Sashe 177
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rera karatun Alkur'ani mai girma manyan baki suka fara yi, kun san fa larabawa akwai iya rera ƙira'a, Abu Abdussalam ne ya buƙaci da a yi karatu sosai kafin a tashi daga taron. Duk wanda zai yi karatu saman stage yake hawa, abin ya yi tsari sosai ya kuma bada ma'ana, sannan ya ƙayatar matuƙa.
Lokacin da Guyson ya fara rera kira'arsa sai da gabaɗaya jama'ar cikin hall ɗin suka bar abin da suke yi suka zuba mashi idanu, tsantsar madarar kyau suke gani, ga zakin murya kamar me, karatu yake rerawa cikin kwanciyar hankali cikin suratul Yusuf, yadda yake fitar da kowani baki, kowani gunna sala sala yake fitar da ita, baya mance wasali ko yaya, dai'dai yake zayyanosu ga nutsuwa matuƙa a tattare da shi sai ya tafi da imaninka, dama ga yaran Momma da bala'in farin jini kamar su suka bawa kansu.
Wasu kyan da Allah ya yi mashi suke gani, wasu kuma kyakkyawan arab hairnsa suke gani, dan fa kunsan gwani ne wajen iya gyaran gashi, ga shi ɗan wanka, wasu daga cikinsu kuma wankarsa suke kallo, wasu zazzaƙar voice ɗinsa ne ya tafi da imaninsa, wasu kuma yadda yake rera karatun cikin nutsuwa ne ya tafi da imaninsu, yaro mai farinjini, dayawa daga cikin manyan bakin nan sun kwaɗaitu da son samu ɗa kamar sa, ji suke yi dama ace ɗansu ne.
A hankali zazzaƙar muryarsa ta fara rikiɗewa daga yadda ya faro karatun cikin zaki da nutsuwa zuwa muryar mai kuka, da kaɗan da kaɗan fararen idanunsa suka fara rikiɗewa izuwa ja saboda kukan, siraran hawaye ne suka fara bin kyakkyawar farar kumarunsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face sanin fassarar surar da yake karantawa da ya yi, zuciyarsa tana kara jinjinawa girman Allah, jikinsa har tsuma yake yi yana kerma a lokacin da yake karanta gudurorin Ubangiji da ya yi ta yi wa annabi Yusuf. Kukansa kara tsananta ya yi lokacin da ya zo in da aka raba annabi Yusuf da mahaifinsa, sanin fasarar surar tasa shi kuka sosai da yake karantota.
Guyson bai kai 17 years ba a duniya, amma Allah ya bashi baiwa ta ilimi fiye da tunaninku, ba boko ba ba Arabic ba, dukka akwai tarin ilimin a kansa, shiyasa yake da saukin kai sosai, saboda ya san girman Allah sosai, yasan duniya ba'a bakin komai take ba, a wajen Allah duniya kamar wuni guda ce. A ƴan shekarun nan nasa ya san farrasarar rabi da kwana na surorin dake cikin Alqur'ani mai girma, kun san larabawa fa ba baya ba wajen iya karatu, basu wasa. A bangaren littafan addini ɗan tahaliƙin nan ba'a magana, yasan dayawa daga ciki, ya haddace dayawa, kuma har yanzu bincike yake cigaba da yi yana kara nutsawa cikin karatun addini, yana ta ƙoƙarin ya haddace fasarar Alqur'ani gabaɗaya, ɓangaren bokon ma baya wasa, yanzu kunga ya kammala secondarynsa, jam zai rubuta kai tsaye ya shiga babban makaranta da kananun shekarunsa, shiyasa ƴan uwansa dukka suke sonsa, saboda jajircewarsa wajen neman ilimi.
