Sashe 137
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A fusace Haidar ya shigo cikin ɗakin, a haukarsa da rashin hankalinsa wai zai daki maman Zainab ɗin. Ai kuwa yana zuwa Sadiq ya tare shi, dan kuwa ya biyo bayansa, saboda yasan halinsa sarai, tun da yaga ya shige cikin parlourn yasan ba zasu yi da kyau ba, shi kuwa ba zai bari su taɓa mashi ƴar uwa ba, tun da faɗar ba'a kan ƴaƴa bane tsakaninsu da ƴar uwarsa ce yana da damar saka baki ya tare mata, da ace faɗar a kan su Khadijah ne to fa bashi da bakin magana, amma a kan ƴar uwarsa yana da bakin magana. Aikuwa ya tare mata a in da ya ce wlh in dai Haidar ya ɗaura hannunsa a jikinta yau sai ya gwada mashi banbancinsu, jahili wanda bai san me yake yi ba, angaya mashi ana taɓa matar aure ne? Matar mutun kawai kasa hannu kace zaka daketa, ai ko kotu aka je in dai shari'ar musulunci za'a bi sai a ɗaureka har igiya ta yi saura a kan hakan.
Da farko Haidar ɗin ya so kama Sadiq ɗin da kokawa. Amma ina Sadiq ya nuna mashi ya fishi hankali da sanin ciwon kansa a in da ya ce da maman Zee ta wuce cikin bedroom ɗinta ta rufe kofa ta rabu da su, idan suka gama hauƙarsu ba'a kulasu ba za su kama kansu.
Da sauri ta wuce cikin room É—inta, ta bi maganar É—an uwan nata. Tana jiyo muryar Hajiyarsu tana cewa to ai ba gidan ubanki bane da zaki shige cikin É—akin, ki fito ki tafi gidan ubanki marasa kunya marasa tarbiya, wlh sai kin bar gidan nan tun da ku baku da albarka dangin matsiyata, dole ya zo ya sakeki ki wuce gidan ubanki tun da har da ni zaki yi wa rashin kunya, dan kin rai'na taki uwar.
Wato ita fa Hajiyarsu bata san cewa yanzu fa baban Zainab bayan Hauwa baya jin maganar kowa ba, har da wani cewa zata sa ya saki maman Zainab, wlh ana show a wannan gida, ana rikici, ko ya tsohuwar nan zata ji lokacin data ga Hauwa na juya mata É—a? Mu dai ana yi muna shan Maltina.
Ko juyowa maman Zee bata yi ba bare ta kallesu har ma ta kulasu, tana jin hajiyar tasu ta ce kada ta yarda ta shiga cikin bedroom É—in nan ta zo ta wuce gidan ubanta, amma ina ta wuce ciki ta banko masu kofa da karfi tare da murza key abinta, irin bata da lokacin sun nan.
Shi ma Sadiq sa kai ya yi ya wuce ya fita abinsa, dan bashi da lokacin biyewa haukarsu a cewarsa, shi a mahaukata ma yake kallonsu, idan sun ga dama su kwana a cikin parlourn suna surfa masifa su dai suka sani, shi dai ya kama kansa abinsa. Baban Zainab ma yanzu ba samun damar ganinsa zasu yi ba bare har su ce ya saki maman Zainab ko su gaya mashi ta yi masu rashin kunya, idan ma sun sami damar ganinsa to ko kallo basu isheshi ba, shi da yake ta Hauwa ina ruwansa da su? Idan ma suka yi wasa sai ya haɗa masu da zagi da kuma duka koma ya ce bai san su ba. Tirƙashi, ana cakwakiya a gidan baban Zainab fa sosai.
Haka suka yi ta surfa uban masifa mai isarsu, da dai suka ga ba mafita sai suka kama kansu, dama shi Haidar already ya bi bayan Sadiq da nufin ya je ya kama shi da faÉ—a, amma ina Sadiq É—in yaki biye mashi, dama yaga zai takura mashi sai ya É—auki wayarsa ya fice daga cikin É—akin, ya bar masu gidan ma gabaÉ—aya, sai dai bai yi nisa da gidan ba, dan yana tsoron ya yi nisa kada su yi wa maman Zainab É—in wani abin.
Haka suka yi ta haukarsu har suka gaji suka hakura suka tafi. Ita kuma maman Zainab tana shiga cikin É—aki ta É—auki waya ta kira mamanta dan ta sanar da ita halin da ake ciki na batun Zainab. Khadija kuwa wadda tun da taga Æ´an uwan baban nata sun zo ta gudu ta shige cikin room nasu ta rufe kofa kamar basu a gidan, dan haka Sadiq ya gaya mata, ya ce kada ta sake tsayawa a wajen da Æ´an uwan babanta suke faÉ—a da mamanta, idan taga sun zo ta shige cikin É—akinsu su rufe kofa babu ruwansu.
Bugu É—aya mamarsu ta É—auki wayar, Æ´ar dattijuwa tana zaune a saman dadduma, kullum cikin yiwa Æ´ar tata addu'a take yi a kan Allah ya kawo mata mafita.
