← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 180

Sashe 144

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sweetie ma cewa ta yi. "Malam Kamran ya aka yi kasan muna nan? Sannunka da zuwa".

"Ai nasan ba zaku wuce nan É—in ba shiyasa da naje can baku nan na zo nan, ya karfin jikinki?". Ya yi maganar kamar wanda shock na wutar lantarki ta kama, ba komai yasa hakan ba kuma face wannan maciji dake ta faman harÉ—e mashi hannu da bindinsa.

"I really missed you Kamran, yanzu ma am thinking of you, na ce baka zo ba har yanzu, ashe kana hanya". Cewar Pretty.

Sweetie ce ta amsa da cewa. "Kamran yesterday bamu yi sallama ba, you just go without telling me, pretty kawai ka gayawa".

Juyowa ga Sweetien ya yi da nufin ya bata hakuri. Ihun da Pretty ta zunduma ne yasa ya dakata da yin maganar, ya manta ya juya ta kalli macijin da yake ta faman harÉ—e mashi singalalin hannunsa izuwa sama, dan macijin yana da tsawo sosai, ga jikinsa sai kyalli yake yi, bakin kirin da shi, mugun maciji kenan, kumurci da idan ya cijeka minti biyar ta yi maka yawa a duniya idan ba'a kawo agajin gaggawa ba.

Ihun da ta zunduma yasa Rocky ya ƙariso wajen da gudu. Ita kuwa ta miƙe da gudu zata bar wajen, ta ruɗar da Sweetie da ba gani take yi ba, sai faman tambayarta take yi Pretty lafiya kike ihu, amma ina ita ƙoƙarin guduwa ta bar wajen ma take yi.

Cikin hanzari ya riƙota da hannunsa ɗaya yana ƙoƙarin ya yi mata magana, ai ina wani irin ihun da ta saki sai da dajin ya amsa, kan kace me kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutar nema, akwai ta da shegen tsoro, kuma shi fa maciji kwarjini ne da shi, ba kowa yake iya kallonsa kuma ya wuni cikin walwala ba, bare kuma ace mutun yana da tsoro dama, idan ka kalle shi sau ɗaya a wuni sai ka rinƙa jin kamar fa yana nan tare da kai, koda kuwa an kashe shi a gabanka, duk sai ka ji kana takure.

Ai kuwa sume mashi a jiki ta yi. Yana ƙoƙarin sauketa ƙasa ya miƙe dan yasan ya zai yi da macijin, sai ga Rocky ya ƙariso wajen. Gabansa ya zo ya fara buɗe mashi baki a kan ya bashi kan macijin ya rike mashi sai ya zame hannunsa daga harɗe shi da macijin ya yi, da alama sun saba yin hakan. Ba musu Kamran ɗin cikin dabara ya bashi, ko tsoro bai ji ba ya warware hannunsa daga naɗin da macijin ya yi masa. Da gudu Rockyn ya bar wajen da macijin sai wintsila bindi yake yi.

Shi kuma ya kwantar da Prettyn a kasa a wajen ya miƙe tsaye ya riƙo Sweetie dake ƙoƙarin miƙewa tana ta ambatar sunan Pretty lafiya kuwa, duk ta ruɗe.

Riƙota ya yi yana faɗin ta yi shiru babu abin da ya sami ƴar uwarta, kawai ta ga maciji ne ta tsorata. Aikuwa ita ma Sweetien tana jin sunan macijin ta kara rikice mashi tana tambayarsa ina macijin yake? Ya cizan mata ƴat uwa ko? Nan take ta fara yi mashi ruwan hawaye.

Rarrashinta ya fara yi babu kakkautawa tare da gaya mata babu abin da macijin ya yi masu, sumewa kawai Prettyn ta yi. Subhanallah ai kuwa sake rikice mashi ta yi tana faÉ—in. "Na shiga uku sumewa kuma? Suma fa kanin mutuwa kenan, dan Allah Kamran ka tasan mun Æ´ar uwata kada ta mutu".

Dafe kansa ya yi yana danasanin gaya mata cewa suma ta yi, shi wlh idan abu ya rikice tsakaninsa da twin's ɗin nan suna rikita shi sosai, kusan buɗa mashi ƙwaƙwalwarsa suke yi, ba Sweetien ba ba Prettyn ba dukkansu idan abu ya rikice halinsu iri ɗaya ne.

Da kyar ya samu ta yi shiru, sannan ya zaunar da ita ya koma wajen Pretty, ɗaukarta cancak ya yi ya ƙarisa bakin ƙoramar da ita, a saman wani dutse mai ɗan faɗi ya kwantar da ita tare da sanya hannunsa ya ɗebo ruwa mai haske daga cikin ruwan dake gudu. A fuska ya shafa mata ruwan.

A haukace ta........

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________43🔥

FOREST🏞️🔥

A haukace ta farfaÉ—o tana ihun kada Kamran ya bari macijin ya kamata.

Da kyar ya samu ta nutsu ya iya gaya mata ai macijin baya nan ya tafi.

Kin yarda ta yi, ta ce ita lallai su bar wajen, ba zata sake zama a wannan wajen ba. Shiru ya É—an yi yana tunanin da bai zo ba fa idan macijin ya farga da suna wajen zai iya yi masu illah, kuma ita Pretty ita zai fara yi wa illar, dan ta fi kusa da shi, tab ai kuwa da yau dajin nan babu zaman lafiya, da kowani namun dawa sai ya san da zamansu a cikin wannan daji, dan wannan É—an bakin nata idan ta fara kurma ihu ina ga har Mamma yau sai ta jiyosu.

