Sashe 140
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hmmmm kawai Jaish ya ce mashi. A hanzarce ya katse kiran, a cewarsa ko hauka yake yi ba zai bari Jaish ya gano cewa yana son chuchu ba, dan ba zasu wanye lafiya ba, Jaish ɗin zai ce shikenan ya gama ja masu raini a idanun kannensu, ya gama zubar masu da mutunci, ya gama da su, ba karamar dirama zasu yi ba, dan wlh Jaish ba zai yarda ba, bare ma shi da ba sanin darajar soyayyar ya yi ba, ba yinta yake yi ba, bai taɓa yi ba bare yasan zafinta ko sanyinta, ai kunga ba zai ɗauketa da mahimmanci ba, zai ce Jawad ya haukace, ina ai bama zai yarda ba, Jawad ɗin yasan da hakan shiyasa yake ɓoye mashi, kuma shi ma Jawad ɗin a rashin sa'arsa da ya tashi ɓoye abin sai ya ɓoyewa har da ita Chuchun, a cewarsa yanzu ta yi karama, idan ya gaya mata cewa yana sonta na farko zata rai'na shi, na biyu kuma a gaskiya ta yi ƙanƙanta da batun soyayya, karatu yake son ta yi, shiyasa ya barta a duhu bai sanar da ita ba, ya dai ce zai koyawa kansa shakuwa da ita, zai na sakar mata fuska su saba, amma banda zancen soyayya, dan a ganinsa tana jin cewa yana sonta shikenan ta rai'na shi. Tashin sense!. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, da alama Rizwan zai riga shi bayyana mata soyayyarsa, ita kuma dai kunga bata taɓa yin soyayya ba bare ta ce akwai son wani a ranta, so a yadda take a yanzu duk wanda ya ce yana sonta daga cikin ƴan uwanta zata iya amince mashi, bare kuma a yadda suke son juna dukkansu, babu nuna banbanci a tsakani.
(Yah Jawad yana ruwa kusa da.....🥱🤔 Akka😅ðŸ¤)
Tuki yake yi yana kallonta ta wutsiyar idanunsa, wannan kwalliya tata ta tafi da imaninsa sosai da sosai. Ita kuma sai kallon hanya suke yi ita da auta, suna farinciki yau dai ga su a wajen Kingdom, kamar bakinsu ba zai rufu ba.
Kai tsaye wani haɗaɗɗen wajen da suke yawan zuwa shi da Jaish su zauna su huta idan pressure ya yi masu yawa a kai ya nufa da su, idan sun tarawa kansu aiki ko kuma Jaish yana son su tattauna ba'a office ɗinsu ba kuma ba'a gida ba, sai su zo wannan wajen hutawar mai cike da kayan alatu su zauna su yi duk tattaunawar da za su yi cikin sirri. Jaish ɗan jarida ne babba, so ba kamar Jawad yake ba, kwakwalwarsa kullum tana cikin aikin ƙaƙale ƙaƙale, shiyasa yake son keɓewa shi kaɗai dan ya rinƙa zurfafa tunaninsa tare da faɗaɗata. Shi kuwa Jawad ai kunga har lokacin soyayya yake da shi abinsa.
"Yah Jawad ka kaimu zoo mu kalli namun dawa, daga nan ka kaimu wajajen wasanni mu É—an yi wasa". Cewar Chuchu.
ÆŠaga mata gera guda ya yi kafin ya ce. "Jannat har yanzu baki yi girma da zuwa wajen wasanni ba ko?". Ya yi maganar yana zama a É—aya daga cikin tsala tsalar sofas dake part na musamman a wajen, part ne na musamman wanda sai wane da wane suke zuwa wajen, babu hayaniya sam sam a wajen.
"Kai Yah Jawad to duka duka shekaruna nawa? Ko sha shidda fa ban kai ba". Ta faÉ—a tana turo baki.
Auta ce ta ce. "Yah Jawad tun da yau mun fito ka kaimu har da gidan kallo mu kalli Film".
