← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 180

Sashe 32

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ya kara zaro mata waɗan nan fararen idanuwan nasa yana kallonta ne yasa ta ɗan tsorata, nan take tsoro ya bayyana a saman fuskarta, hakan kuma sai ya kara bayyanar mashi da kamanninta da mum twins, dan rana ta farko da ya fara kallon mum twins fuskarta a cike yake tab da tsoro, duk a firgice take, so ba zai taɓa mantawa da wannan yanayi da ya fara ganinta a ciki ba.

Da sauri ta raba jikinta da nasa, a tsorace ta fara yunƙurin barin wajen.

A hanzarce ya riko hannunta, da harshen turanci ya tambayeta ina mamanta da Æ´ar uwarta?.

ÆŠan zaro idanunwanta ita ma ta yi tana tunanin a ina ya san tana da mama da Æ´ar uwa? Waye shi ma tukun nan.

Bata bashi amsa ba, sai ta yi ƙoƙarin gudu ta bar wajen, sake ta ya yi tare da miƙewa tsaye, nan take yanayin face nasa ta sauya, kome yasa hakan oho?

Yana saketa ta miƙe da gudu ta nufi ta gefen ƙoramar. Da gudu Rocky ya yi yunƙurin bin bayanta, da sauri Kamran ɗin ya dakatar da shi, dama yasan in dai ta gudu Rocky zai bi bayanta ya kamota ya dawo da ita.

A hanzarce Kamran É—in ya rufa mata baya, dan yaga ina ta nufa, ita kuwa tana barin wajen nasu sai ta daina guduwar, ta fara tafiya da sauri sauri, dan kafarta babu takalma, idan ta ce zata yi gudu to tana iya taka wani abin ya ji mata ciwo, so dole ta kula sosai, ta tafi cikin nutsuwa, ta kuma lura da in da zata taka.

Bata san Kamran É—in ya biyo bayanta ba, dan a sese ya biyo ta, baya son ta gansa, yana so ne kawai yaga shin suna a tare da mamarsu ce ko dai bata a tare da su.

Meyasa yake tunanin bata tare da su kuma? Hakan na nufi akwai wata a kasa kenan? Ko kuma akwai wani abin da ya sani? To mu dai namu ido kawai.

Ta yi tafiya mai ɗan nisa kafin ta isa wani wajen da gabaɗaya farin yashi ne a wajen, babu ciyayi, sai bishiyoyi dake ɗan gefe gefe. Cigaba da tafiya a cikin yashin ta yi har sai da ta isa karshen yashin, ta fara shiga cikin ciyayi, sannan ta tsugunna a wajen tare da sa hannunta a cikin ciyayin ta buɗe wani waje kamar kofa da aka yi da itace, tana buɗewa ta shiga cikin wajen tare da zuro hannunta ta ja marfin ta rufe, wajen ya koma kamar ba'a taɓa buɗe shi ba.

Mamaki kaɗan ne ya ɗan kama Kamran ɗin, a jikinsa yana jin duk yadda aka yi wannan ƴar mum twins ce, koma yaya ita ce ɗaya daga cikin twins, dan ga kamannin mamarsu a saman fuskarta, duk da ba wani kama sosai suke yi ba, amma tabbas wannan ƴaƴanta ne, dan jini ba wasa ba. Nan take kuma fuskarsa ta sake sauyawa, alamar damuwa da ɓacin rai ta bayyana a saman fuskar nasa, a take jikinsa kuma ta saki kamar wadda aka zarewa laka, tunanin mum twins yana jefa shi cikin mawuyacin hali, ko me dalili oho?.

Ya jima a tsaye a wajen kamar wadda aka zarewa laka, jikinsa duk ya yi la'asar, da kyar ya iya motsawa daga in da yake tsaye ya nufi wajen da ta shiga É—in, dan ya duba ita da waye a cikin?.

kafin ya ƙarisa wajen bari mu leƙa KINGDOM OF POWER mu dawo.

🔥✨KINGDOM OF POWER💪👊

Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haÉ—aÉ—en shinfiÉ—i na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da..........

Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.

🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/7/2024.....✍️📚🌹

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________11🔥

🔥✨KINGDOM OF POWER💪👊

Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haɗaɗen shinfiɗi na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da kyawawan kwalliya na gidan sarauta, da alama wajen hutawa ne, wajen hutawar ma da alama na wani babba daga cikin ƴan gidan ne, babba kuma wanda ake ji da shi, domin yanayin wajen sam bai yi kama da na ƙananan kwari ba, na manyan kai ne.

Tulin tuffa ne a cike a cikin gwando a gabanta, kuyanga ce ta kawo mata tuffar, yau dai Hoorain baya a tare da ita, da alama yana ta wani wajen, tana nan dai cikin wannan shiga tasu ta Æ´aÆ´an manyan sarakuna da ake ji da su, shigar yana yi mata mugun kyau sosai, kowa dai yasan kayan yara ya fi na manya kyau, to haka idan ta sa kaya sai ya fi kyau a jikinta sama da su Gimbiya Chuchu.

Har wa yau dai bata sanya hular alkyabbar a kanta ba, sai dai a yau ta sanya wani kyakkyawar hula mai matukar kyan gaske a kan nata, ta rufe gashinta, ba kasafai ta cika yawan sanya É—ankwali ba, dayawan lokuta zaka ganta babu É—ankwali a kai, ta fi son shan iska ta ko'ina.

