← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 180

Sashe 156

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Autar ta ce. "Babu abin da ta yi mun Yah Jawad". Tana magana tana goga kanta a kirjinsa.

Izuwa yanzu ya fahimci abin sirri ne a tsakaninsu Chuchu take yi mata wasa da hankali take kuma sanyata kuka a banza. Dan haka sai ya ce. "Shikenan our Auta, jeki abinki yanzu zan bata punishment ba tare da na ji ma me ta yi maki ba". Ya yi maganar yana shafa kyakkyawa arab hairnta da ko É—ankwali bata É—aura ba ta shigo room É—in na Chuchun a ruÉ—e, dan a tunanin wani abin ne ya sameta.

Da sauri ta raba jikinta da na shi tare da nufar hanyar komawa room É—in na Chuchun rike da pillown tana faÉ—in. "Allah Aunty Chuchu ba zan yafe ba idan kika gayawa wani".

Juyawa da gudu ita ma Chuchun ta yi da nufin ta bi bayanta dan ta ji Yah Jawad É—in ya ce zai bata punishment, ba zata iya É—aukar punishment É—insa ba.

Aikuwa bai bari ta bar wajen ba ya yi saurin riƙo hannunta tare da janyota ta dawo in da take tsaye ta tsaya. Ƙasa da murya sosai ya yi kamar wani na yi mashi laɓe, kamar kuma maras gaskiya ya fara magana, ita kuma Auta ta yi tafiyarta sai kumbure kumbure take yi.

"Me kika yi mata? Meyasa zaki saka mana ita kuka?". Yana magana yana kallon cikin kwayar idanunta, while ita kuma tana ɗan satar kallonsa ta wani yi ƙasa da kai kamar wata mai ɗaukar darasin hadisi a islamiya!.

"Babu fa komai Yah Jawad". Ta faÉ—a a sanyayye.

Shiru bai sake yin magana ba, domin ya shagaltu da kallonta, gaskiyar uncle Abbas da King da suke cewa in dai zai haÉ—u da chuchu sai ya karewa Æ´arsu kallo tsab sannan yake kama kansa, ashe dai sun san komai.

Jin ya yi shiru bai sake yin magana bane yasa ta É—ago ido dan ta É—an saci kallonsa. Ai kuwa tana É—agowa suka yi four eyes.

"Yah Jawad in tafi?". Ta faÉ—a ba tare da ta kawar da kallonta daga saman fuskarsa ba, sai dai ba kallon cikin kwayar idanunsa take yi ba.

"Ban gama kallonki ba ai my Jannat". Ya faÉ—a ba tare da yasan lokacin da hakan ya fito daga bakinsa ba, sai da ya ji ta ce. "Kallona kuma Yah Jawad? Na yi kyau ne?".

Nisawa ya yi, kamar mai jin barci ya furta. "Over ma kuwa kika yi kyau".

"To Yah Jawad ka mun hoto". Cike da zumuÉ—i ta yi maganar.

Wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke tare da ciro wayarsa É—ayar. "Where's my other phone da na baki jiya?".

Sai a lokacin ta tuna da wayar. "The phone is in my room, in je in kawo shi yanzu?". Murya a warware ta yi maganar.

Girgiza mata kai kawai ya iya yi alamar a'a, bai iya sake furta komai ba sai matsowa da ya yi kusa da ita tare da shiga camerar wayarsa, sannan ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman shoulder ɗinta. Zafafan hotuna ya fara ɗaukarsu, ita da ta ce ya ɗauketa ita kaɗai ya ɓige da ɗaukarsu a tare.

Sai canza style suke yi sun manta da cewa a parlourn King fa suke, ga shi yau King yana da baki sosai saboda zuwan su Ramish da za su yi gobe, jama'a suna ta kai koma a part ɗin, already kun san dama akwai part na saukar muhimman bakinsa na kusa sosai a cikin part ɗin nasa, so su Jawad suna tsaye ne a tsakanin wannan ɓangare na saukar bakin da kuma hanyar nufa master room na King.

Canza style ya yi daÉ—i harda kwanciya a saman kirjinsa ta yi, yau abin nema ya samu, Chuchu mayyar É—aukar hoto, to ga dama ya samu, mai hanata É—aukar hoton ya takura mata yau da kansa yake É—aukarta, ai style kuwa sai abin da kuka gani.

Suna tsaka da kashe hotunansu basu ankareba kawai sai tsinkayo muryar Akka suka yi a cikin kunnuwansu tana sababi, ta nufo parlourn ɗin ne tana ta surfa sababi da masifa, da alama wani ya taɓota. Tun daga nesa take faɗin. "Ai Zuhair shi ne ya mori aure, ku cigaba da yi, har ku kwanta a gadon ajalima kada ku dai'na, yo ni idan baku yi haka ba ai sai nace sam sam Zuhair ba mata ya aura ba, kuma idan baku yin haka ai sai na sa a bincika mun ku ko da wata munafurcin a ƙasa, dan cikakkun mata kam dole sai sun ɗana wannan kishi, shi kuma Abbas ba yadda ban yi da shi ba dan ya ƙara aure ya ji daɗin aure amma yaki, shi sam ba aure ya yi ba, dan idan baka haɗa mata biyu a gida suna nuna kishi karara kamar dai matan Zuhair suna faɗa a kanka ba to ba aure ka yi ba, ku ta yi abinku shi ne dai'dai, wadda ta fi sanin kan duniya ta kwace Zuhair ɗin ya tattare a wajenta". Sai sababi take yi.

