É—in nan ya buÉ—e kofar ya fito. Shirye yake cikin dakakkiyar shaddar mai shegiyar kyau, da alama yau ma yana da class.
Har suna haɗa baki wajen cewa Uncle Sadiq ina kwana. Murmushi ya yi yana kallon Zainab sarkin tsiwa kafin ya amsa masu gaisuwar, yarinyar nan Zainab ba dai iyayi ba, haka take zama ta karewa maman Haidar da kakansu zagi fes kamar an aikota, bata da sauki, Khadija kam daga e sai a'a, sai kuma gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa.
"Dama na shirya ku nake jira, ina da class karfe 7:30 dai'dai mu je ko?". Sadiq ya faÉ—a yana kai hannunsa ya É—an bugi bakin Zee da take aikin turo shi kamar wadda aka zaga.
"Kai kawu Sadiq menayi maka to?". Ta faÉ—a tana É—aure fuska.
Khadijah ce ta amsa mata da. "KwaÉ—ayin duka yake ji yasa ya dake ki, ko dai bai kai bane?".
Wani irin harara ta bi Khadija da shi. Shi dai Sadiq wucewa ya yi izuwa wajen mashin ɗin baban nasu, da yake key na a hannunsa, fito da mashin ɗin ya yi kamar yadda suka saba, ba ɓata lokaci ya ce su yi sauri su hau su tafi lokaci yana ƙurewa. Da sauri suka hau Zainab sai raki take yi. Da haka suka bar gida, shi kuwa Haidar yana can yana barcin asara, wani lokaci ma sai 10 yake tashi ya tafi kasuwa ko kuma wajen mamarsa or kakarsa, kullum aiki ɗaya, ya kusa yin aurema bai canza hali ba, ko waye zai ciyar mashi da matar idan ya yi auren? Shi da kasuwar ma sai yaga dama yake zuwa. Akwai matsala sosai, akwai case ba kaɗan ba.
Misalin karfe 9 dai'dai sai ga Aunty Hauwa ta nufo gidan kamar yadda ta faɗawa maman Zainab zata zo jiya. A lokacin baban Zainab bai fita ba, yana ciki, da alama yau ba zai je kasuwa da wuri ba, ita ma maman Zainab tana cikin ɗakinta ta yi zaman ƴan bori a saman tsakiyar gado, ta haɗa hannayenta ta buga uwar tagumi kamar wadda aka aikowa da wahayin yinsa, ta luluƙa duniyar tunanin ya zata yi da rayuwarta, har yanzu ta kasa iya gane cewa damar da Allah ya bata a baya ne take wasa da shi son ranta, tana yi kuma ba tare da godiya ga Allah ba, to yanzu damar tana neman kubce mata, ta kasa iya gane hakan ma bare ta yi ƙoƙarin dawo da damar izuwa gareta..... Tirƙashi, akwai matsala fa my people's, mu je dai zuwa.
A parlourn Aunty Hauwa ta zauna, ta tsantsara kwalliyarta cikin wata shegiyar lace mai kyan gaske, da alama ma case ɗin maman Zainab ɗin bai wani dameta ba, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya a kanta irin yau ba mutuncin nan, sai wani kwaɓe fuska take yi kamar wadda taga kashi.
Fitowa maman Zainab ta yi daga room ɗinta cike da damuwar halin da take a ciki, tsawon shekarun nan da suka yi aure baban Zainab bai taɓa yi mata makamancin haka ba, har ya share tun jiya bai yi mata magana ba har yau, abin dole ya jefata cikin damuwa sosai, a maimakon ta kira mahaifiyarta ta sanar da ita abin da yake faruwa, sai ta sake kirawo Aunty Hauwa kuma.
"Hauwa ki zo mu shiga cikin bedroom, baban Zainab yana nan fa". Maman Zainab ta faɗa murya ƙasa ƙasa.
Okey Aunty Hauwa ta amsa tare da ɗaukar wata ƴar figaggiyar jakarta irin na dillalai, ga gyalenta dama a kafaɗa ta yafo shi kamar ba matar aure ba, burinta kawai su shiga ciki ta tambayi maman Zainab ɗin baban Zainab ya sha maganin? A ƙage take da ta ji ya sha ɗin ko bai sha ba?.
A haka ta miƙe da nufin su shiga cikin bedroom ɗin dan rashin hankali irin na maman Zainab da kuma damuwa da ya rufe mata idanu.
Tana miƙewa tsaye sai ga baban Zainab ya fito cikin shirinsa na shadda mai shegen kyau launin sky blue, ɗinkin manyan kaya ne, so ya ɗaura babbar rigar ma a sama, a takaice dai makurar shigar mutunci ya yi, da alama yau ma ba zai ci abincin maman Zainab ba, kamar dai daren jiya, dan dai ga shi ya kammala shirin fita abinsa.
"Sannu da fitowa, ina kwana?". Aunty Hauwa ta faÉ—a cikin sanyin murya.
Turus ya ja birki ya tsaya tare da juyo da kallonsa a kanta, wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya sauke idanunsa a kanta. Da ni da ku duka mun san cewa baban Zainab in ya shigo ya sami maman Zainab da bakuwa wlh ko kallon in da suke baya yi, baƙin suna gaishesa ma baya tsayawa, wani lokaci kafin ya amsa masu gaisuwar nasu ma ya kai bakin kofar ɗakinsa, amma yau sai ya tsaya tare da juyowa yana kallon Aunty Hauwa.
Maman Zainab ta É—an yi mamaki, amma sai ta ce kila zai tambayi Aunty Hauwa É—in ina ta je jiya ne, dan haka sai bata wani damu ba.