Ganin ya yi shiru ya afka duniyar tunani ne yasa ta miƙe da sauri tana faɗin. "Bari na je na kama hannun Sweetie mu koma, ba zamu sake zuwa wajen nan ba".

A hanzarce ya miƙe ya rufa mata baya, bai ce da ita komai ba, dan yasan ko ya ce zai yi magana ma ba zata saurare shi ba, ta rigada ta yanke hukuncin, kuma a yadda take uwar tsoron nan ai kuwa ba ita ba sake zuwa wannan waje kamar yadda ta faɗa, sai dai su sake wajen zama dan shan iska amma ba nan ba! Ta.

Tana zuwa ta riƙo hannun Sweetie tana faɗin. "Tashi mu tafi Sweetie, Allah there's snake's here, ba zamu sake zuwa ba".

Da sauri Sweetien ta miƙe tare da faɗin. "I hope snake ɗin bai yi maki komai ba?".

"Yeah bai mun komai ba, let's go kawai". Tana kai karshen maganar ta ja hannunta ta mata jagora suka nufi hanyar komawa, ko kula Kamran É—in taki yi, kamar shi ne ya kawo macijin wajen, wannan yarinya idan baka san halinta ba sai ka ce aljanu ne a kanta, wanda ya yi laifi daban, wanda kuma ake fushi da shi daban.

Bata tsaya ko'ina ba sai mazauninsu. Ciki suka shige. Bayansu ya bi, bawan Allah shi tunanin zuwa wajen wancan tekun ma yake yi, bai wani damu da kin kula shi da suka yi ba, dan in da sabo ai yasaba da halin Pretty, sai dai hakuri.

Bayan sun zauna ne shi ma ya zauna a saman dutsen da ya saba zama. Cikin sanyin murya ya ce. "Pretty zaki rakani?".

Tana ƙoƙarin kwaso kayan cimarta haɗe da su fruits da ba'a yanyanka ba, dama bata wani ci abu sosai da safen nan ba, dan tana jiran ya zo sai ta ci, idan tana kewarsa bata wani jin yunwa sosai, sai dai Sweetie ta ci abin da zata ci, ita kuma sai ta jira ya zo.

"To where?". Ta faÉ—a tana zube kayan a kusa da Sweetie dake zaune a bakin gadonsu.

"Wajen wancan teku na jiya, daga nan zamu je......". Sai kuma ya dakata da yin maganar, da ya so ne ya ce mata daga nan sai su je gonar Mamma su ciri masara da sauransu, sai ya tuna in dai ya bari Pretty ta san hanyar mazauninsu to wlh da ta ji kewarsa zata nufi wajen, idan mamma ta ganta kuma kun san me zai biyo baya, lokacin rabuwarsu ya yi kenan, kuma gonar na mamma idan baku manta ba bashi da nisa da in da ƙogonsu yake, so idan ya kuskura ya je da ita wajen tamkar ya kai ta mazauninsu ne da kansa, hakan yasa ya dakata da yin maganar bai ƙarisa ba.

Da yake ita ma ta abinci take yi bata tasa ba, sai bata wani mayar da hankalinta a kan ya dakata da yin wata magana bama, sai ta ce mashi. "Kamran I can't go anywhere today, am very scared for seeing this snake, so today am here no going out again". Tana magana tana ɓare wasu ƙosassun ayaba, sun ƙosa sosai, kuma a jikin bishiyarsu suka nuna, hakan yasa suke da zaƙi sosai, ga matuƙar kyau a ido ɓul ɓul, ai dole ne ma jikin Sweetie da Pretty ya yi kyau tamkar waɗan da suke rayuwa a cikin Ac cikin wata Daula mai girma, jikinsu luwai luwai saboda shan kayan marmari, ga su kuma ta ko'ina a cike ɓul ɓul, tsokar jikinsu masha Allah, shiyasa kullum Kamran yake karewa gurun wuyar nan nasu kallo, barema na Pretty, tsoƙar wuyar tata ya fi na Sweetie cikowa sosai, kun san fa ita dama acici ne mala'ikun tauna, bata wasa da ci, kuma a koda yaushe ka ganta sai ka ganta rike da ayaba ko lemu or kwakwa tana ɗan motsa baki, ita dai bata son zaman shiru, shiyasa ga shi nan tafi Sweetie cikowa ta ko'ina ɓul ɓul kamar wata mai shekaru 13 zuwa 14, alhalin nan ko 11 years basu cika ba.

"Haba Pretty please escort him mana". Cewar Sweetie.

Tana aikin tura ayaba a ɗan bakinta ta bata amsa da. "I can't, amma ke zaki iya miƙewa ku je ai, ni an ce maki na shirya mutuwa ba tare da na sake kallan mum ɗina bane? Ai sai mum ta dawo tukun nan koma me zai faru ya faru". Ta kai karshen maganar tare da miƙowa Kamran ɗin nonan ayaba guda ɗaya mai ɗan girman da akallah ayaba 12 ne a jikinsa.
Chapter 144 · 0% Book details