← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 180

Sashe 120

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana daga kwance a jikinsa ta ce. "A'a ban sani ba, shima wani kalar abincin na Mammarka ko kuma fruits ne?". Ta yi maganar ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba, tana kwance tana ganin zubar ruwar ƙorama abinta.

Ajiyar zuciya ya sauke, jiya wuni zunbur ya yi yana bincike cikin littatafan Mammarsa ba tare da sanin Mammar ba, a nan ne ya ci karo da wata littafi mai suna true love never end, da yake litattafin bata da yawa sosai, short story ne da bata wuci pepar ashirin ba, sai ya nutsu ya karanta, a nan ne ya samu abubuwa da dama har amsarsa na dan gane da aure, kasancewar a littafin ya karanta duk wahalar da jaruma da jarumin suka sha daga karshe sun yi aure sun mallaki juna, kuma sun haifi ƴaƴa, a nan ne ya fara tunanin kenan shi ma dai yana da baba? Ba iya mama bace kawai?. Ya dai samu abubuwa da dama a ciki littafin, ya kuma yi masu kyakkyawar fahimta, ya kuma tarawa kansa uban tarin tambayoyin da ƙwaƙwalwarsa take ƙoƙarin kasa ɗauka, ya kasa iya tambayar Mammarsa ina babansa? Ya kasa iya gaya mata labarin su Pretty, ya kuma rasa ta ina zai iya sanar da ita cewa an bashi auren Pretty, kuma da ya karanta wannan littafin ya fahimci yana son yarinyar nan Pretty, kuma zai aureta ɗin kamar yadda mum ɗinta ta bashi aurenta, duk ya kasa samun kwarin gwiwar iya sanar da mamma komai, ya shiga damuwa na wuce misali, sai saƙa da warwara yake yi na yadda zai ɓullowa da Mamma ta bashi amsoshinsa a kan waɗan nan al'amura.

Lallai akwai cakwakiya, finally ga shi dai Kamran yasan menene aure da ma ita kanta soyayyar, sannan kuma yasan cewa yanzu mace bata haihuwa ita kaɗai, har ya fara tunanin to shi ina nasa uban? Ga wani sabon cakwakiya kuma da Sweetie ta matsa mashi a kan su kurewa dajin nan tafiya ko akwai wasu mutane a wajen dajin, dan ita bata yarda da cewa suma warriors ɗin nan a cikin dajin nan suke ba. To Kamran fans ya kuke tunanin makomar Mamma idan har Kamran ya fita daga cikin wannan dajin yaga akwai mutane a wajen? Anya zai sake yarda ya zauna a dajin kuwa? Anya zai iya yin hakuri ya danne ba tare da ya buƙaci sanin ina mahaifinsa yake ba kuwa? One day one time da wuya idan bai tambayi Mamma da ta fito mashi da babansa ba, duk da yanzu yana tsoron tambayarta, amma dakamar wuya ya iya hakuri da babansa... Tashin hankali kenan, babbar magana!!. Forest ma ya kusa kamawa da wuta da alama!.

"Pretty soyayya ba abinci bane sarkin son cin abinci, kuma soyayya ba kayan fruits bane, wani abin ne na daban". Ya bata amsa ta hanyar raÉ—a mata a kunne.

Jin cewa ba abinci bane kuma ba kayan fruits bane soyayya yasa ta yi saurin É—ago da kanta daga saman kirjin nasa ta juyo garesa. "To menene kenan?".

Yadda ta É—ago da kan nata sai ya zama suna fuskantar juna. Tsura mata ido ya yi yana kallonta, tun da ya fahimci sonta yake yi sai ya dai'na jin wani irin yanayi tare da fargabar kallon cikin idonta, sai ya zamana ma idan bai kalli cikin idanun nata ba sam baya jin daÉ—i.

"Ya kake ta kallona haka Kamran? Na ce maka menene soyayyar baka bani amsa ba? Wajen yawo ne to? Ko dai wasu dabbobin ne?".

A hankali ya motsa kyawawan lips É—insa ya furta. "Kece soyayyar mana".

Kyafta idanunta sau biyu ta yi tare da sakar mashi wani irin cool murmushi mai kara mata matuƙar kyau, har dimples ɗinta suka lotsa. "Kai kam Kamran wani lokaci ka iya maganar banza, ni ce soyayya kuma? To ni dai sunana Pretty ba soyayya ba".

Tun daga yanayin maganar Pretty zaka fahimci duk wanda zai auri wannan yarinya yana ruwa kusa da kada, sai ya shirya shanye duk wani shirmenta har Allah ya gyara mashi ita, ko da yake yarinta ne sosai a kanta, Æ´ar shekara goma zuwa shaÉ—aya nawa take dama? Ai yarinya ce sosai.

Da yake shi Kamran ya saba da halin kayarsa, sai ya ɗan matso da face nasa dab da tata, ƙasa ƙasa kamar mai tsoron wani kada ya jisu ya ce. "Ai ban ce maki sunanki ne soyayya ba bare ki ce mun sunanki Pretty, duba idonta a wajen kamar na raƙumin dawa".

Da yake ba'a yi mata ta kyale sai da ɓallah mashi harara tare da faɗin. "Ai garani ma idon Raƙumin dawa ce da ni, kai kuma idonka kamar na wannan Rocky ɗin naka". Ta kai karshen maganar tana kara ɓallah mashi harara.

Murmushi kaÉ—an ya É—an sakar mata kafin ya ce. "Na ji to, yanzu dai koma menene ki sani dai ina sonki".