Bayanai ta kora mata dan gane da halin da Zainab take a ciki kamar yadda Sadiq ya ce ta gaya mata. Ajiyar zuciya maman tata ta yi tare da kara yi mata nasiha mai ratsa jiki sosai, daga karshe ta rufe fa ce mata. "A duk in da kike Aisha ki kasance mai jin tsoron Allah, in ma a lokacin kaɗaicewarki ko a cikin mutane, ki sani idan kowa baya ganinki to shi Allah yana ganinki kuma baya barci, dan haka kada ki ji tsoron kowa ki ji tsoron Allah shi kaɗai, sannan ita kuma Zainab ki samu ganyen magarya guda bakwai, ki daka shi a wajen da babu ya ji, sannan ki zuba shi a cikin ruwan da zai ishata wanka, sai ki karanta mata suratul baƙra aya biyar ɗin farko, ki haɗa da ayatul kursiyu kafa ɗaya, sai wattabau ma tattlusshayaɗini ala mulki sulaimanu waman kafara sulaiman har dai zuwa karshen ayar, sai amanarrasulu kafa ɗaya, sai ayoyin sihiri wato wa auhaina musa zuwa karshe, sai kala musa attakiluna maja'akum sihirulhazakulyan shi ma har karshe, sai kulhuwallahu kafa uku, falak da nasi kafa uku uku, daga karshe ki rufe da fatiha ki tufa a cikin ruwan ganyen magaryar, a bata ta yi wanka da shi".
Wannan duk girman sihirin da aka yi wa mutun manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce in dai ka yi hakan to ba shakka wannan sihiri duk girmanta sai ta warware, koda kuwa da me aka haÉ—ata wlh sai Allah ya kwance ta, sai ta warware, so wannan ba iya Zainab na bama ba, gabaÉ—aya al'ummar Annabi na bawa, Allah ka tsaremu da tsarewarka, ka shiga tsakanin nagari da mugu. Idan kin ji daÉ—i kafin ki wuce ki mun addu'a ko wace iriyace in dai ta alkhari ce a gareni ina so.
Godiya maman Zainab É—in ta yi mata tare da yi mata fatan karin samun lafiya, sannan suka yi sallama.
Shiru ta yi bayan ta ajiye wayar a gefen gado tana tunanin da zata samu ace baban Zainab ma ya yi wanka da wannan haÉ—i da zata yi wa Zainab É—in, ai da shikenan kashin Hauwa ya bushe, asirin zai karye asirinta ya tonu, komai da zai dawo daidai, amma ina babu halin ta yi wa baban Zainab É—in, ina ma ta gan shi da ido ma bare har ta haÉ—a mashi wannan haÉ—in? Ai bata ma ga alama ba, hakuri kawai zata yi ta cigaba da addu'a har Allah ya kawo mata mafita, ita kuma Zainab da izinin Allah zata samu lafiya komai ya wuce ya dawo normal.
Gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike taf da tunanin mafita, sai addu'a take yi na Allah ya kawo mata saukin al'amura da haka barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.
🕊ï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸
ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN EMPIRE.🌼
Sosai Leesharh take yin aikinta na gyare gyare kamar yadda aka umarceta, sai dai tana taƙa tsantsan da ƴan gidan sosai.
Kwance take a saman bed É—inta daga ita sai doguwar riga mara nauyi, hular rigar ce a kanta, ta yi shiru tana tunani, ta kammala aikinta na yamma, ta yi sallar la'asar.
Ta yi nisa cikin tunanin da take yi kamar daga sama ta ji wayarta ta ɗan yi kara alamar shigowar sako, wayar da tun da ta zo gidan bata taɓa amfani da shi ba bayan duba time, ba'a taɓa kiranta ba, sai ga shi yau saƙo ya shigo ciki. Cikin hanzari ta janyo wayar har hannunta na kerma, a ƙage take da taga wani saƙo ne?.
Unknown number ce wadda aka rufeta da kyau, da ita aka turo mata sakon. Cikin hanzari ta fara duba saƙon ba tare da damuwar sai ta kalli number ba, ita dai me saƙon ya ƙunsa kawai take son sani, ba wani karatu sosai can can ta iya ba, amma dai ba laifi.
Jikinta har yana kerma wajen buɗe saƙon, miƙewa ta yi daga kwanciyar da take ta zauna tare da fara karantawa. Saƙo ne da aka turo mata a kan su Sharifat, ya tabbata dai duk wani motsinta suna sane da shi, rubutu ne kamar haka. A'isha tun da Sharifat ta nuna tana son samun kusanci dake to dama mu haka muke fata, dan haka ki saki jiki da ita ta yadda zaki shiga jikinta sosai, ta hanyarta ne kawai zaki iya samun damar isa wajen da Ramish yake, domin kuwa ta hanyar mutun ɗaya zaki samu kusanci da Ramish, ta hanyar Omar ne kawai, shi kuma dole sai ta kasancewarki kusa da Sharifat, idan kika shaƙu da Sharifat tabbas shi ma zaki shaƙu da shi, dan su ɗin abokai ne, idan kuma kika shaku da shi to tamkar kin shaƙu da kowa na cikin gidan ne, kin ga kuwa zamu samu abin da muke so, kema zaki kammala aikinki da wuri ki zo ki koma ƙasarku, ammafa ki kula sosai, kada ki saki baki, ki dai shiga jikinta sosai, kuma kin yi ƙoƙari taimakon Omar da kika yi, hakan ma wata dama ce da zata sa ki samu kusanci da shi, ko na ce ma yanzu ma kin samu kusanci da shi tun da har ya kulaki, ki cigaba da dagewa saura kiris mu isa in da muke so.