Girgiza kai ya yi, kwata kwata su auta basu da wata matsala a rayuwarsu, wai gidan kallo, su dai tun da yau sun fito shikenan kuma, sai abin da Allah ya yi, akuyar É—aure an samu sake.
"Zaku ci abinci a waje yau?". Ya tambayesu yana kallon face É—in chuchu.
Har suna haɗa baki wajen amsawa da e zasu ci, basu taɓa cin abincin waje ba.
Bai sake yi masu magana ba ya buga masu oder kawai, a kawo masu kayan cima da abinci mafi tsada a wajen. Ba'a ɓata lokaci ba aka kawo masu.
"Bismillah ku ci abincin waje yau ku ji ya take". Ya faÉ—a yana ciro wayarsa, sai kuma ya kawar da kallonsa daga kansu, dan ba zai so ganin yadda za su yi da fuska ba, sai É—auki su kuma suke yi yau dai za'a ci abincin waje.
Chuchu ce ta fara É—aukar spoon ta É—ebo madbe dake a saman plate na gabanta. Madbe ba sabon abinci bane a wajensu, amma yau ji suke yi kamar sabon abu aka kawo masu, saboda na waje ne ba su kuyanga Zubaida ne suka haÉ—a ba.
Fuska a ɗauke da murmushi ta kai shi bakinta, ta zuba ta fara tauna. Nan take ta kwaɓe fuska kamar wadda ta tauna wani abin mai ɗaci.
A hanzarce ta tufo shi waje tana kara kwaɓe fuska. Dariya ne ya so kubce wa Yah Jawad ɗin, dama yasan za'ayi hakan shiyasa ma ya kawar da kansa, ba zai so ganin sauyawar fuskar masoyiyarsa daga murmushi zuwa ƙunci ba.
"Aunty Chuchu what happened naga kin fito da abincin?". Cewar auta.
"Isn't sweet at all auta, like coffee and salt".
Ai kuwa Jawad bai san lokacin da dariyar da yake ɓoyewa ta kubce mashi ba, bama abin da ya bashi dariya kamar yadda ta ce wai kamar coffee da gishiri, innalillahi Chuchu anji ɗanɗano kam tab.
Ganin yana yi masu dariya ne yasa Chuchu ta gane da gangan ya yi masu hakan, kenan yasan É—anÉ—anon babu daÉ—i ya barsu suka ci? Har da wani É—aukinsu zasu ci wani abinci na daban bana kingdom ba. Hakan yasa Chuchun ta fashe da kuka mai sauti, ta ji haushin dariyar da yake yi masu.
Ita kam auta mamakin ganinsa yana dariya ya sa ta ƙasa iya yin magana, ta dai san yana ɗan yin murmushi time to time, amma dariya mai sauti haka bata taɓa ganinsa yana yi ba sai yau.
Ita kuwa Chuchu zagewa ta yi da gaske tana kuka har da hawaye. Ganin hakan yasa ya dakatar da yin dariyar tasa, sannan ya fara ƙoƙarin rarrashinta.
Ƙin yin shiru ta yi, ta cigaba da yin kukanta. Da yaga da gaske fa take kukan sai ya miƙe ya dawo saman nasu sofan, dama su sun zauna ne a mai zaman mutun uku, shi kuma ya zauna a mai zaman mutun biyu, so sai ya miƙe ya dawo kusa da ita.
ÆŠan rungumota ya yi yana faÉ—in. "Sorry my sister, tuba nake yi, kuma ai dama ba laifina bane, da nace maku babu daÉ—i kada ku ci ai da zaku ce na hanaku, kuma nasan halinku sarai zaku yi ta jin haushi na, amma kuma dana barku kuka É—anÉ—ana ai kunji da kanku ko?".
Cikin kuka ta ce. "To Yah Jawad meyasa zaka yi mun dariya?".
