← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 180

Sashe 126

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nisawa ya ɗan yi tare da gyara tsayuwarsa kafin ya ce. "Maman Zainab sanin kanki ne bani da wani iko a kan su Khadija, babansu yana raye kuma danginsa ma suna raye, ni kaninki ne kawai, a halin yanzu sai dai na basu shawara a matsayina na kawunsu, ba wata magana zan gaya maki ba face na tuna maki da abin da kika manta, ki sani ke kika haifi yaran nan, duk in da za'a je a dawo kina da iko da kayanki, babu wata daga cikin ƴan uwan babansu da zata nuna maki iko a kansu, addini bai ce hakan ba, kina da damar buɗe murya ki yi magana a kansu! Ba wai zan haɗaki faɗa da ƴan uwan baban Zainab bane, amma ki sani shirunki zai iya ja maki danasani mafi girma a kan yaran nan, su suka haifa maki su ne da zasu rinƙa tsara maki ga yadda suke son rayuwar yaran ta kasan ce? Dukkansu ba mata bane? Ba suna da yara ba? Akwai wanda ya isa ya ce ga abin da zasu yi wa ƴaƴansu ne? To meyasa sai ke kawai suke tsarawa naki yaran abin da suke so? Ke kuma kin zuba masu ido kina ganinsu, ko kin manta da cewa ƴaƴa amana ce da Allah ya bawa iyaye? Ko kina tunanin idan Allah ya tambayeki meyasa kika tauyewa ƴaƴan nan naki hakkinsu idan kika ce mashi maman su Haidar ne sila shikenan sai Ubangiji ya yafe maki? To idan ma haka kike tunani kin yi kuskure, ba Maman Haidar Allah ya bawa amanar su Zainab ba, ita Maman Haidar tana da nata amanar da zata amsa tambayoyi a kansu ranar gobe ƙiyama, babu wanda zai amsa na wani, kowa nasa zai amsa, dan haka yana da kyau ki buɗe baki ki kuma tsaya komai zai faru ya faru amma ki tabbatar baki jefa rayuwar yaranki cikin kunci ba". Ɗan dagatawa ya yi da maganar yana mai da numfashi kafin kuma ya cigaba da cewa.

"Khadijah bata ɓoye mun komai ba, ta gaya mun duk wani abin da Haidar yake yi mata, to ina son ki sani ni daga nawa ɓangaren na hanata tsayawa hira da Haidar, na gaya mata ko ya tsayar da ita kada ta sake kula shi dan bashi da hankali ko kaɗan, sannan na gaya mata in dai ya sake ɗaura hannunsa a jikinta to kada ta yi tunanin komai ta koya mashi hankali, na bata goyan baya da ta zabga mashi mari, nasan zai iya cewa zai daketa dan ba hankali ne da shi ba, dan haka na ce mata ko kusa ko alama kada ta tsaya ya daketa, sannan kuma kada ta sake nuna cewa tana jin tsoro ko shakkarsa, ina son ki buɗe kunnuwanki kema ki saurateni, ko a cikin parlourn nan Haidar ya zo yin hira da Khadija kada ki sake bari, kada ki yarda, ki ce mashi kin hana hirar daga yau, ya bari sai anyi auren, sannan shiru da kike yi kina zuba wa Haidar ɗin da uwarsa ido ya isa haka, ba wai na ce ki yi wa yar mijin rashin kunya bane, a'a, kada ki manta yarsa ba uwarsa bace ba, dan haka ba kowani irin takaki zata yi ki yi shiru ba, lokacin da ya dace ki yi fito na fito da su ya yi, yanzu ne yakamata ki gyara masu zama su san da cewa kema ƴa ce, kuma dan zaman aure ya kawo ki cikin familynsu ba hakan yana nufin kema naki familyn basa sonki ba, ƴa ce kamar kowa, kuma kamar yadda kowasu iyaye suke son ƴaƴansu haka kema ake sonki, dan haka yana da kyau ki mayar da hankali, a yanzu baban Zainab hankalinsa baya a kanku gabaɗaya, yanzu ne lokacin da ya dace ki taka masu birki dukkasu, ki zana masu jan layi, su shiga taitayinsu da kyau......". Sake dakatawa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, yau ya samu ya fitar da abin da ya jima yana cinsa a cikin zuciyarsa, ya jima yana son gayawa yayar tasa da wannan shirun nata a kan ya yi yawa, amma taki bashi dama ta saurare shi, ta biyewa Hauwa a tunaninta hakan ce mafita, to Alhdulillah a yanzu dai ya samu ya fitar da abin da yake cikin cikinsa, ya huta.

Bai ɓoye mata komai ba, duk abin da Haidar yake yi wa Khadijah ya sanar da ita tas, sannan ya ɗora da cewa. "Ga Khadija ɗin a zaune a gabanki, ki binciketa da kyau a iya haka abin ya tsaya ko kuma ya wuci hakan, kin tsaya biyewa Hauwa har ya zama ƴarki bata samun damar da zata iya gaya maki halin da take ciki sai dai ta zo ta sameni ta sanar da ni, kinyi kuskure babba, kuma yanzu lokacin ɗaukar mataki ne.......".

Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon knocking na kofar gida da suka ji ana yi.

"Khadijah je ki duba wanenen mai buga kofar nan". Cewar Maman nasu.

"No ta barshi bara na dubi". Sadiq ya faÉ—a tare da sa kai ya nufi wajen.

Shiru maman Zainab ta yi tana tunanin maganganun É—an uwan nata, duk abin da ya faÉ—a zancensa haka ne, yana a kan gaskiya, tun farko ma ita ta yi masu sake, yanzu ga shi wankin hula ya kaita dare.

