← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 180

Sashe 122

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________36🔥

Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa.

Ita kuwa gabansa ta nufo, sam bata tuna komai ba. A É—an nesa da shi kaÉ—an ta tsaya tare da cewa. "Yah Jawad gani nan".

Tamkar bai san da shigowarta room ɗin ba, aikin gabansa kawai ya cigaba da yi, sai dai kuma a zahirin gaskiya ya kasa yin aikin dai'dai saboda ɓacin rai, hankalinsa kuma yana kanta, tunanin kalar hukuncin da zai yi mata kawai yake yi.

Ta jima a tsaye a wajen almost 10 mins bai ko É—aga idanu ya kalleta ba, aikinsa kawai yake yi na latsa laptop É—in buge dan kada ta gane hankalinsa baya a kan aikin.

"Yah Jawad in ta fi ne?". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, saboda ta gaji da tsayuwa, ta ga bashi da niyar kulata, kuma yau ta sha alwashin wlh ba zata tsaya a cuceta ba, idan ya ce ta yi kneel down ko makamancin haka to wlh guduwa wajen Akka zata yi, sai dai ya bita can ya kakkaryata idan yana so...... Lallai Chuchu ta fara girma, abin ya fara kureta........😅

Sai da suka kara good 5 mins a haka kafin nan ya É—an ture laptop É—in daga gabansa izuwa gefensa, ba tare da ya É—ago ya kalli in da take ba ya ce. "Zo nan ki yi mun kneel down, domin yau sai na koya maki hankali sosai, ke kunnanki baya jin magana ko Jannat? To yau zai fara jin magana dole........"

Bai gama rufe baki ba ta watsa a guje zata nufi waje, dama ta ce wlh ba wani hukuncinsa da zata karɓa yau, yana yin yunkurin hukuntata zata gudu, aikuwa sai ga shi ta ruga a guje zata yi waje.

Wani irin miƙewa ya yi babu shiri, dan yasan idan ya barta ta gudu ya shiga tara da Akka na farko, na biyu kuma bai ga dalilin da zai sanya yana yi mata magana zata gudu ba, a cikin kannen nasu ma fa ita da auta sune kanana, amma tsabar ta rai'na shi ne yana magana zata gudu? Lallai yau dole ta ci duka, ba ma zai yiwu ya barta ta gudu ba ai, dole ya kamota ta karɓi hukuncin dama bai taɓa yi ma kowa daga cikin kannen nasu ba, ko Sarina da take sarkin rashin ji yau hukuncin da zai yi wa Chuchu bai taɓa yi wa Sarina ɗin ba, sannan ya ja mata kunne a kan idan ta gayawa Akka ko uncles Abbas sai ya karairayata........ (Ku ji mun mugunta, a dakeka a hanaka kuka, ya azabtar da ita kuma ya ce kada ta gayawa kowa🤔 Allah Yah Jawad ma mugu ne)

Bata kai ga isa kofar É—akin ba ya damkota ta baya, duk da tasan cewa ko ta yi ihu babu wanda zai iya jinta a cikin gidan, saboda ainahin kofar shiga part É—in nasa ma a rufe, tana shiga kofar ta rufe, ga shi izuwa yanzu tasan kowa ya rufe kofofin part É—insa, koda bama haka ba yanayin tsarin ginin gidan mawuyacin abu ne tana cikin wani part ta yi ihu a jita a wajen, hakan ba zai yi ba.

Amma duk da haka hakan bai hana ta waje baki zata kurma mashi ihu ba, domin ta tsarorata da kamota da ya yi, bata yi tsammanin zai yi yunƙurin bin bayanta har ma ya kamata ba, ta yi tunanin zata iya tsira ne ma yasa ta fara gudun, tasan ba komai yake kulawa ba, so a tunaninta idan ta gudu ma zai kyaleta ya ce wata kila da safe zai kamata, amma sai ta ji an damkota ta baya, shi ne abin ya razanata da har yasa ta waje baki da karfin gaske zata zunduma ihu, ga tsoron kalar hukuncin da zai yi mata, yanzu ma bata gudu ba ma ya ce ta yi kneel down bare kuma ya ce ta yi ta ki yi zata gudu? Ai ita da kanta tasan hukunci ya karu sosai!.

Ina duk da yasan ba wani jin ihun nata family zasu yi ba, amma bai bari ta yi shi ba, tana waje ɗan bakin yasa hannu ya toshe mata bakin nata, ransa ya sosu matuƙa, duk cikin sisters ɗinsu babu wanda ya taɓa yi mashi makamancin abin da ta yi mashi, bai san cewa idan ka cina takurawa mutun dama ya kansa ya rage tsoronka idan ma yana ji ba, takura mata da yake yi ne yasa ta rage jin tsoronsa da har ma take kiransa da mugu, yanzu da Yah Jaish ne ya kirata ai ko yankata yake yi ba zata tsallake abin da ya ce ba, saboda me? Saboda da ni da ku dukka mun san Yah Jaish dai ba wanda ya ishe shi kallo a cikin kannen nasa, baya kulasu kuma baya bi da kansu, kunga kuwa dole a ji shakkarsa sosai, shi ma dai Yah Jawad ɗin chuchu kawai ya sakawa ido, kuma dani da ku duk mun san dalilinsa na yin hakan.

