Sashe 175
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk magiyar da ta yi mashi ya kafe a kan lallai shi ba zai dawo ba, ta yi hakuri kawai, daga ƙarshe dai ya bata hakuri tare da kashe wayarsa ya yi switch off ɗinta mai gabaɗaya dan ma kada ta sake kiransa.
A wannan daren dai sai da barci ya kasance ɓarawo ya saci maman Zainab, nan ma har wuraren karfe 2, bakinciki da ɓacin rai ya hanata rintsawa baiwar Allah.
Washegari da safe haka ta farka idanunta a kumbure luhu luhu, saboda kuka da ta sha ga kuma rashin barci, tana farkawa ta fito kuma Hauwa ta ce lallai lallai ita zata yi masu kayan ƙarin kumallo, rai a ɓace ta ce ba zata yi ba, baban Zainab ya ce ta yi ko ranta ya ɓaci.
Danne zuciyarta ta yi ta girka ba dan ta so ba, yau dai su Khadijah basu je school ba, dan basu taho da uniform É—insu sabon gidan ba, ga shi yau jumma'a, so basu taho da uniform É—in da suke amfani da shi ranar Friday ba.
A takaice dai babu daɗi suka yi ƙarin kumallo a gidan, duk wanda ka gani ransa a cunkushe banda Hauwa da take cikin farinciki, ranta fes, sai daɗi take ji tana kuntatawa maman Zainab.
Da misalin karfe É—aya na rana tana zaune a parlour ita da su Khadija, Zainab tana kallo a Tv, Khadija kuma ta buga uban tagumi kamar yadda mamanta ta yi.
"Mama ina kawu Sadiq ne? Ba zai zo gidan nan bane?". Cewar Zainab.
Wani irin ƙululun bakinciki maman ta ji ya taso mata. "Khadija tashi ki je ɗakina ki ɗauko mun wayata bari na gwada numbersa ko yanzu kam zata shiga, tun safe nake gwadawa bata shiga".
Da to Khadija ta amsa mata.
Bata kai ga miƙewa ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito. Yana shirye cikin wata haɗaɗɗiyar shadda chocolate color, ya yi kyau sosai, da alama masallacin jumma'a zai je, ita ma Hauwa ta ci kwalliya cikin abaya brown color.
Gaisuwa Khadijah ta É—agawa baban nata, a takaice ya amsa ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya É—aga idanu ya kalleta ba. Zata wuce cikin kenan ya ce. "Khadija ki shirya Hauwa ta ce lallai yau a É—aura aurenki da Haidar bayan mun sauko sallar jumma'a, dan haka ki shirya su Maman Haidar zasu zo su É—aukeki".
Wani irin kuka Khadijan ta fashe da shi mai matuƙar tsuma zuciyar mai sauraro, da gudun gaske ta afka cikin ɗakin maman nata, wani irin jan numfashi da take yi cikin kuka sai ta baka tausayi, kamar zata haɗiyi zuciya. Da gudu Zainab ta tashi ta bi bayanta.
Ita kuwa Hauwa wani irin murmushin mugunta take ta faman saki. Miƙewa tsaye maman Zainab ta yi, cikin wata iriyar murya da ba zaka iya fassara halin da take ciki ba ta furta. "Baban Zainab kada ka yi wannan kuskuren, wlh billahi Haidar ba zai aura mun ƴa ba, kada ka bijiro da abin da zai sanyaka yin danasani, wlh a kan farincikin ƴaƴana na yarda komai ya faru, zan iya barin maka gidanka a kan wannan aure".
Hauwa ce ta ce. "To me laifi dan yarinya ta auri É—an uwanta na jini? Kyamar dangin nasa kike yi ne? Amma kuma ke kin haÉ—a jini da shi ko?......"
