← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 180

Sashe 125

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tsoro ne ya kamashi, yasan da cewa tabbas idan tasan da su Pretty sai ta rabasu babu makawa, shi kuma har ga Allah ba zai iya rabuwa da su ba, gara ta kashe shi kawai ta huta da ta rabasu, sun zamar mashi wani ɓari na rayuwarsa.

Har wani zufar tsoro ce take tsastsafo mashi, duk ya ruÉ—e ya rasa abin faÉ—a. Voice É—inta ne ya katse shi da cewa. "I'm waiting for your amsa ne fa Kamran".

Ɗago da idanuwansa izuwa kanta ya yi, sannan ya koma bakin bed ɗin ya zauna, ko zai mutu ba zai gaya mata ga wadda ta yi mashi wannan kitso ba, sai dai yau duk abin da zai faru ya faru. Dan haka shiru ya yi mata bai iya sake cewa ko uppan ba, yana jinta sai tambayarsa take yi, da yaga zata matsa mashi sosai ma sai ya miƙe da sauri ya nufi waje da nufin ya barmata kogon ma mai gabaɗaya.

"Where are you going?". Ta jefa mashi tambaya.

Ina ai bai tsaya ba, da sauri ya nufi waje irin shi ya yi fushin nan. Da sauri ita ma ta rufa mashi baya. Kusan a tare suka fito wajen kogon.

Damko gashin kan nasa da karfi ta yi har sai da ya furta wash. Ai kuwa yana furta wash ɗin nan Rocky da yake kwance ya yi tsalle da nufin ya haye kanta. A hanzarce ta kauce mashi, kamar dama tasan zai aikata hakan, ko da yake tasan cewa ko ita ta taɓa Kamran Rocky baya barinta, dan yafi sabawa da Kamran ɗin sama da ita, so in dai zata taɓa shi sai ya yakusheta da waɗan nan shegun faratunan hannun nasa dake fasa fatar mutun.

Ko da ta kauce mashi kuma bata saki gashin Kamran É—in ba, kaucewar da ta yi kuma yasa ta ja mashi gashin da karfi ta yadda ya sake furta wash da karfi, hakan yasa Rockyn ya sake daka tsalle ya yi kanta da karfi a karo na biyu.

A wannan karon kam dan dole ta saki Kamran ɗin tare da yin baya baya. Tana sakinsa kuma bai bi ta kanta ita da Rocky ɗin ba yasa kai ya sauka ƙasa daga saman dutsen.

Sunansa ta fara kira da karfi karfi, amma ina Kamran yaki ko juyowa ya kalleta, yasan idan ba haka ya yi mata ba ba zai rabu da ita lafiya a kan su Pretty ba, yasan yanzu idan ya nuna mata ya yi fushi ya tafi wuni zunbur bai dawo ba, to da kanta zata fita nemansa, idan kuma ta nemosa lallaɓasa zata fara yi tana rarrashinsa, daga haka zata mance da zancen kitso......... (Ashe dai Kamran ma ya iya tsiya😅)

To bari dai mu leƙa gidansu Khadija mu je mu dawo.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Lokacin shan Maltina ta yi🥱

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________37🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Duk yadda Maman Zainab ta yi tsammani abin ya wuci nan, the thing is getting out of hand, ya sha gaban tunaninta, wasa wasa dai da gaske baban Zainab ya juya mata baya, komai ya lalace mata, ga Zainab bata jin maganarta, saboda maganin Aunty Hauwa ya taɓa Zainab ɗin, amma bai taɓa Khadija ba, saboda da ni da duk mun san Khadija da Zainab akwai banbanci sosai a tsakaninsu, Zee yarinya ce, and kuma bata wani riƙo da addini kamar Khadija, bata kai Khadija ilimi ba, so ita abin ya ɗan taɓata duk da ba sosai ba, bata dai'na son mamar tata ba, amma kuma bata jin magana, ko kina yi mata magana sai ta ga damar amsawa, idan mamanta zata yi mata magana sau dubu sai lokacin da ta ga damar amsawa take amsawa, wani lokaci maman tana magana ma tana mayar mata da martani..... Abin akwai tsananin ciwo sosai.

Da farko har Sadiq ya so dukanta sosai a kan hakan, sai maman ta hana shi, dan tasan ba laifin Zee É—in bane, bama ta san tana yi ba. Duk abin da ya faru from A to Z maman Zainab ta kwashe ta gayawa Sadiq É—in, shi kansa sai da ya ji kansa ta yi wani irin sara mashi, ya jima yana guje mata irin wannan matsala, amma sam taki yarda, duk wani abin da zai gaya mata sai ta saka kafa ta shure, yanzu yadda komai ya lalace É—in nan ta ina zasu fara neman mafita ma tukun nan?.

"Ki kira mama ki gaya mata batu a kan Zainab, watakila akwai abin da zata taimaka maki da shi". Cewar Sadiq da yake tsaye a bakin kofar parlournta, ya dawo daga school ne, ya shigo kenan ya samu tana kuka, shi ne ya je jin ba'asi, a nan ne take sanar da shi ai ga abin da ya faru duka.

