← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 180

Sashe 143

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin zolaya ya ce mata. "Jannat menen a wajen kafafunki kamar kamar snaka? Kamar fa É—an snake É—in dake cikin glass É—in ne ya fito......."

Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata saboda wani irin ihu da ta zunduma, a guje ta bar wajen tana ƙoƙarin cire alkyabbar jikinta kamar ance mata a jikin alkyabbar macijin yake, kunsan irin wannan abin sai ka ji kamar da gaske yana taɓa maka jiki, musamman ma idan tun farko kaga macijan da idon ka, to wlh ko baa tsoratar da kai ba sai ka rinƙa jin kamar suna taɓaka, to ita ma haka ta ji, sai ta ji kamar da gaske yaron macijin ne yake taɓa mata kafa, ai kuwa ta rinƙa tsalle tana kakkaɓe kayan jikinta tana ƙoƙarin cire kayan ma gabaɗaya, sai ihu take yi.

Cikin sauri ya bi bayanta, da gudu ita ma auta ta bar wajen, dan ma kada su kamata.

Yana zuwa in da take ya riko wuyar alkyabbar tata dan ya hanata cirewa. Ƙanƙame shi ta yi tana faɗin. "Na shiga uku, Yah Jawad dan Allah ka cire mun shi, wlh na ji yana taɓa mun kafa".

Dariya kamar zata kashe shi, yau ba karya ya yi nishaÉ—i over to over, bare ma idan ta zaro ido tana faÉ—in. Ya yi sauri ya cire mata ta ji yana haura mata saman kafafu wajen cinyarta, innalillahi Jawad kamar zai mutu da dariya, bayan rike wuyar alkyabbarta da ya yi dan kada ta cire, ya kasa iya aikata komai, saboda dariyar da yake dannewa ta hana shi ko da É—aga hannunsa bare ya yi rarrashi.

Ma'aikatan da suke wajen ne suka yi saurin ƙarisowa in da suke domin su ji ko lafiya. Hannu kawai ya ɗaga masu alamar su tafi babu komai. Cikin kuka ta ce. "Kada ku tafi, ku zo ku cire mun macijin nan kada ya kasheni, Wayyo mummyna, Yah Jawad ka mayar dani gida, ni ba zan sake fitowa ba, na shiga uku daddy yau zan mutu, idan ya cije ni shikenan na mutu".

Ai a wannan gaɓar dariyar ba zata dannu ba, ta ci karfinsa a in da ya fara tikar dariya kamar wani zararre. Ita kam auta ta rigada ta gane ba wani maciji da gangan ya yi wa Aunty Chuchunta haka, dan haka sai ta sanya hakan ma a cikin lissafin abin da zata gayawa Chuchu idan suka koma gida, zata gaya mata cewa da gangan ya yi mata hakan.

Ganin yana tikar dariya har da tsugunnawa a ƙasa yasa ita ma Chuchun ta ɗan tsagaita kukanta tana binsa da kallon mamaki.

Da kyar ya iya tsayar da videon da yake É—aukarsu tun farko, har murÉ—a mashi cikinsa ta yi saboda dariya.

Jin ta ɗan tsagaita kukan ne yasa shi ma ya yi ƙoƙarin ya danne dariyar tare da miƙewa tsaye. Ɗan rungumota ya yi yana faɗin. "Ai tun ɗazun snake ɗin ya sauka daga kafafunki, ya koma wajen ƴan uwansa, kece baki gani ba". Yana magana yana guntse dariya.

Duba kafafunta ta fara yi da sauri tana mai cigaba da kuka. Rarrashinta ya hauyi yana yi mata sorry. Ita dai auta ta harÉ—e hannaye a kirji tana ganin ikon god.

"Sorry my sister, yanzu mu je muga su zaki dasu zamisa sai mu koma gida ko?".

Ai a É—ari ta ce mashi. "Ni Yah Jawad ka mayar da mu gida kawai babu in da zan sake zuwa".

