← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 180

Sashe 128

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramish yana da kani mai suna Bilal wanda ya kasance yaya ne ga Gimbiya Chuchu uwarsu ɗaya, wato ɗan mummy kenan, Bilal air force ne shi, ba sai na tsaya yi maku dogon bayanai a kan su waye air force ba, kun san jami'ai ne da suke sadaukar da rayukansu a kan ƙasarsu, sun fi sojoji shiga haɗari nesa ba kusa ba, su ɗin jami'an sama ne, yakin sama ake turasu, jami'ai ne da ba kowa yake iya yin aikin da suke yi ba, jajirtattun ne kuma jarumai na gasken gaske. Bayan Bilal kawai Dr Raj wanda ya kasance shi ma ɗan mama ne, Kanin Ramish kenan uwa ɗaya uba ɗaya, shi kuma hamshaƙin Medical Dr ne, mutun ne shi da ya san aikinsa, baya kuma wasa da aikinsa, bama sai na ɓata bakina wajen gaya maku cewa yaran King Zuhair basu da wasa ba, ku da kanku kun san jininsu a tafashe yake, sun gada wajen mahaifinsu, Akka da take mace ma da yake jinin Modarawa ne ke gudu a jikinta ita ɗin ma, baku ganinta a zafafe take ne? Tana da zafin nama bare kuma su maza, sam basu da wasa ko kaɗan, kuma idan ka kuskura ka kawo masu wasa a cikin lamuransu yanzun nan zasu saɓa maka kamanni.

Rizwan kuma wato yayan Yah Jawad, kamshaƙin ɗan kasuwa ne wadda yake business tsakanin manyan kasashen duniya, yana da kamfanonin a ƙasashe daban daban, baya da ra'ayin siyasa ko sarauta, haka zali baya ra'ayin kaki, duk da cewa kowace irin kaki ya yi ra'ayi zai iya sanyawa ga jikinsa ya yi aiki, domin kada ku manta da muƙamin uncle ɗinsu wato uncle Abu Abdussalam bin Badeen, shiyasa su Ramish ɗin ma suke da manyan muƙamai a wajen aikinsu, kuma ya haɗu da basu da wasa, jajirtattu ne su ɗin. To shi Rizwan ya zaɓi kasuwanci ne abinsa, shi ne ra'ayinsa. Dukkan ƴaƴan King Zuhair idan ka kallesu ba sai an ce maka ƴaƴansa bane, akwai alamar kamanni ta jini a tsakaninsu, musamman Ramish da kaninsa Dr Raj, suna kama sosai, duk kuma kamannin Akka suka ɗauko, shiyasa suke sajewa da su Abu Abdussalam bin Badeen, sun zama dai duk iri ɗaya.

Wannan shi ne takaitaccen labarin waÉ—an nan zaratan samari na Abu Abdussalam bin Badeen wanda kuma ya renesu kamar wasu zakuna, suka taso a haka, tun suna kanana suke a hannunsa, shi kuma Æ´aÆ´ansa maza biyu basu a tare da shi, suna gidan the most powerful King Badeen, wato gidan mahaifinsa kenan, Æ´arsa Sharifat ce kawai a gidan, sai Ummie, yana kaunar King Zuhair ne over, hakan yasa yake kaunar Æ´aÆ´ansa ma.

To mu koma kan labarinmu tun da kun ji su waye su Ramish, ɗan mama ne dai, mama sarkin masifa, ƴaƴanta maza biyu ne sai Aneesa ta uku, kuma ga duka yayan nata da Ramish da kuma Dr Raj ɗin duk a Dubai, amma a haka kullum take tsayar da bala'i a kan ita King baya yi mata adalci, ya fi son Momman auta, ɗan adam kenan, ba'a iya mashi, ita fa ƴaƴa maza manya har biyu ke gareta saɓanin Mummyn Gimbiya Chuchu da take da iya Bilal kawai, amma Mummy bata wani damu ba, ita kuma mama sarkin haɗama so take ace ita kaɗai ce take da ƴaƴa maza, kuma fa su Ramish ɗin nata sune manya a kan Bilal ɗin Mummyn Gimbiya Chuchu, idan ma mulki take so ai su zasu karɓi mulki, amma ita dai duk bai yi mata ba, sai ka rasa me take so a duniyar nan kuma, mummy ma fa tana da babban ɗanta na fari kafin Gimbiya Aunty MieMie wanda ya rasu, rasuwa ya yi shiyasa yanzu su Ramish sune manya a kan Bilal ɗinta da yake matsayin ɗanta a uku, sai Chuchu auta. Fatan dai kun gane?.

A kullum baza idanu Leesharh take yi tana tunanin ta in da zata kalli Ramish, amma shiru babu shi babu labarinsa.

Yauma dai kamar kullum, ta gama aikin gyaran parlourn ita da su Fadila da suka tayata, tana shirye cikin arab jallabiya ash color, ta yi kyau matuƙa, yanzu ta kara gogewa ta yi wani fresh da ita, ta kuma ɗan yi kumatu, amma kullum tana cikin zulumi tare da fargabar ya zata kalli Ramish? And ya zata kaya da wannan aiki da yau tsawon wata guda kenan bata fara shi ba? Yaushe zata kammala wannan aiki har ta koma ga mahaifinta?. Kullum tana cikin yin wannan tunani.

"Leesharh ki je ki gyara room É—in guyson and na Aunty Sharifat bari mu kuma mu fara shirya kayan abinci kamar yadda muka saba". Cewar Fadila.