Haƙiƙa ya yi matuƙar tausaya mata sosai da sosai, sai dai kuma bashi da wani abin yi a yanzu face ya taya da addu'ar samun mafita.

Duk ta wani uban rame kamar ba ita ba, bata cin abinci, sai idan ta ji yunwa sosai ne zaka ganta tana shan ruwan tea, ba yadda Khadija bata yi ba wajen rarrashinta, amma ina taki ta hakura, a yanzu fa shi baban Zainab yana yin kwana uku ma bai leƙo gidan ba, to a ina yake kwana kenan? Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana.

Kasuwar ma baya wani zuwanta, ko maman Zainab ta tambayi Sadiq baban Zee ya je kasuwa, sai dai ya ce mata a'a, Sadiq ne mai kula da komai yanzu, shi kuma baban Zee sai a hankali, Æ´an kwana biyun nan ma kamar baya garin ne gabaÉ—aya, domin kuwa idan da yana garin baya kwana uku huÉ—u haka yana zuwa ya É—auki abin da ba'a rasa ba a room É—insa.

Sai dai ko ya zo gidan yadda kuka san bai taɓa sanin yana da wata mata da ƴaƴa a duniya ba, ko kallon in da suke bayayi, ko maman Zainab ta yi mashi magana tamkar da mutun mutumin da aka sassaƙa take yi ba shi ba, kamar yadda bango baya magana haka shi ma baya kulata, wannan abin shi ya fi komai ɗaga mata hankali. A kowani lokaci ta kira mamarta a waya ta sanar da ita, amsa ɗaya take bata shi ne ta cigaba da yin istigifari tana tuba har izuwa lokacin da Allah zai karɓi tubanta ya dubeta da idon rahama, kuskure dai ta rigada ta tapka shi, shirka haɗa Allah dawani ai dole taga sakayya, dan haka ta yi hakuri ta cigaba da tuba tana gayawa Allah kukanta one day one time komai zai wuce In Sha Allah.

Haƙiƙa maman Zee ta shiga tashin hankali na kin karawa, bare ma kuma idan ta tuna harda ƴarta Zainab abin ya shafa, wannan abin yana kara ɗaga mata hankali ta yadda take jin har wani juya mata duniya take yi, sannan ga batun aure Khadija da Haidar da yake ta kara matsowa, kun dai san ba fashi wannan aure, koda baban Zainab baya nan kuma baya a cikin hayyacinsa dole za'a ɗaura auren in ji hajiyarsa, saboda already anrigada an bawa Haidar ita, maman Zee dai a yanzu ita kam jira kawai take yi taga ranar da zuciyarta zai fashe ta mutu kowa ya huta, abin gwanin ban tausayi.

Ta ce da mamarta zata dawo gida da zama, maman ta ce mata a'a kamar yadda ta zauna a É—akin mijin nata ta ruguje komai ta lalata farincikinta dana Æ´aÆ´anta, hakan zata zauna a yanzu ma a buga da ita ta gyara komai kamar yadda ta lalata. Wannan dalilin yasa ta hakura ta cigaba da zama.

Tun daga ranar da abin ya faru bata sake saka Hauwa a idanunta ba, ta aika Sadiq gidan ya fi sau a kirga, amma ko ya je kullum gidan a rufe da kwaÉ—o, abin ya yi mugun É—aure mata kai, to ina Hauwa ta tafi? Tana son samun amsa, ga shi mamarta ta ce bata yafe mata ba idan har ta sake saka kafafunta ta fita waje ba tare da izinin baban Zee ba, kuma bata yafe mata ba idan ta kuskura zata fita ta yi mashi karyar ga in da zata je ta je wani wajen na daban, domin kuwa duk shi ne ya jefata cikin wannan bala'i, fita bada izininsa ba, da ya sani ai baya bari ta je ba, yanzu ga shi tana kuka tare da danasani maras amfani.

"To shikenan Sadiq, bari na kirata na gaya mata halin da ake ciki a kan Zainab É—in". Ta bashi amsa kamar zata fasa ihu, duk ta yi wani futu futu da ita yadda kuka san ba maman Zee Æ´ar kwalliyar nan ba, duk ta fice daga hayyacinta.

Khadijah na zaune a saman sofa a gefenta, ita kuma Zainab tana cikin dakin, ba kasafai ta cika fitowa ba a yanzu, duk kuma saboda wannan magani ne.

Nasiha sosai Sadiq É—in ya kara yi mata tare da haÉ—awa da Khadija da take a zaune, daga karshe ya rufe masu da cewa. "Maman Zainab dama akwai maganar da nake son mu yi dake, shi ne ma ya dawo dani ta nan, ba dan haka ba kasuwa na so wucewa tun da kinga yanzu komai ya dawo kai'na, baban Zainab baya zuwa kasuwar".

Da kyar ta iya amsa mashi da. "Ina jinka Sadiq, faÉ—i duk abin da kake so".
Chapter 125 · 0% Book details