ÆŠan kara rungumeta ya yi yana É—an bubbuga bayanta alamar rarrashi. Sai a lokacin kuma ya haÉ—a ido da auta da ta harÉ—e hannaye a kirji tana ganinsu. Ido É—aya ya kashe mata tare da É—aga gera guda, irin alamar Malama ya ne?.

Dariya ta É—an yi mara sauti kafin kuma ta É—an kawar da kanta tana faÉ—in. "Yah Jawad gida zaka mayar damu daga nan, mun yafe sauran wajen yawon".

Alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba mutu ta ƙariso wajen nasa da sari, haɗata ya yi da chuchun dukka ya rungume yana kara rarrashin chuchu, sai ajiyar zuciya take saukewa, ta sha zunduma ihu kam.

Sun dan É—auki a kallah minti goma a haka kafin ya rabasu da jikinsa ya ce su wuce gidan tun da sun ce yawon ya ishesu.

Chuchu ce a gaba, ta yi sauri ta wuce zuwa wajen motarsu, taki ɗagowa ta sake kallon komai a wajen, wai dan ma kada wani abin ya sake bata tsoro. Sai murmushi kaɗan kaɗan yake yi ya riƙo hannun auta suka rufa mata baya.

Har suka shiga cikin mota bata dai'na sauke ajiyar zuciya ba, a haka ya tada motar suka nufi gida, sai janta da hira auta take yi, amma bata wani kulata ba, saboda hankalinta ya yi gida, so take ta koma ta cire kayan jikin nan nata, ta yi alkawarin ba zata sake saka kayan ba, zata bawa kuyangarta dake gyara mata ɗaki kyauta, dan ita tun da maciji ya taɓa kayan bata so kuma.

Suna isa gida ba ɓata lokaci ta fice daga cikin motar, Jawad ya yi mamakin ganin irin saurin da take yi, ko sallama basu yi ba, bai san tana son zuwa ta cire kayan jikin nata bane. A hanzarce auta ta rufa mata baya bayan ta yi mashi sallama, har lokacin wayar momma yana hannun autar, ta haɗa kuma da wayar da Yah Jawad ya bawa Chuchun ɗazun, domin Chuchun ta bata ajiyar wayar tun da suka fita, so sai ta haɗa da wayar ta nufi cikin gida, shi kuma bai lura da ta tafin mashi da waya ba, kawai ya fito ya nufi nasa part ɗin yana ɗan murmushi.

Ita kuwa auta sai sauri take yi dan ta je ta gayawa Chuchun cewa da gangan yah Jawad ya yi mata duk abin da ya yi mata É—in nan.

A ɓangaren su Kamran kuwa, wato Forest.

Washegari da safe kamar yadda ya saba zuwa wajensu haka ya nufo in da suke bayan ya kammala yi wa mama dik abin da ya saba yi mata. Yana tafiya yana tunanin yadda zai yi ya fita wajen dajin nan da kuma yadda zai yi da mama ta barsa ya fita ɗin, ba zai iya tafiya bai tambayeta ba, domin yasan zata shiga tashin hankali na wuce misali, yana kaunarta over, amma kuma ya kasa iya gaya mata, domin yana tsoron kada hakan ya ja mashi rabuwa da su Pretty, ta hana shi zuwa in da suke ma kwata kwata, ƙaramin aikinta ne ta hana shi fita ma kwata kwata idan ta ji yana da burin barin wannan dajin.

A kan hanyarsa na zuwa wajensu ya cikaro da Rocky, bai wani kula shi ba ya cigaba da tafiyarsa kawai, rufa mashi baya Rockyn ya yi suka jera kamar yadda suka saba, sai wani miƙa yake yi da alama ya ci nama ya ƙoshi ne ya yi barci ya tashi.

