← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 180

Sashe 135

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumgumeta ya yi shima yana murmushi mai ƙayatarwa, alamar suna cikin tsantsar farinciki da ganin juna.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/8/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________40🔥

Rumgumeta ya yi shima yana murmushi mai ƙayatarwa, alamar suna cikin tsantsar farinciki da ganin juna.

Ruwan sama ne mai karfin gaske ya kece kamar da bakin kwarya. A É—ari ta sake shi tana faÉ—in. "Kamran mu gudu cikin raminmu ruwan sama".

Hannunta ya riƙo shi ma yana faɗin. "Me ruwan saman zai yi maki sarkin tsoro? Babu komai, zu mu zauna a saman dutsen nan kina mana busa ruwa na jiƙamu".

ÆŠan turo baki ta yi. "Kamran akwai sanyi fa ruwan".

Jan hannunta ya yi suka koma saman dutsen suka zauna. "Ai haka kike so, shi ma ruwan ƙoramar da kike shiga kullum ai akwai sanyi".

Kwantar da kanta a saman shoulder É—insa ta yi tana faÉ—in. "Not like rain, shi sanyinsa daban ne, but is so sweet kuma fa".

Tafukan hannunsa ya buÉ—e ruwan na zuba a samansu. "The water is so very very fresh and cool". Ya yi maganar yana É—an watsa mata shi a saman face É—inta.

Jinjina mashi kai ta yi. "Yah ikon Allah kenan, ko iya ruwan saman nan idan ka kallah ya isa ya sanyaka ka kara jin tsoron Allah, ka kara ganin girman Allah, Allah buwayi gagara misali, yanzu idan ka É—aga kanka ka dubi sararin samaniya sai ka rasa ta ina ruwan yake fitowa, hmmmm wani abin sai Ubangiji, yanzu fa a saman nan akwai ruwan da zai iya cinye duniya da abin da yake a cikinta, kaf duniya babu wanda ya isa ya tare ruwa kada ya wuce idan ya doso waje, amma shi Ubangiji ya rike ruwan da zata iya cinye duniyar nan tas ba tare da ta zubo ta cinye duniyar ba, kai komai ma fa ka gani a duniyar nan idan kana da hankali ya isa yasaka ka kara jin tsoron Allah!!".

Yadda ta yi maganar kamar wata babbar mace, ta kwantar da kanta shiru tana zayyano bayanai cikin natsuwa, ruwan saman na sauka a kansu, abin sai ya ƙayatar da masu kallon.

"Pretty ina son sanin wanene Allah? And ina son samun karin sani sosai a kan abubuwan da kuke yi keda Sweetie". Ya yi maganar tare da juyowa da kallonsa izuwa saman face É—inta.

"Kamran Allah shi ne wanda ya halicceni ya kuma halicceka tare da sauran mutanen da kake gani suna giftawa a cikin dajin nan, sannan ya halicci sammai da ƙassai, halittun Ubangiji ba zasu kirgu ba, dan sun wuce gaban tunanin kowa".

Juyowa da kyau ya yi ta yadda zai sami damar ganinta da kyau da kyau. "To meyasa Ubangiji ya haliccemu kenan?".

"Bauta, domin mu bauta mashi, kuma sallah da ka tambayeni a kan mecece ita ranar da kasame ni ina yinta to ɗaya ce daga cikin abin da Ubangiji ya haliccemu muzo mu yi mashi, kuma ita ce ma a kan gaba, sai karatun Alkur'ani mai girma, ita ce littafin nan da ka ɗauka a wajenmu ranar, akwai azumi da sauransu, amma ni dai bana yin azumi gaskiya, ba zan iya yunwar nan ba, Sweetie ce kawai take yi, ni kam wlh dana ji yunwa zan ci abinci na, so ban taɓa yin azumi ba". (Sarkin cin abinci ba, yo dama ke a yanzu ai ba zaki iya yi ba, wata kila idan ya zama wajibi a kanki kyayi dan dole😅)

"E ina karanta littafin dana ɗauka a wajenku, kuma yana da matuƙar daɗi sosai, sai dai ban yi nisa a karatun ba, wannan littafin ma yana ɗaya daga cikin abin da ya hanani karanta diaryn da mummynku ta bani, wannan Alqur'anin ya ja ra'ayina sosai, ya ɗauke mun hankali da a kullum a ƙagare nake dana karanta shi".

Murmushin ta sakar mashi tare da kai hannunta ta ja karar dogon hancin nan nasa. "Ka yi ƙoƙari ka karanta zaka ji daɗinsa, aduniya babu abin da ya kaisa daɗin karantawa da kuma sauraran mai karantawa".

Shafa kumatunta ya yi kafin ya ce. "To É—an karanta mun kaÉ—an na ji". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa a cikin gashin kanta dake ta zubar da ruwa sosai, ga hadari sai kara haÉ—uwa yake yi, ruwan sama yana kara tsananta karfin zubarsa kamar da bakin kwarya, ga walkiya mai hasken gaske da yake haske arear wajen a duk lokacin daya wanzu a sararin samaniyar, sai tsawa ya biyo baya. Hankalinsu a kwance suke zaune a wajen abinsu, ko kaÉ—an basu damu da ruwan da yake zuba masu a kansu ba.

Rera mashi karatun Alqur'ani mai girma ta fara yi cikin suratul iklas, ga voice É—in nata da zaki ga shegen daÉ—i. Shiru ya saurara yana jinta, har wani irin ni'imantaccen ajiyar zuciya ya sauke, Alqur'ani akwai daÉ—in saurara, ga kwantar da hankalin mai sauraro.