A nutse ta kai hannu ta ɗauki apple guda ɗaya daga cikin kwandon Apple dake a gabanta, ta kai saitin ɗan bakinta zata gutsira. Bata ji motsin mutun ba, bata ji komai ba sai gani ta yi an kwace apple ɗin daga hannunta, bata ƙarisa kai shi bakin taba.

Cikin sauri ta É—ago kanta tare da É—ago da idanunwanta sama, dan taga wanene da wannan É—anyen aikin?.

Tsaye yake a gabanta, cikin kayansu na jarumai kuma jajirtattun mayaka, kamar kullum wannan hula tasu mai kan zaki tana a kansa, tsayuwar jaruman mazan nan nasa masu jini a jikan nan dai ita yake yi a kullum, kai daga ganinsa ma bakaga wajen wasa ba, baya É—aukar wargi.

Zuba mashi ido ta yi bata ce da shi ko uppan ba, yau karo na farko da ta ji tana son kallon fuskar wannan dakaren nata.

Ɗan dukar da kansa ƙasa ya yi, cikin girmamawa ya ce.

"Afuwa ranki shi daÉ—e, ina neman izinin yin magana".
Yau ya yi maganar da É—an sauti, sau da dama idan ya yi magana na kusa da shi ma basu jin me ya faÉ—a, saboda a hankali yake magana, baya fitar da sauti, baya É—aga murya.

Gera É—aya ta É—aga mashi alamar go ahead ya yi maganarsa ba tare da ta yi magana ba.

Sake ɗan risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ya karɓi umarnin kuma ya gode. Cikin natsuwa ya fara magana words ɗinsa na fita ɗaya bayan ɗaya babu hayaniya.

"Afuwa ranki shi daÉ—e, ban binciki tuffar bace shiyasa ban bari kin kaita bakin ki ba, Gimbiya Sarina ce ta aike ni, shiyasa ban samu damar bincikar tuffa É—in ba har aka kawo maki".

Tun da ya fara magana ta zuba mashi wayan nan dara daran idanun nata, ta kasa koda kyaftawa, yau shine rana ta farko da ta fara jin muryarsa da sauti, idan yana magana kasa kasa sosai yake yi, kullum tana tare da shi, amma bata taɓa ganin ya yi magana da kowa ba, sannan bata taɓa ganin fuskarsa ba, sakamakon wannan hular tasu ta mayaka dake rufe musu ko'ina a fuskarsu, baka ganin komai sai ido da tsagen ɗan baki, sai kofofin hanci, suma kaɗan kaɗan ne, bayan haka baka samun damar ganin komai na fuskarsu, ga kayan yakin nasu kuma da karfe aka yi shi, kunsan dai yadda kayan shahrarrun mayaka suke ai?, Amma duk cikin dakarun dake Masarautar ya fi su natsuwa, yana da hankali sosai, yana bata kulawa, gabaɗaya masu kula da su shi yafi bata kariya yadda ya dace, ko motsi ta yi sai ya matso kusa da ita dan ya ga menene, tana da tabbacin ko barci dare baya samun dama ya yi sosai, saboda ita, baya taɓa rabuwa da bakin kofar shiga arear part na King Zuhair.

Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce mashi. "Ai babu komai a cikin Apple ɗin, daga ɓangaren Momma aka ɗauko mun fa, kuma Aunty Chuchu da kanta ita ta haɗa mun su a kwando, amma nagode da kulawarka a gareni".

Ita ma cikin nutsuwa take magana, da alama yarinya ce mai hankalin manya.

Jinjina mata kai ya yi tare da risinar da kai ya sake É—agowa, sannan ya tsugunna a gaban kwandon Apple É—in, dan ya duba ya tabbatar da ingancinsu, saboda ya tabbatar da aikinsa, ya tabbatar ya bata tsaro yadda ya dace.

Da ido kawai ta bishi da kallo, bata ce da shi komai ba, shi ma bai sake yin magana ba har ya kammala bincikensa a kansu, sannan ya miƙe tsaye tare da komawa ɗan gefenta kaɗan ya tsaya. Ƙasa ƙasa kamar dai kullum ya ce mata zata iya cin Apple ɗin yanzu, babu wata matsala.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dawo da kallonta a kan gwadon Apple ɗin, a kullum idan zata ci abu in dai a waje ne ba'a cikin ɗakinsu ba, to sai Hoorain ya binciki wannan abin tsab, sai ya tabbatar da ingancin wannan abin, sannan yake barinta ta ci, hakan yasa take jin daɗin kasancewa a tare da shi, yana da kula sosai, ga shi babu ruwansa da kowa da komai, in da ya sa kansa kawai yake kallah, baya ɗaga kai ya kalli wasu ma abinsa, ga namijin jarumta da kuma nutsuwa.......... Ɗa ɗaya tilo ga commander ZAFAR kenan.💪

Baki a É—auke da sallama wata kuyanga ta shigo cikin wajen, hannunta na rike da wani kyakkyawar kuma tsadadden Apple laptop, sabuwa gal da ita.

A gaban Gimbiya Zunaira ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa ta nemi izinin yin magana.

Yadda kuka san mutun mutumi haka Hoorain yake tsaye, ko kallon in da suke bai yi ba, yana tsaye kamar saƙago yana fuskantar kofar shigowa abinsa.

"Mama Haulat menene yake tafe dake?". Cewar Gimbiya Zunaira É—in.
Chapter 32 · 0% Book details