Wani irin mamaki ne ya kama Sadiq a lokacin da ya buÉ—e kofar gidan, ba kowa bane yake knocking face baban Zainab a tare da Hauwa, dukkansu sun ci uwar kwalliya, ko daga ina suke haka oho dai.

Sannu da zuwa Sadiq ya yi wa baban Zee É—in yana bin Hauwa da kallo, sai wani yauki da yange take yi, tana sanye cikin shadda da ya sha É—inki mai kyau, ko rantsuwa Sadiq ya yi ba zai yi kaffara ba wannan shadda daga shagonsu aka É—auketa, wato kayan da baban Zainab É—in ya kwasa ranar da ya je shagon ita ya kaiwa kenan? Sadiq ya tambayi kansa da kansa, lallai akwai cakwakiya ba kaÉ—an ba. Sai zuba kamshi suke yi suka nufi cikin gidan.

Saboda tsabar mugunta irin na Hauwa ce ta ce sai dai baban Zainab É—in ya rakota ta gaisa da maman Zainab, dan tana kewar kawar tata, kawai ta yi hakan ne dan ta kara kunsawa maman Zainab bakin ciki, yanzu fa Hauwa bata gidan mijinta, da alama kashe auren ta yi ko wani abu makamancin hakan, yanzu haka daga gidan kanin mahaifinta ta fito, garinsu maman Zainab kenan, ita ma Hauwa dama mahaifinta ya jima da rasuwa, ya riga baban su maman Zainab É—in ma rasuwa, so already dama a hannun kanin mahaifin nata take, ku ma shi ba mutun ne mai karfi ba, kusan kaso saba'in na matsalolin gidansa ma Hauwar ce take É—aukar nayinsu, shiyasa duk abin da zata yi yake ganin tana a kan dai'dai, dan yana tsoron kada ya ce bata yi dai'dai ba ta É—auke mashi tallafi, Allah ka rabamu da mutuwar zuciya. Yanzu ta zubar da Æ´aÆ´an nata wa dangin mijinta ta koma garinsu.

Suna sako kafarsu a cikin parlourn aka sake yin knocking na kofar gidan, a lokacin shi kuma Sadiq yana ƙoƙarin shiga room ɗinsu, dan ya je ya ɗan kwanta ya huta kafin ya fita kasuwa.

A dubu ɗari maman Zainab ta miƙe tsaye na ganin Hauwa a tare da baban Zainab da ta ɗauki kwanaki bata sanya shi a idanunta ba.

Wani irin shu'umin murmushi Hauwa ta sakar mata tare da faɗin. "Gaskiya nayi kewarki sosai maman Zee, yau dai na ce dole baban Zee ya rakoni na zo mu gaisa, zan iya zama a kujerar taki ne?". Cike da kirsa da makirci ta yi maganar, daga jin yadda take magana kuma ba sai an faɗa ba kunsan da biyu ta yisa, ta yi ne duk domin da kara jefa zuciyar maman Zainab cikin ƙunci.

Kallon baban Zainab kawai maman Zee take yi, tamkar bata san da Hauwa a wajen ba. Shi kuwa Baban Zee tamkar bai san da mama Zee É—in a cikin parlourn ba, wucewa ya yi ya zauna a saman sofa yana faÉ—in. "Hauwa me ya tsayar dake a tsaye? Ki samu wuri mana ki zauna......". Yanzu fa har su Khadija ma ya mance da su bawan Allah.

Bai gama rufe baki ba aka banko labulen parlourn aka shigo ciki. Ba kowa bace face su maman Haidar, dama tsawon kwanaki yau suna neman baban Zee ɗin basu samu ganinsa ba, shi ne nan suka sanya Haidar da ya saka masu ido duk idan ya ga giftawarsa ya sanar da su, sun zo gidan ya fi sau a kirga suna cin mutuncin maman Zee a kan wai ita ta hanashi zuwa wajensu, basu san ita kanta bata samu ganinsa da ido ba, amma haka suke cin mata mutunci son ransu, sai dai ta bisu da ido kawai. To yanzu kafin baban Zainab ɗin ya zo gida sai da suka fara zuwa kasuwa Hauwa ta kwashi abin da take so, sannan ne suka nufo gidan, a nan ne kuma Haidar ya gansu, shi ne ya yi maza ya sanar da mamar tasa ta hanyar kiranta a waya ya ce mata to ga baban Zainab ya nufi gidansa, shi ne suka biyo sahunsa dan su zo su ji dalilinsa na kin zuwa in da suke, su kira wayarsa ba zai ɗauka ba, ga batun aurensa da suke ta jiran ya zo ya je su gaisa da bappan nasa a samu a saka rana, ayi komai cikin ƙanƙanin lokaci, ƴar bapparsa suke son aure mashi dama, to fa shi ne suke ta nemansa amma shiru, sai yau Allah ya yi suka ji labarin ga shi a gida, shi ne suka kwaso ayari suka yi maza suka zo.

Ko sallama babu suka faÉ—o cikin parlourn fuskoki babu mutunci, shi kuma Haidar ya tsaya daga bakin kofa. Baban Zainab yana zaune a saman sofa tamkar bai san da shigowarsu ba.

Maman Zainab ce ta ce masu. "Sannunku da zuwa".

Ita kuwa Hauwa wani irin kallon sama da ƙasa ta wurga masu kafin ta ce. "Ya zaku wani shigowa mutane cikin ɗakin babu ko sallama kamar wasu dabbobi? Ko dai ba musulmai bane ku?".
Chapter 126 · 0% Book details