Da okey ta amsa masu tare da nufar room ɗin nasa, shi kansa Omar ɗin yau tsawon wata kenan bata samu damar ganinsa ido da ido ba, sai dai a wannan hoton, kuma kullum ita take gyara mashi room ɗin nasa, amma suna samun saɓani sosai da shi, wani lokaci sai ya fita take shigowa ta gyara ɗakin, wani lokaci kuma tana gama gyara ɗakin ta fita shi kuma zai shigo, Sharifat ta so ta haɗata da shi dan ya ga kyakkyawa, amma ina ba dama, dan kuwa bai zauna ba, yana shirye shiryen komawa KINGDOM OF POWER, so dayawan lokuta yana gidan King Badeen, yanzu bai cika zama a gidan Abu Abdussalam ba, shiyasa basu haɗu ba.

Room É—in nasa ta nufa, hannunta na rike da mooper da abin share share. Duk da ta san cewa ba lallai ta sami mutun a cikin room É—in ba hakan bai hanata ta yi sallama cikin sanyin murya ba. Tana yin sallamar kuma ta afka cikin room É—in. A tsakiyar É—akin ta ajiye kayan share share da goge gogen nata. Kai tsaye ta nufi saman katafaren bed É—insa na alfarma mai matukar girman gaske, room É—in nasa ya ji komai na more rayuwa, sai tashin kamshi yake yi, ko'ina tsab tsab, amma a haka sai ta sake gyarawa ta goge ko'ina.

Jibgegiyar duv ɗinsa dake a saman bed ɗin nasa ta sanya hannu tana ƙoƙarin janyewa, domin ta cire ta canza mashi wani, kullum sai ta sake wani bedsheet ɗin, bata da tabbacin ana kwanciya a gadon ne ko ba'a kwanciya, amma dai kullum sai ta canza.

Tana ganyo duv É—in mutun ya bayyana kwance a saman gadon, da yake duv É—in yana da girman da idan mutun ya kule a ciki ma ba lallai kasan yana a cikin É—in ba, ba zaka yi zaton akwai shi a ciki ba, shiyasa ta zo ta janye kawai.

Tana janyewa kuma kamar wadda aka yi wa allura ya fara mutsu mutsu haɗe da murkusoso kamar wadda yake shirin mutuwa, tamkar ana zare mashi rai, juyi ya fara yi a saman bed ɗin, jikinsa na a sanye da farar jallabiya tas da shi, farar kyakkyawar fuskarsa ta yi kal kal da ita, ya yi wani fayau, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin mawuyacin hali, kyakkyawar arab hairnsa da ya zubo mashi har ta gaban goshinsa yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ga shi kwanciyar ruf da ciki ya yi, so ya bawa Leesharh ɗin baya, ko ba'a gaya mata wanene bane tasan shi ne guyson, saboda room ɗinsa ne, kuma tasan hotonsa, kullum idan ta shigo babbar parlourn da face ɗinsa take fara cin karo, yana sakin ƙayatatcen murmushi, so tasan shi ne.

Ganin shi cikin wannan mawuyacin hali ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, a razane ta zaro dara daran idanun nan nata tana kallon yadda take juyi kamar ba zai rayu ba, idanuwansa a rufe ruf, yama datse idanun nasa ne sosai tamkar zai fasasu, da alama yana jin tsananin azaba, kuma da alama ma baya a cikin hayyacinsa, sai wasu siraran hawaye da suke fita mashi daga idanuwansa suna bin gefe da gefen face ɗinsa, hakan zai kara tabbatar maku da yana cikin mawuyacin hali.

Sam Leesharh bata taɓa kallon irin hakan ba, hakan yasa hankalinta ya yi mummunar tashi, cike da ruɗu ta...........

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 26/8/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________38🔥

*Assalamu alaikum everyone ina fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya?! Allah yasa! Ina yi wa kowa da kowa fatan alkhari tare da fatan kasancewa cikin ni'ima da kuma rahmar Ubangiji, a duk in da kuke Allah ya cigaba da dafa maku yana kara tsareku da tsarewarsa, Allah ya jiɓanci al'amuranmu bakiɗaya, ina matuƙar farinciki tare da godiya da irin tarin addu'oinku dana samu daga bakunanku masu albarka, na kuma ga tasirin addu'oinku wlh, Allah ya amsa jikina ya warware Alhdulillah, babu abin da zance maku face in ce Allah ya bar kauna ya kuma cikaku da farincikin da babu bakinciki a bayansa, arxikin da babu talauci a bayansa, daga karshe Allah ya bar kauna ina godiya 💘 taku PRINCESS TEEMA ta amana✍️💘*

E____________38🔥

Sam Leesharh bata taɓa kallon irin hakan ba, hakan yasa hankalinta ya yi mummunar tashi, cike da ruɗu ta kai hannunta ta mayar mashi da duv ɗin da nufin ta gudu ta fice daga room ɗin kada ace ita ta yi mashi wani abin, kunsan maras gaskiya da shegen tsarguwa, sai yaga kamar komai ƙanƙantar motsi idan ya yi asirinsa zai iya tonuwa.

Sannan kuma kunga tana janye mashi duv É—in ne ya fara wannan murkusoson, so sai tana ganin kamar za'a ce ita ce sila.

Har ta juya zata fita ta tsinkayo zazzaƙar voice ɗinsa ya daki dodan kunnuwarta, idanunsa a datse gam yana ruwan hawaye, voice nasa ɗan siriri kamar na mata, ga shi cool voice gare shi sosai, akwai daɗin saurara, bare da ya haɗu da yana cikin ciwo, sai maganar tasa tana fita wani iri.
Chapter 128 · 0% Book details