Su Omaid kuwa, akwai tarin ilimin suma, amma sai shegen shakiyanci, iyashege, da tarin rashin ji, ga ɗan banzan shiga rai garesu kamar me, ga farin jini kamar su suka yi wa kansu, amma duk da hakan baya hanasu karatu, duk iskancin da suke yi basa wasa da karatu, dan idan suka kuskura suka yi wasa wlh zasu kwashi kashinsu a hannun idan su Ramish suka riƙe su, shiyasa kome zasu yi banda wasa da karatu kam. Kai in takaice maku labari gabaɗaya jinin King Zuhair babu jahili, sai dai ilimin wani ya fi na wani, wani ya fi wani kaifin basira, ga tafasasshen jini, dagiya da kafiya, jarumta da jajircewa, babu jahili sam sam! Suna da dagiya wajen neman ilimin boko dana addini basa wasa!.
Kukan Guyson a cikin hall É—in nan yasa dayawan mutane kuka, masu raunin zuciya sun taya shi kuka, shi kansa Abu Abdussalam sai da idanunsa suka É—an yi ja.
Kasancewar a nutse yake karatun sai ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya kammala. Yana kammalawa Abbien nasu ya miƙe ya rungumo shi tare da fara goge mashi hawaye, kabbara jama'a suka fara yi suna zuba mashi ruwan albarka sosai da sosai.
Omaid ne ya miƙe ya fara rera nasa kira'ar cikin suratul ma'ida, dama kun san su sarakan shiga rai ne, ga farinjini, nan take jama'a suka fara binsa dana mujiya, sai santin kyansa da muryarsa kusan irin na Guyson suke yi. Shi kam Omaid saboda dakiya da taurin zuciya ko ɗigon hawaye babu a idonsa, sarai kuma yasan fassarar surar da yake karantawar, amma akwai taurin zuciya, ko alamar hawaye ma babu a idanunsa, idanun suna bushe karau yake rera karatunsa har ya kammala, har lokacin kuma Abu Abdussalam bai saki Guyson ba, yana bala'in kaunarsa, duk da sun koma sun zauna yana ƙanƙame da hannunsa suna sauraron kira'ar Omaid ɗin. Bayan ya kammala Obaid ma ya miƙe ya fara rero nasa cikin suratul Maryam.
A wannan gaɓar ma sai da Guyson ya yi hawaye, saboda yasan fassararta, sosai kuma ya kara jin tsoron Allah matuƙa, sai goge mashi hawaye Abu Abdussalam yake yi. Shi kuwa Obaid da ya karanta surar ma idanunsa a bushe karau, Guyson sai sharar kwallah yake yi shi da ba shi yake karatun ba, mai karatun kuwa idanu a bushe karau, ga gashin idanun nasa zara zara a tsaitsaye na rashin kunya da rashin jin magana, kowa ya ga idanun Obaid da Omaid ya san akwai tarin rashin tsoro da rashin kunya game da mugunta a cikinsu, basu tsoron a mutu.
Bayan Obaid ya kammala karatun ne Æ´aÆ´an manyan baki suka fara rero nasu.
A can cikin gida kuwa, Leesharh ta saki jiki sosai suna ta hira da Sharifat.
"Leesharh anata gudanar da abubuwa a wajen walima ni kuma ina nan a tare da ke, ki tashi mu je can mana? Kin ga ai sai mu yi hira a can ko?". Cewar Sharifat.
Make mata kafaÉ—a ta yi. "A'a Aunty Sharifat ni bana son zuwa, ban son shiga cikin mutane sosai, ki barni a nan kawai".
Gyara zama ta yi. "To shikenan Leesharh mu zauna tare a nan É—in kawai ko? Mu cigaba da hirarmu ni ma na fasa zuwa duk da nasan Yah Guyson zai damu idan bai ganni ba".
Da sauri ta girgiza mata kai tana faÉ—in. "A'a Aunty Sharifat, kada ki sa ya ji babu daÉ—i, idan kin san zasu damu da rashinki a wajen kawai ki tafi".
Gyarawa ta yi ta kwanta a saman gadon tare da miƙe kafafunta. "Kawai mu cigaba da yin hirarmu Leesharh ba zasu damu ba, ai na gayawa Yah Guyson bari na je wajen ki tun lokacin da ya gaya mun kin yi kuka".