Dajin gabaÉ—aya akwai danshi danshin ruwa, saboda ruwan saman da aka yi jiya, da wasu ganyayyakin itace suna zubar da ruwa, wasu ramukan sun cika da ruwa, idan suka zo wucewa sai Rockyn ga tsallaka Kamran yake bin bayansa, haka suka cigaba da tafiya har izuwa wajensu Pretty.

A waje Rocky ya kwanta, already kunsan baya iya shiga ciki, kofar ta yi mashi ƙarami. Ciki shi kuma Kamran ya shige, ga mamakinsa sai ya tarar basu a ciki dukkansu. Zaro idanu sosai waje ya yi yana tunanin to ina kuma suka tafi? Yasan dai Sweetie ita bata fita, koda Pretty ta ce tazo suje waje, in dai ba da shi bane bata yarda ta je, kullum tana cikin abinta, to ina suka je yau kuma?. Ya jefawa kansa tambaya.

Ganin babu mai bashi amsa ne yasa ya yi saurin juyawa cikin zafin nama ya nufi wajen. Rocky na kwance kamar yadda ya barshi. Bai bi ta kansa ba ya nufi wajen ƙoramar nan, dan ya duba su. Da sauri Rocky ya miƙe ya rufa mashi baya.

Tun daga nesa yake baza idanu ko zai gansu, amma kuma bai ga alamar su a kusa ba, hakan yasa ya yi saurin ƙarisawa wajen, dayawan lokuta tun daga nesa yake hango Pretty a saman durse tana wasa da ruwa, to yau dai bai ganta a wajen ruwan ba.

Har yana haɗawa da gudu ya ƙarisa wajen. Zaune suke a ƙarƙashin bishiya, Sweetie tana magana ita kuma Pretty ta buga uban tagumi tana kallon ruwan dake gudu a ƙasar ƙoramar.

A hankali Kamran ɗin ya lallaɓo kamar wani ɓarawo, ya ce da Rocky ya tsaya yana zuwa, da yake sun saba sai Rockyn ya tsaya, sanɗo ya fara yi kamar mai son yin wani abin, da yake Pretty ta bawa hanyar da yake zuwa baya sai bata gansa ba, ita kuma Sweetie dake fuskantar hanyar bata gani, so basu san da zuwansa ba.

SanÉ—o ya cigaba da yi har ya iso kusa da Pretty, dama tana zaune ne a saman jijiyar bishiyar, irin bishiyoyin nan ne masu jijiya manya manya kamar jikin wani bishiyar, to a saman jijiyoyin suka zauna daga ita har Sweetien.

Yana ƙarisowa wajen cikin dabara ya sanya hannunsa ya capke kan black snake dake ƙarƙashin jijiyar bishiyar ta bayan Pretty ta kuma gaban Sweetie kenan, yanayin yadda suka zauna kamar suna fuskantar juna ne, Pretty tana fuskantar ruwa, ita kuma Sweetie tana fuskantar hanyar dake bayan Prettyn, so Pretty ta bawa macijin baya shiyasa bata gansa ba, ita kuma Sweetie bata gani ma bare ta ganshi, ga shi kuma a gabanta, sai dai bai yi yunƙurin cizonsu ba, yana kwance ne shiru shi ma macijin, da alama ma kamar bai ji motsinsu ba, kuma dai hira suke yi a kan mum ɗinsu, suna tattaunawa a kan ina take? Ina ta shiga? Ina ta tafi ta barsu? Ta mutu ne ko tana raye? Suna kewarta.

Yana damke kan maciji, macijin ya harÉ—e mashi hannunsa da bindinsa, matse kan ya yi da karfi dan ma kada ya fito da waÉ—an nan shegun harshen nasa mai baki biyun ya caka mashi dafi.

Kusa da Prettyn ya zauna tare da ɓoye hannunsa da ya riƙe macijin ta bayansa dan kada ta gani. Jin an zauna a kusa da ita yasa ta juyo da sauri.

"Lah Kamran kai ne?". Ta faÉ—a cikin tsantsar farinciki tana sakin murmushi.
Chapter 143 · 0% Book details