"Stay quiet, if not a cikin daren nan zan kakkaryaki na zubar da kasusuwanki a dustbin". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar, ya kuma kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga saman ɗan bakin nata.

Wani irin kermar tsoro jikinta ya fara yi, danasanin abin da ta aikata ta fara yi, yau dai ta shiga uku ta lalace, haka take ta faÉ—i a cikin ranta.

Saketa ya yi tare da juyo da ita suna fuskantar juna, sannan ya kai hannunsa ya damko wannan arab hair É—in nata, saboda hular kanta ya cire tun lokacin da ta watsa a guje zata yi waje, so sai ya zamana babu É—ankwali a kan nata, hakan ya bashi damar damko mata kyakkyawar gashinta da ta É—aure shi kashi biyu.

Da karfi ya danki gashin nata tare da jan shi baya sosai, hakan yasa dan dole babu shiri sai da ta É—ago kanta sama, wani irin azaba ne ta ji ya ziyarceta lokaci guda.

"Kin girma ko Jannat? Har inai maki magana zaki gudu ko?".

Kai ta fara girgiza mashi ba bakin yin magana, sai wasu zafafan hawayen azaba da suka cika mata idanu, kan ka ce me sun fara wanke mata fuska, amma fa a cikin ranta faÉ—i take yi wlh yana sakinta sai ta sake watsawa a guje, kuma yau ba sai gobe ba sai ta gayawa uncle Abbas muguntar da yake yi masu ita da su Sarina, sannan zata gayawa Akka da daddy, wlh ba zata hakura da kudurinta na gaya masu ba, ko dan su samu sassauci a kan irin cin zalinsu da yake yi, duk sai ta ji ta kara tsanarsa sosai.

"Zaki yi mun shiru ne ko sai na É—auko belt?". Ya yi maganar yana kai kallonsa izuwa saman bed É—insa, wayarsa ce take kara alamar shigowar kira.

Kara jan mata gashi baya ya yi da ƙarfi, tare da dawo da kallonsa a kanta. Ba komai ne yake kona mashi rai ba face fitowa da kayan barci da ta yi, kishi ne kawai yake cinsa a zuciya yasa yake azabtar da ita har haka. Izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci cewa tabbas uncle Abbas gaskiya yake gaya mashi na cewa yana son Jannat, domin kuwa idan har baya sonta ba zai yi kishinta har haka ba, wannan kishi ya wuce na yaya da kanwa sai dai mata da miji, kuma ba zai rinƙa damuwa da son ya ganta har haka ba, yanzu da yasa auta ta kirata a fili idan ta zo dama wayarta zai bata, a zahirin abin da yake cikin zuciyarsa kuma ba wayar yake son bata ba, ganinta yake son yi, dan yana kewarta, shi ne gaskiya!!.

Amma kuma shi fa wai a haka so yake ya cire son nata a ransa, saboda a cewarsa ita ɗin sistersa ce kawai, kuma ta yi ƙanƙantar da zai iya cewa yana so, bugu da kari ba zai iya jawa kansa rai'ni na cewa zai aureta ba, idan ya yi haka ai yagama da kansa, ya jawa kansa rai'ni, shi ne yasa tun farko yake kaucewa yaki yarda da cewa yana sonta, dan bai son rai'ni, yanzu kuma da ya fahimci hakan yake ƙoƙarin cire son nata a ransa. Akwai cakwakiya ga Mammie ɗinsa ma kun dai ji bata kaunar wannan haɗin, uncle Abbas kuma fatansa kenan, wai ma to meyasa Mammien bata son haɗin Jawad ɗin da Chuchun? Akwai dai wata a ƙasa gaskiya.

Kasa iya yi mashi shirun ta yi, sai ma kara karfin gudu hawayen nata suka yi, sakamakon ya kara ja mata gashi kanta baya, zafi ya karu, dan haka ita ma sai ta kara kukan nata. Har cikin ransa yake jin zafin wannan kuka da take yi kamar yadda ita kuma take jin zafin jan mata gashin da yake yi. Ya yi iya kar yinsa, ya yi mata iya barazanar da zai yi mata akan ta yi shiru amma taki, bashi da zaɓin da ya wuce ya sakin mata gashi idan har yana son ta yi shiru, zuciyarsa ba zata iya jurar ganin kukan nata ba, dan haka sai ya zame hannunsa daga kan nata tare da gyara tsayuwarsa da nufin ya fara magana, ya gaya mata kalar hukuncin da zai yi mata a yau, dan ba zai barta ba.

Ai kuwa yana saketa ta sake watsawa a guje ta nufi waje. Ba shiri ya sake rufa mata baya a karo na biyu. Tana fitowa parlourn ya damkota, da hannu É—aya ya É—agata sama, É—ayan hannunsa kuma yasa ya toshe mata baki saboda waje bakin da ta yi zata zunduma mashi ihu.
Chapter 122 · 0% Book details