"To na tuba, ba zan sake ba". Yana magana yana ƙoƙarin goge mata hawaye, ita dai auta da Allah ya rufa mata asiri bata ɗanɗana ba lafiya lou ɗanɗanon bakinta yake.
"Yanzu ga shi ɗanɗanon bakina ya ɓaci". Ta faɗa tana fito da harshe domun ta goge harshen nata.
Sake guntse dariyar ya yi. (Ni ina tantanma ma, anya da ya tashi buga oder nan bai ce a ɓata abincin Chuchu ba kuwa?🤔 Dan wannan dariyar dai na mugunta yake yi, da biyu gaskiya, da gangan ya yi mata hakan.)
Hannu ya kai yana tayata goge É—an harshen nata yana faÉ—in. "Bari ma na tayaki gogewa". Yana magana yana guntse dariya.
Kome auta ta tuna sai ita ma ta kwashe da dariya kamar wadda aka tsikara.
"Me kike dariya ke kuma?". Chuchu ta tambayeta.
Cike da zolaya ta ce. "Aunty Chuchu É—anÉ—ana nawa madbe É—in ki ji kamar ya fi naki daÉ—i....."
Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon harara da Yah Jawad ɗin ya wurga mata, da alama dai ya tabbata da gaske da gangan yasa aka ɓata na Chuchu dan ya tsokaneta.
"Ba zata sake É—anÉ—ana komai ba, salon É—anÉ—anon bakinta ya kara canzawa ko?" Ya tari numfashin auta da sauri, dan ma kada Chuchun ta ce zata É—anÉ—ana ta ji akwai banbanci da nata, idan ta ji hakan kuwa kuka zata sanya masu ta ce sai ta ji dalilin da yasa nata É—anÉ—anonsa daban.
Ganin irin hararar da ya yi mata ne yasa autar ta gane shi ya shirya komai, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru, amma fa a cikin zuciyarta ta ƙuduri niyar sai ta gayawa Chuchun gaskiya idan suka je gida.
Cigaba da rarrashinta ya yi, ya kuma goge mata É—an harshen nata tas, sannan ya É—auko mata ruwan da ta zuba a cup da nufin ta sha idan ta gama cin abinci, yana É—an rungume da shoulder É—inta ya kawo mata cup É—in saitin bakinta. Da sauri ta fara girgiza mashi kai tare da ce mashi ita ba zata sha ruwansu ba, kila ruwan ma sun zuba gishiri.
Dariya ne cike fal ransa, amma ya danne ya ce auta ta É—auko mashi ruwa a mota bari ya bata ta kuskure baki. Ita dai auta Æ´ar ba ruwana, koma me za'ayi sai ayi ta yi babu ruwanta.
Auta na fita ya ce. "To juyo naga harshen naki ko ya fita?"
Ba musu ta juyo suna fuskantar juna, sakin shoulder ɗin nata ya yi tare da ƙurawa face ɗinta idanu.
"Yah Jawad har sai da harshena ya yi ja fa nasani". Ta faÉ—a tana mayar da harshen nata.
Jin ya yi shiru bai amsa mata bane yasa ta ɗago dan ta kalli meyasa ya yi shirun. Tana ɗagowa suka haɗa ido. Dariya ne ya so kubce mashi, domin da suka haɗa idon sai ya tuna da lokacin da ta ɗanɗana madbe ɗin ta kwaɓe fuska.
Yankar salar lemu ya É—auko daga cikin kayan ciman da aka kawo masu ya sanya mata a É—an bakin nata yana faÉ—in. "ÆŠan kuskure baki da wannan tukun nan".
A hanzarce ta fara ƙoƙarin turo shi waje, dan a tunaninta duk kayan wajen akwai gishiri a cikinsu. Ɗan riƙo shoulder ɗin nata ya yi yana faɗin. "Kisha babu komai".
Make mashi kafaɗa ta yi tare da faɗin. "A'a Yah Jawad babu daɗi kayan waje, gaskiya ni na ƙoshi".