Okey ta amsa mata da shi haka suka cigaba da yin hirar duniya cikin nishaÉ—i abinsu.
Sun shagala da hirar duniya mai daÉ—i Sharifat ta dubi É—an siririn diamond watch dake manne a hannunta. "Kai Leesharh karfe 7 ta yi bamu yi sallar mangariba ba! Sannan karfe 7: 30 dai'dai zan kaiwa Yah Ramish abincinsa da cappuccino, kin san shi bai yarda da kowa ba, bai yarda da Æ´an aikin gidan nan ba, abincin da zai ci ma wanda yake girka mashi na musamman ne, bai yarda wata ko wani mai aiki ya keto cikin É—akinsa ya kawo mashi abinci ba, garama idan da rana ne yana zaune a babban parlourn haka zai iya cewa a kawo mashi, nan ma sai idan yasan na tafi school ko bana kusa ne zai yarda wata ta kawo mashi abinci, duk wata Æ´ar aiki da kika gani a cikin gidan nan sai da Abbie ya aminta da ita kafin ta fara aiki, amma shi ya Ramish bai aminta da kowa ba sai ni da su Yah Rizwan, ke ni ina ganin ma kamar Ummie ma bai yarda da ita ba fa, dan naga baya wani sakin jiki da ita kamar yadda su Yah Rizwan suke yi".
Shiru Leesharh ta yi tana sauraron tun da ta fara maganar, wani irin sanyi ta ji yana ratsa mata zuciya, tsuntsu daga sama gasasshe! Ta sha wahala wajen neman mai kai mashi abinci cikin room É—insa, ashe dai tana tare da ita bata sani ba, wannan shi ne tsuntsu daga sama gasashe! Sosai abin ya yi mata mugun daÉ—i, har wani sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke.
"Leesharh tunanin me kike yi?". Ta yi maganar tare da ɗan taɓata. Ƴar razana ta yi tare da cewa. "Babu komai, amma meyasa Yah Ramish ɗin baya yarda da kowa?".
"Saboda ya ce yana da tarin makiya, kuma fa na gaya maki dukka masu aikin gidan nan daga maza har matansu amintattu ne, shi ne dai kawai bai aminta da su É—in ba".
Shiru Leesharh ta yi tana jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwarsa, yana da gaskiya, su suke ganin kamar dukka ma'aikatan gidan amintattu ne, shi da ya san da cewa ɗan adam yanzu ba a abin yarda bane, ya san kan duniya ai ga shi bai yarda da su ɗin ba, ita kanta Leesharh ai kunga ba amintatciya bace, ƴar leken asiri ce, ƴar ɓadda kama!.
Miƙewa Sharifat ta yi. "Bari na ɗauro alwala Leesharh, kema ki tashi lokacin sallah ya yi, ki yi sallah mu je ki rakani wajen Yah Ramish mu kai masa abinci, idan mun je sai ki jirani a kofar shiga part ɗinsu, dan idan kika shiga na shiga uku na, ba kowa yasan in da part ɗinsu yake ba a cikin gidan nan, kuma Yah Ramish baya son wata ma'aikaciya ta zo arear part ɗinsu, wai kyamar ƴan aikin yake ji, idan sun zo in da yake zai yi amai, so sai ki jirani a waje".
Sharifat baki abin magana, ta aminta da Leesharh ta saki baki sai gaya mata sirrin gidan take yi, bata san cewa Leesharh dai green snake under green grass bace, ƴar ɓadda kama kuma ƴar basaja. Rashin sani bai yi ba a rayuwar nan.
Okey ta amsa mata da shi, nan take ta ji kwarin jikinta ya dawo, wani irin daÉ—i ta ji ya kamata, duk yadda zata yi ta zuba mashi maganin nan yau sai ta yi, dole ta san yadda zata yi ta shammaci Sharifat ta aiwatar da aikinta.