Ƙarar da suka fara jiyowa daga can nesa da su ne yasa Pretty ta dakata da karatun, a lokacin already ta kammala suratul iklas ta shiga falak, dan ƙasa ta yo. Dakatawa da yin karatun ta yi tana zaro idanun nan nata da suke kara fito da tsantsar kyanta.

"Kamran menene yake kara har haka?". A tsorace ta yi maganar.

"I don't know, amma mu je mu duba mana mu gani". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta, shi fa ko tsoro baya ji, wai su je su duba, ita dai Sweetie baiwar Allah tana ciki abinta, ba ruwanta da yawace yawace har sai idan ya zama dole.

"Kamran ina tsoro fa". Ta faɗa tana ƙanƙame hannunsa tare da kara zaro idanu.

Sauƙowa ƙasa daga saman dutsen ya yi tare da juya mata faffaɗar bayansa a kan ta hau ya goyata yana faɗin. "Kada ki ji tsoron komai my Pretty, ina tare dake, mu je muga menene yake kara har haka?".

Ba musu ta haye bayan nasa tana murmushi, idan da sabo ai ya saba goyonta, dan haka sai ta ɗale abinta tare da saƙalo wuyarsa ta kwantar da kanta a gefen shoulder ɗinsa, sai murmushi take saki dimple ɗinta na lotsawa, ga ruwa na zuba mata daga tsakiyar kai, kyalkyawar gashin kanta sai zubar da ruwa yake yi.

Kai tsaye Kamran ya nufi ta wajen da suke jiyo wannan kara a tare da ita. Sai hira suke yi gwanin birgewa har suna É—an yi nisa. Suna tafiya suna kara jiyo wannan sauti tana kara matsowa kuma tana kara karfin kara.

Sai da suka sake matsawa kusa sosai suka fahimci ashe sautin ƙugin igiyar ruwace mai karfin gaske ne, da alama katafaren teku ce a wajen wadda ta cika take ambaliya sanadiyar wannan ruwan saman, igiyar ruwace ke ƙugi.

A hanzarce ya ƙarisa matsowa sosai, babu ko shakka bare tsoro ya nufi waje. Wannan katafaren tekun nan wanda mum ɗinsu ta faɗo daga ɗaya daga cikin duwatsun dake kewaye da tekun nan ne, sai dai a yanzu iya gane daga ta ina mum ɗin nasu ta fito har ta faɗo ta wannan waje abu ne da ba zai yi wu ba, su bama su san daga ta wajen ta fito ba, so sai basu wani damu ba. Mamaki ne kawai ya bayyana a saman fuskokinsu na ganin tekun a dajin bai sani ba.

Duk zaman Kamran a wannan daji bai taɓa sanin wannan teku ba, sai dai kananan ruwa dake ta wajen tsauninsu, ashe akwai teku mai girman da idan ka bi cikinta zaka je ƙasashe da dama.

"Kamran saukeni na ga tekun nan da kyau". Ta faɗa tana zaro idan, yadda igiyar ruwa ke juya tsakiyar ruwan tekun kawai take kallo. Shi ma Kamran ɗin abin da yake gani kenan, abin ya ƙayatar da su kuma ya basu mamaki sosai. Ba musu ya sauketa dan ta yi kallo da kyau.

"Pretty ina ganin kamar wannan teku ta nan ce hanyar fita daga cikin wannan Forest É—in ko?".

Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kanta, ya jima yana neman hanyar da zata fitar da shi wannan Forest ɗin cikin sauki, ita kuma wannan teku abin da bai sani ba ta kasance kamar border ce, iya kar ƙasashe da damane a wajen, sai dai tabbas ita ce hanyar da zata iya kaisu cikin babbar ƙasar, kuma dai kada ku manta su su Pretty ta nan mum ɗinsu ta fito, kunga hakan na nufin koma dai me ta nan garinsu or ƙasarsu yake. Akwai cakwakiya kenan, da alama su Pretty zasu kai kansu in da ake nemansu ruwan ajallo idan suka yi wasa.

Sai hira suke yi suna ta kallon yadda igiyar ruwa yake jan ruwan har sama sai kuma ya sake sake shi, hakan yakansa ruwan ta bada sauti mai karfin da har suka iya jiyowa ɗazun, sai zancen neman hanya suke yi, Kamran ya kafe a kan shi dai lallai wannan teku a akwai hanya a kusa da ita, ita kuma Pretty ta ce bata ga alama ba, domin kuwa ita dai ruwa take kallo maras iyaka, kuma wlh ita ko kasheta za'ayi bafa zata shiga cikin ruwan nan ba........😅

(Kunga laifinta? Da gaskiyar ruwa ba iyaka haka ace su shiga su ketare?🤔 Ni dai ina bayanta, ko za'a kwasheta kada ta yarda ta shiga😅 ta bar Kamran da Sweetie su je, idan suka isko mutane sai azo da jirgin ruwa a ɗauketa😅😅 saura naji wata magana, shawara na bata🥱😎)

Sun jima tsaye a wajen ruwan sama na jiƙasu, sai da Pretty ta fara rawan sanyi ne ta dube shi. "Kamran sanyi nake ji sosai".

Juyowa ya yi da kallonsa a kanta. "Zo na goyaki mu koma, gobe dole mu dawo wannan waje".

Da sauri ta faÉ—a jikinsa, sai rawan sanyi take yi sosai, shi ma dai zubar ruwa yake yi.
Chapter 135 · 0% Book details