← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 180

Sashe 142

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai yi mamaki ba, dan shi fa yasan su waye su, fin haka ma zasu aikata in dai su ne.

Da lafiya ya amsa masu sannan ya É—aura da cewa. "Me yau kuma kuka aikata?".

Ajiyar zuciya suka sauke a tare, faÉ—i suke yi a cikin zuciyarsu cewa ko zamu mutu sai Yah Jaish ya É—aura mana ayar tuhuma, mu dai mun shiga uku, wai kullum mu cikin aikata abu muke yi.

A fili kuwa sai cewa suka yi. "Yah Jaish babu abin da muka aikata fa, mu fa yanzu we're so silent, innocent and babu ruwanmu da kowa".

Ita dai Momma sai murmushi take yi, dan tasan halin kayanta, tana da tabbacin sun yi wani abin kamar yadda Jaish ya zarga, baya zargi a banza ai. Kuma da gasken ne sun yi wani abin kamar yadda ya faÉ—a, mugunta suka shiryawa mama a daren yau, dan gobe zasu koma Dubai an buÉ—e school, shi ne ma yasa suka zo yin hira da mommsrsu, dan zasu koma, to tabbas sun aikata wani abin ne, shi ne dan iya shege har da wani kara nutsuwa kamar wasu limaman masallacin harami.

"Kun gama shirin ku ko?". Jaish ya tambayesu.

Har suna haÉ—a baki wajen ce mashi e sun kammala shiri.

"To ku dai tsaya ku yi karatu, kuma a duk in da kuke ku sani Allah yana ganinku idan mu bama ganinku, ku rage rashin ji, ku nutsu ku dai'na zalintar kowa, na gaji da jin sunanku a bakunan mutane, yadda kuka san ku kaɗai ne student a makarantar nan naku, ko ziyara na kai maku sauran students har tsayawa suke yi suna satar kallona, saboda yayanku ne ni, duk kun takurawa yayan mutane a makaranta, ku akwai wanda ya takura maku ne? To wlh ku nutsu, idan ba haka ba Allah next time na sake jin wani abin kun aikata, to ba makawa sai na miƙaku ga kasar Faransa ku je ku zama sojojinta na dai gaya maku, tun da ku dama wahala bata yi maku komai, kun saba da yin up and down".

Zaro idanu waje suka yi, har suna haɗa baki wajen cewa. "Allah Yah Jaish mu mun nutsu yanzu, ba zaka sake jin komai ba, mun tuba, dan Allah ka bar maganar ƙasar France ɗin nan, mu bama son ji".

"In dai baku son ji to ku nutsu, idan ba haka ba kun san dai bana magana biyu".

Omaid ne ya ce. "Ni dama can babu ruwana, Obaid ne baya ji"

(Tab wai kun ji Omaid babu ruwansa🤔 bayan kuma ya fi Obaid iya mugunta da rashin ji😅)

"Kai Omaid ni ma ai babu ruwana".

Momma dai murmushi kawai take binsu da shi, dan ita bata da ta cewa, yaran nan nata sai addu'a, dan ma yayyunsu maza sun tsaya tsayin daka a kansu ne, da wlh Obaid and Omaid sai Allah, rashin jinsu ba zai tsaya a iya nan ba, amma Alhamdulillah, a cikin kingdom of power idan suka zo su Jaish basu kyalesu ba, suna kula da su tare da yi masu faɗa da nasiha, dan nasiha tafi tasiri a zukatan mutane sama da faɗa ko duka, wani ma idan ka dake shi sai ya ce ba zai yi abin da kake so ɗin ba sai dai ka kashe shi, amma koya mutun ya kai ga taurin kai wlh nasiha tana tausasa zuciyarsa koda a iya wunin ranar ce kawai, bare kuma nasihar idan aka haɗa da annabi Muhammad (S.A.W) ta fi shiga cikin zuciya ta tausasa zuciyar bawa, karya ne a kirawa mutun Allah da annabi a sake kira bai ji zuciyarsa ta risina ba, sai dai kafurar zuciya ta kafuran farko. So a gaskiya nasiha ta fi faɗa ko duka tasiri musamman ga zuƙatan yara, ku rinƙa nuna masu Allah da annabi cikin ruwan sanyi tare da dabara ta yadda zasu fahimta ya kuma nutsa cikin zuƙatansu, hakan zai sa su taso cikin kamala da nutsuwa.

A Dubai kuwa ga su Ramish, suma a kullum suna yin nasu iyaka baƙin ƙoƙarin wajen ganin kannenen nasu sun nutsu sosai. Amma kuma abin mamaki yadda kuka san ba lafiya ba, kullum rashin jinsu da taurin zuciyarsu karuwa yake yi, sun iya shirya mugunta daki daki babu ko ɗar ɗar, yanzu ga shi Yusuf saurayin Sarina da mu readers muke zargin su suka shirya mashi wannan mugunta, ga shi bawan Allah nan kafin a sakesa ya koma gida baya iya tafiya da kafafunsa, commander Zafar sai da ya ragargajesu kamar ba gobe, takawa da kafafunsu dai sun ƙasa iya yinsa, a haka aka kwashesu zuwa hospital, bayan sun sami lafiya aka sallamesu zuwa gida, wai a haka ma sboda uncle Abbas an yi masu da sauki, ba dan haka ba kaciya ta biyu za'ayi masu, commander baya ɗaukar wasa ai, kuma ba abin da iyayen Yusuf ɗin suka isa su yi, domin kuwa ba wanda ya isa ya ɗaga yatsa a kan wannan masarauta kuma ya zauna lafiya, sannan kuma ai hannu dumu dumu aka kama Yusuf ɗin ba zarginsa ake ba, so dole su ja baki su yi shiru.