Shiru ta ɗan yi, sai yanzu kalmar ina sonki ya fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwata, mum ɗinsu tana yawan gaya masu cewa ina sonku ƴaƴana, kune duniyata kuma kune komai nawa, ina alfarhari daku kuma ina son yin rayuwa da ku, na kasance da ku na kuma kula da ku, na baku tarbiya irin ta addinin Musulunci na kuma baku ilimin addini dana zamani, ina kaunarku fiye da yadda nake son kai'na.

Sosai maganganun mum ɗinta suka rinƙa yi mata zarya a cikin kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta, kenan yanzu shi ma Kamran irin son da yake yi mata kenan? Irin son da mum ɗinsu take yi mata?

Ganin ta luluƙa duniyar tunani ne yasa ya kai hannunsa ya ɗan shafi lallausan kumatunta haɗe da dogon kyakkyawar hancinta da ya zauna ɗas a face ɗinta.

"Kema kina sona ko?". Ya faÉ—a a hankali.

Kara kallon cikin kwayar idanunsa da kyau ta yi kafin ta ce. "Ni ban san menene ma'anar kalmar ina sonki ba, mum É—inmu tana faÉ—a mana shi, so ni ban san me take nufi ba".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara yi mata bayanin menene soyayya kamar yadda ya karanta a wancan littafin, sai dai ya ɓoye mata menene aure da kuma ganowa da ya yi cewa suna da iyaye maza, dukka ya ɓoye mata wannan, saboda a ƙananun shekarun nan nata ba fahimtar komai zata yi ba, sai dai ta kara tabka mashi shirme, dan haka sai ya yi mata bayanin abin da zata gane kawai cikin sauki.

Ɗan taɓe baki ta yi a lokacin da ya gama yi mata bayanin menene soyayyar. "Dama wannan ce soyayya? To ai ina sonka nima". Ta bashi amsa tana kallon cikin idonsa.

Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗi da sakar mata cool murmushi mai matukar kyau, ya ji daɗi sosai. Tabbas kamar yadda ta faɗa tana son shi haka ne, tana son shi amma ba kamar yadda shi yake sonta ba, kunsan kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to hakance, dole zasu so Kamran sosai, dan a yanzu shi ne komai nasu.

Cigaba da hirarsu mai shegen daÉ—i a tsakaninsu suka yi, yana kara fahimtar da ita yadda soyayya take, ta wani kasa kunne tana É—aukan bayanai, ita kuwa Sweetie tana can tana barci abinta, ba ruwanta da hayaniya.

Sun jima a haka kafin nan ya ce mata zai koma gida ta tashi ya rakata wajen maɓoyarsu da yamma zai dawo su sha hira da soyayyarsu. Sam bata so tafiyarsa ba, kawai dan ba yadda zata yi ne, tana matuƙar jin daɗin kasancewa da shi, idan ya ce zai koma har ji take yi kamar ta yi kuka ko kuma ta bi bayansa su tafi a tare, amma ba hali. Haka ta miƙe tana turo baki, sai hakuri yake bata, har da goyata a bayansa ya yi izuwa wajen bakin ramin nasu, duk dan baya son ganin fushinta, duk dan ya lallaɓata ta yi farinciki kafin su rabu.

Da kyar ya iya sakata dariya kafin su rabu, sai da ta yi dariya mai sauti ma tukun nan, sannan ya ce ta shiga ciki kuma kada ta yarda ta tashi Sweetie daga barci, sannan kada ta sake fitowa waje sai ya dawo da yamma. Da okey kawai ta amsa mashi kafin ta sa kai ta wuce ciki. Shi kuma bayan ya tabbatar da ya rufesu da kyau sai ya nufi gida.

A bakin kofar shiga ƙogonsu ya ci karo da Rocky dake ta faman barci, da alama ya ci ya ƙoshi ne, wucewa ciki ya yi izuwa cikin ɗakinsa. Ga mamakinsa sai ya isko Mammarsa a cikin ɗakin nasa tana yi mashi bincike.

Bai nuna mata ya yi mamakin hakan ba, ya wuce kawai ya haye saman gadonsa yana faÉ—in. "Mamma sannu da hutawa ina abincina?".

Zuba mashi idanu sosai ta yi na Æ´an sakanni kafin ta ce. "Kamran cire hular kankan nan bari na gani".

Da yake ya manta shap da zancen cewa Pretty ta yi mashi kitso, sai bai wani damu ba, yana kallon face É—in mammar tasa ya cire hular.

Kun san fa idan mutun ya yi kitso koma ya take sai face ɗinsa ta ɗan canza, shi ne yasa Mamma ta iya ganewa, kuma da yake taga wannan uban tulin gashin nasa da idan ya sanya hula take cika hular duk ta ɓace, hakan yasa ta fahimci an taɓa mashi gashin, shi yasa ta ce ya cire hular ta gani, sam bata kawowa ranta cewa kitso ma aka yi mashi ba, ta dai fi tunanin cewa shi ne ya datse gashin nasa ya zubar.

Zaro idanu waje ta yi sosai tana kallon kitso guda biyun, tun da take da shi ko da sunan wasa bata taɓa yi mashi kitso ba, bata taɓa kwatanta yin kitso bama, dan ita gashin kanta baya kitsuwa saboda tsantsi, to a ina kuma ya samo kitso? Tasan dai ba shi ya yi wa kansa ba, dan bai iya ba.

Shi kuwa ganin yadda ta zaro idanun nan nata tana kallon kan nasa ne yasa ya yi saurin kai hannunsa saman gashin nasa dan ya ji menene ya sanyata zaro idanu haka?.
Chapter 120 · 0% Book details