Cikin ɗaga murya tare da zafin rai haɗi da ɓacin rai maman Zainab ta ce. "Hauwa ban kasa dake ba, a wannan gaɓa idan kika saka mun baki a maganata zan ci uban, wlh wlh wlh idan kika sake saka baki a maganar nan babu uban da ya isa ya dakatar da ni daga sumar dake a cikin gidan nan, sai na yi maki dukan uwar ala tsine, ke sai na yi maki abin da wlh ke da kanki ba zaki iya gane kanki ba, kin san halina bani da full stop idan aka kureni, in dai ba so kike hajiya ta haifi wata Hauwar ba, ki sake saka mun baki shegiya mai kama da kazar mayu".
Juyowa ta yi ta kalli baban Zainab ɗin. "Honey ka tafi masallaci abinka, kada ka dakata kowa, idan an ɗaura auren ka kirani ka sanar da ni". Cewar Hauwa. Ta yi hakan ne kuma dan tana tsoron maman Zainab, tana tson sake yi mata magana, amma tana da bakin yin magana da baban Zainab ɗin kam ai, a ranta kuma ta ƙuduri niyar yau sai an ɗaura auren nan ko dan taga ya maman Zainab zata yi.
Kai Hauwa dai anyi sheÉ—aniya makirar mace.
Sa kai baban Zainab É—in ya yi zai wuce ya fita ba tare da ya ce da maman Zee uppan ba, ko kallon in da take ma bai yi ba.
A É—ari maman Zainab ta sha gabansa tana faÉ—in. "Kada ka haÉ—a wannan aure, zaka yi danasani".
Wani irin mari ya zabga mata wai dan ta sha gabansa, rai a ɓace ya daka mata tsawa ta bashi hanya ya wuce.
Æacin rai iya É“acin rai yau ranta ya É“aci, dama ga baÆ™incikin tafiyar Sadiq, sannan ga bakincikin da ya Æ™unsa mata da safe na sanyata ta yi girki da ya yi, ga na jiya da daddare, sai abin ya haÉ—u ya yi mata yawa, yanzu kuma ga marin da ya dalla mata, sannan ga future yarta da yake Æ™oÆ™arin lalatawa ta hanyar aura mata Haidar, ta Æ™uduri niyar ba zata bari hakan ya faru ba!!.
Hauwa dake tsaye a bayansa kaÉ—an ne ta ce. "Yes honey, wlh ka kyauta da ka mareta, kai sa'arta ne da zata tare maka gaba?".
A wani irin kaunace maman Zainab ta ɗauketa da wani irin wawan mari wadda sai da ta ga wani haske ya gifta a gabanta idanunta, yau ɓacin rai ya rufewa mmn Zee ido. Cakumo wuyar rigarta ta yi da nufin ta yi mata ɗan iskan duka. Baban Zainab bai bari hakan ta faru ba ya fara ƙoƙarin kwatarta, wasa wasa yaga idan bai saka karfi ba ba zai iya kwatarta ba.
Cikin fushi yasa kafa ya kwashe kafafunta sai ga mmn Zee a kasa rigijib, har lokacin kuma bata saki wuyar Hauwar ba, a tare suka yi ƙasar, ta ƙanƙame wuyar tata kamar mage a saman ɗan siririn reshen bishiya da idan ta sake saza faɗo, kunga dole ta ƙanƙame da kyau. To haka maman Zainab ta ƙanƙame wuyar Hauwa!.
Mari baban Zainab ɗin ya sake kai mata, daga karshe ya fara haɗa mata da duka, Hauwar ma ta fara kai mata duka domin ta kwaci kanta, ta ji shaƙa shegiya, ta ji kamshin lahira, dole ta fara kai duka dan ta samu ta tsira da ranta.