Sosai Jaish ya yi masu nasiha mai rasa zuciyar mai sauraro, amma kuma su dai bai wani ratsa su ba, tabbas sun É—an yi ladab, amma dai ba wai can can ba, abin nasu kamar dai ba lafiya ba.

Sun ɗan jima suna hira a tare da mahaifiyar tasu kafin su miƙe su ukun dukka, sannan suka yi mata sallama suka fita.

Addu'a da fatan alkhari ta yi masu har suka fice. Suna fita kuyanga Mama Haulat ta dawo cikin parlourn domin ta ƙarisar mata da lallenta, sannan ta wanke mata tare da yi mata hayakin turaren lallen da sauransu, lalle mai turare take yi mata, shi kwaɓinsa na musamman ne, ya fita daban da sauran dukkan lalle da kuka sani, shi yana yin two months kafin ya goge, kuma kullum zaka gansa kamar sabo yana kyalli, kuma zaki yi ta zuba ƙamshi mai bala'in daɗi har sai ranar da ya goge, larabawar Dubai ne suka fi yawan amfani da shi, yana da tsada sosai, ba ko'ina ake samunsa ba sai gidan mulki, shi ma sai wane da wane, to ita dai momma kowani lokaci irinsa ake yi mata, haka Gimbiya Zunaira da Chuchu ma.

A bangaren Mammien Yah Jawad kuwa, haka ta yi ta jiran Jaish amma ina shiru bai zo ba, dama tasan da wuya ya zo, saboda sau da dama tana aikawa a kirasa baya zuwa, idan kunga ya je kiranta to an aiko ya zo É—in suna a tare da Yah Jawad ne, shi ne zai je, domin kada Jawad É—in ya ji babu daÉ—i, amma idan Jawad baya nan wlh baya zuwa, ko kallo ma bata ishe shi ba.

Ranta ya sosu sosai da sosai, ga shi a duniya bata da burin da ya wuce Jaish ɗin ya auri Fanan, wato ƴar autarta kenan, kanwar Sarina, shi kuma abin da yasa ma kenan baya kaunar zuwa in da take, dan in dai ya je sai ta yi mashi zancen Fanan, bata ma san shi haushi Fanan ɗin take bashi ba, kai shi fa baka gane mashi, kowa ma haushi yake bashi.........😅

Tana burin Fanan ta auri Jaish ɗin ne saboda dalilai da dama, kaɗan daga ciki sun haɗa da kasancewar Jaish jika ne ga the most powerful King Badeen, and kuma ƴan uwansa daga sama har kasa part na mommarsa daga masu mulkin siyasa sai masu sarauta, sannan Jaish yana da tarin dukiya duk da bai kai mommarsa ba, momma ta fi shi kuɗi sosai, amma dai shi kuma ya fi uncle Abbas kuɗi, sai kuma kasancewar ƴaƴan Momma sun fi zama mafi soyuwa a wajen King, wannan ma yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa take son Jaish ya auri Fanan, a ganinta idan Allah yasa Jaish ya auri Fanan zasu samu dama sosai a cikin masarautar, King zai zo Fanan kamar yadda yake son Jaish ɗin, ƙudurin da take da shi na son ganin ɗanta ne a kan kujeran King zai iya cika, amma fa a nata tunanin.

Sam ranta bai ji daɗi ba na rashin zuwansa, da alama akwai abin da ta shirya mashi ne wadda bata son ya tsallaka, sai kuma ga shi ya tsallaka, ranta ya sosu sosai, cikin fushi ta ƙuduri niyar sai ta yi maganinsa, zata gyara mashi zama, shi da yana can bai ma sani ba tana nan tana haukarta, har da wani ɗaukarwa kanta alkawarin ko yana so ko baya so sai ya auri Fanan, bata fa da tabbacin cewa ita Fanan ɗin tana son Jaish ɗin, ita dai tsarinta kawai take tsarawa kamar yadda take ƙoƙarin ruguje soyayyar Jawad ta gina na Rizwan, abin nata dai sai ita ta san me take nufi da bayin Allahn nan, duk so take taga kowa a cikin ƙunci ne ko yaya ne oho mata dai, lokaci ne zai nuna mana ainahin me take da buƙatar cinmawa a ranta.

A bangaren su Jawad kuwa, kamar yadda ya sakata kuka ta hanyar sanyawa a ɓata mata abinci, haka ya sake sakata dariya ta hanyar kaita yawo duk in da take so, sai dai duk in da suka je sai ya tsokaneta ta ɗan yi kuka hankalinsa yake kwanciya, ita dai auta ta tara abubuwan da zata gayawa Chuchun wanda Yah Jawad ya yi mata da gangan idan suka koma gida.

Ko da suka je gidan zoo ma sai da ya tsokaneta, sun je wajen wasu irin macizan mesa masu haɗiye mutane, macizan suna cikin wani irin glass mai kyau aka sanyasu, sai yawaro wasu daga cikinsu suke yi, wasu kuma sun haɗiyi saniya suna ƙawance bata gama narkewa a ciki cikinsu ba, so sun zo wajen suna kallo, sai ɗaukarsu a video suke yi, auta ta tsaya sai magana take yi wa macizan wai su nannaɗu kamar taya yadda take gani a film bari ta gani a zahiri, sai ka ce an ce mata macizan dama magana ake yi masu sai su nannaɗu ɗin, ita kuma Chuchu ta tsaresu da ido tana kallon ikon Allah, idanunsu kawai take kallo, sai dai ta takure jikinta waje guda, da alama tsoro take ji, kawai ta dake ne ta cije ta tsaya a wajen.
Chapter 142 · 0% Book details