(Jama'a kun ji mun wannan tsohuwa da bala'i 🤔 ita fa har dattijon arzikinta wato mijinta King Abdul Malik ya kwanta dama ita kaɗai ce matarsa, bata da kishiya, amma take cewa uncle Abbas ya karo aure, Akka sam bata son zama lafiya, ga rikicin tsufa, mata suna faɗa tana kara hura wuta 😅)

Jin motsinta tana surfa wannan uban sababin yasa Jawad yaja hannun Chuchun da sauri suka haura izuwa master room na King, domin idan ya bari Akka ta kama shi da Chuchu a ɗan wannan lungu to fa ya shiga uku, ai ta rinƙa takurawa rayuwarsa kenan, idan ma bata ce zai lalata mata jika ba, dama kun san ba shiri suke yi ba, kullum cikin faɗa da samun saɓani suke, kuma idan baku manta ba Akkar ta sha shiga tsakaninsa da Chuchun tana rabasu faɗa, so tasan basa shiri sam sam, yanzu kwatsam ta gansu a tare a wannan ɗan hanya na zuwa master room ai shikenan ya shiga uku a cikin wanna kingdom ɗin, ba zata barshi ya zauna lafiya ba, kuma abin da yake gudu na kada Jaish ya san halin da ake ciki na tsakaninsa da Chuchun fa to sai ya sani idan Akka ta gansu, bugu da kari Mammiensa ma sai ta sani, kuma ɓoye mata yake yi dan yasan bata son alƙarsa da ƴaƴan King Zuhair, shi kuma a part ɗin ya taso ya girma, ya fi sabawa da su fiye da ƴan uwansa su Sarina ɗin ma, amma bai san dalilin Mammaien ɗin tasa na bata son taga yana alaƙa da ƴan uwan nasa ba, jini ɗaya suke amma tana son raba jini da karfi da yaji.

Kai tsaye room na King suka nufa da gudu, wajen hawa ƴan ƙananan stage da suke a bakin kofar room ɗin na King Chuchu ta yi tuntuɓe ta faɗi, gudun da suke yi ne yasa bata lura da sun iso wajen ba.

Cak Yah Jawad ya ɗauketa suka ƙarisa shiga room ɗin. A lokacin da suka shigo kuma King yana wanka, bai jima da dawowa daga masallacin jumma'ar ba, so shi dama kayansa na zuwa masallaci daban suke da sauran kayansa, saboda daraja da girma da yake bawa ranar, a ranar kwalliya na musamman yake yi, saboda jumma'a babbar rana ce, kayan zuwa masallacin nasa ma na musamman ɗin na musamman ne, idan ya dawo daga masallacin kuma yana yin wanka ya canzasu izuwa wasu na musamman ɗin dan komawa fada ya zauna zuwa yamma irin karfe 5 ɗin nan bayan sallar la'asar kenan, sai a fita yin wannan gasa tasu da suke yi.

Coz yau ba zuwa fada zai yi ba, saboda abin da yake faruwa da Mama, yanzu haka idan ya yi wanka ya shirya wajen Mamar zai wuce, domin idan bai yi haka ba sai ta ce bai yi mata adalci ba, idan Momma bata da lafiya ko Dubai ta koma can yake tarewa, kunga kuwa idan yana son zaman lafiya dole ya zauna kusa da Mamar ma, idan ba haka ba a tashi gidan gabaɗaya da ruwan bala'i......... 😅

Akka dai ta ce idan basu yi haka ba to ba mata Zuhair ya aura ba, da alama fa Akka tana jin daÉ—in wannan diramar tasu, suna É—ebe mata kewa.

Ganin cewa King na cikin toilet yana wanka, ga kuma Akka a bayansu tana zuwa yasa Yah Jawad ɗin ya sauketa a tsakiyar room ɗin saman shinfiɗar tsakiyar ɗakin, sannan ya riƙo hannunta da sauri suka faɗa cikin dressing room na King. A bayan wajen glass na jera watch ɗinsa suka tsaya suna mayar da numfashi.........

Akka kuwa cikin room É—in ta shigo tare da zama saman shinfiÉ—ar King É—in in da yake zama ya huta. A nan ta zauna tana jiran É—an nata ya fito daga wanka, da alama su Momma sun bakanta mata rai ne yasa ta nufo wajen King dan su yi magana, har ta zauna saman wannan sofa da aka kawata da shinfiÉ—u na alfarma na gashin jimina bata dai'na zance su Momma ba, sai sababi take yi, aikuwa Allah ya rufawa Yah Jawad asiri, dan a yadda take kan tsini tana surfa sababin nan ta gansu shi da Chuchun a yadda suke É—in nan ai shikenan rayuwarsa tana kwale kwale, dan ya shiga talatin ma ba uku ba.

Ni kam na ce to su yanzu da suka shigarwa King cikin dressing room ɗinsa ku gaya mun idan ya fito daga wanka zai sanya kaya ya kenan?.🤔 Ya zasu yi idan zai shigo sanya kayansa?🤔 Ga dai Akka a cikin ɗakin, King kuma zai shigo nan, my people's kuna ganin a gudun nan da suka yi sun tsira kuwa?🤔 To ni dai bari na leƙa Daular Abu Abdussalam wato Dubai in dawo, sai naga zasu tsira ne ko asirinsu zai tonu.

Abu Abdussalam empire🤍🔥

LEESHARH....✍️💘

A hankali ta É—an waro idanun nata waje, from down ta fara kallonsa, a maimakon ta É—aga idanu ta kalli face É—insa, sai ta fara kallon kafafunsa da suke sanye cikin cover shoe masu kyau da tsada launin baki. In a slow ta fara É—aga idanunta tana binsa da kallon from down É—in har up.
Chapter 156 · 0% Book details