Dukan da baban Zainab yake kai mata ne ya yi mata tsananin zafin da yasa ta saki Hauwar, a guje ta miƙe ta nufi kitchen, sabuwar wuƙa ta ɗauko wadda ba'a taɓa amfani da shi ba, dan komai na cikin kitchen ɗin sabbi ne. Da gudun gaske ta yi kansu da wukar faɗi take yi yau ko sama zata haɗu da ƙasa sai ta kashe Hauwa, sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Sanin halinta da balai'n bakar zuciya yasa Hauwar ta ruga a guje ta yi É—akinta. Da mahaukacin gudu ta rufa mata ba, kamar wata mahaukaciya haka maman Zainab ta zame masu, hauka take yi masu kamar wadda take da aljanun kukar buluhi a kanta.
Da gudu baban Zainab ya bi bayansu. Ihu Hauwa ta fara yi tana kewaye É—akin dan ta ceci rayuwarta, ita kuwa maman Zainab yadda kuka san bata san menene hankali bama yau, binta take yi kawai tana faÉ—in. "Yau idan kinga baki mutu ba to ni ce nan na mutu, shegiya mugun iri, ina kika ce ke shaiÉ—aniya ce? To ki tsaya dan ubanki, yau sai dai hajiya ta haifi wata Hauwar!!"
Sai kewaye ɗakin suke yi, a hau gado a sauka, duk maman Zainab sai farfashe abubuwan cikin ɗakin take yi. A haka baban Zainab ya iskosu, da gudu ya yi ƙoƙarin shiga tsakaninsu dan ya rabasu, ai kuwa maman Zainab zata cakawa Hauwa wukar sai ta caka mashi a tsakiyar cikinsa wajen cibiya. Dama da Hauwa taga ya shigo sai ta tsaya a saman gadon, dan tasan zai tare mata, shi ne maman Zainab ta nufota da wukar, zata caka mata shi kuma ya shiga tsakani.
Nan take jininsa ya fara yin wani irin tartsatsi kamar wutar welder, ga wukar ta cakesa har can cikinsa, gabaɗaya kaifin wukar ta lume a cikin nasa. Kan kace me ya zube ƙasa a kan gadon, jini ne yake zuwa kamar an buɗewa ruwa hanya.
Wani irin mahaukacin ihu maman Zainab É—in ta saki tare da yin kansa tana kiran sunansa, ita kuwa Hauwa waje ta nufa a guje kamar mahaukaciya tana kurma nata ihun.
Da gudu su Khadija suka fito daga ɗakinsu jin irin ihun da mamansu take kurmawa, kai daga jin wannan ihu kasan bana lafiya ba, dan ihu take kurmawa tamkar maƙoshinta zai ɓalle, sai ambatar sunansa take yi.
Gwanin ban tausayi shi kuma sai shure shure yake yi kamar wadda ransa yake fita, ƙafafunsa sai kaɗawa suke yi, ko'ina na jikinsa kakkarwa yake yi, harta gashin kansa sai da suka mimmiƙe tsaye, wani irin zara zaran jijiyo ne suka fito ɓaro ɓaro a hannunsa zuwa ƙafafunsa har gaban goshinsa da kuma wajen wuyarsa, wahala ta fito da su, nan take ya yi wani irin fari kamar ba shi ba, har lokacin jini na feshi kamar wutar welder, haka zalika har lokacin yana ta shure shure, idanunsa sai juyawa sama suke yi, bakin ciki sai ƙoƙarin ɓacewa yake yi, wani irin zufa dake tsastsafo mashi yana wanke ko'ina na jikinsa sai ya baka tausayi, fuskarsa kamar an watsa mashi ruwa, ya jike sharkaf da zufa, kayan jikinsa duk sun jike da zufar azaba!!.
Ai Khadija na leƙowa taga abin da yake faruwa sai ta yi waje da gudu domin ta kira mutane su zo su taimaka masu kada babansu ya mutu, ita kuwa Zainab ta yi kansa da gudu tana ihu, Hauwa kuma sai Allah kaɗai yasan in da ta nufa...... Tashin sense!!! Akwai matsala fa my people's😥💔
Shin baban Zainab zai mutu ko zai rayu? Ina Hauwa tsohuwar makira? Ya makomar maman Zainab?.