Sashe 117
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Akwai komai a cikin toilet ɗin na buƙata, harta su kyawawan towels masu kyau na wanka, ga jacuzzinta ma mai ɗan girma da shi. Wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala ta fito, tun asali ita Leesharh tana yawan son zama da alwala, shiyasa a duk lokacin da ta shiga toilet bata fitowa sai ta ɗauro alwala ko da ba lokacin yin sallah bane ba.
Akwaitin kayanta ta jawo bayan ta fito daga cikin toilet. Dukka Arabian dressing ne a ciki, daga dogayen riguna, sai riga da sket, riga da wando. Leesharh mayyar son riga da wando ce, tana da son yin gayu sosai, kawai halin babu da suke ciki ne yasa take hakura, amma idan ba haka ba tana da son yin gayu, lokacin da take gaban iyayenta mafiya yawan kayanta riguna da wanduna ne, ta ci gayu gwanin ban sha'awa, ga ta kyakkyawa kuma dirarriyar mace.
A yanzu ma riga da wando ta ɗauko tare da mayar da sauran kayan da ta fitar ciki. Riga da wandon sun haɗu makurar haɗuwa, Arabian dressing ne, wando ne mai kyau dogo har ƙasa, sai rigarsa da ya tsaya mata izuwa gwiwowinta, sannan wani ɗan ƙaramin veils mara girma sosai.
Da alama Leesharh ta jima a tare da larabawa, domin kuwa tsab ta iya dressing nasu ya zauna a jikinta da kyau da kyau, kamar wata balarabiyar gaske, a yanzu ma haka ta shirya cikin wannan kaya ta fita ras abinta, ta yi rolling veil É—in nan a kanta kamar yadda suke yi, sai kyanta ya kara fitowa sosai.
Wayarta ta É—auko ta kunna da nufin ta duba time, haka kawai ta tsinci kanta da shiga fargaba da faÉ—uwar gaba na kunna wayar, sai take jin kamar kada ta kunna wayar ta kyale shi a haka.
Amma haka ta kunna ta duba time. 2:5 pm. Ganin har karfe 2 ta ɗan wuce ne yasa ta zaro waɗan nan manya manyan idanun nata waje. Cikin hanzari ta miƙe tare da fara waige waigen ina ne gabas dan ta yi sallah?.
Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi saurin juyawa izuwa kofar shigowa room É—in. Fadila ce ta shigo hannunta É—auke da abinci a wani katuwar try, É—azun ma ta kawo mata abincin, sai ta sameta tana barci, shi ne ta koma da abincin, yanzu kuma na rana ne ta kawo mata.
Fadila fa babbar budurwa ce wadda a kallah zata kai 25 year, amma saboda tarbiya irin na gida Abu Abdussalam yasa suma masu yi masu aiki suke É—aukar kansu kamar dukka Æ´an uwa ne, basu nuna banbanci ko fifikon shekaru, suna aiki a tare sun zama kamar Æ´an uwan abin gwanin ban sha'awa, yanzu na tabbata kun ji sha'awar yadda Fadila bata nuna cewa ai ta fi Leesharh shekaru dan haka ba zata kawo mata abinci ba, da wasu ne za su ce sai dai ta zo da kanta ta É—auka, amma a gidan Abu Abdussalam ba'a yin haka, masu yi masu aiki ma suna da tsari na bin doka haka ina kuma ga Æ´an gida? Masu aiki ma an koya masu haÉ—in kai har haka ina kuma ga Æ´an gida? Ya kuke tunanin haÉ—in kan Æ´an gidan zai kasance?.
A saman carpet ta ajiye mata abincin tare da sake yi mata sannu da tashi daga barci. Kasancewar ita Leesharh tana under umarni da kashedi na kada ta kula kowa a cikin gidan, sai ya zamana ciki ciki ta amsawa Fadila É—in, tana yi kuma tana kawar da kanta, dan a wawtarta hakan ce zata sanya ta yi nesa da Æ´an aikin kada ta kulla abota da kowa.
Fadila kuwa, ta yi tunanin saboda Leesharh bakuwa ce yasa bata sake da ita ba, ta yi mata wannan uzurin, a in da ta ajiye mata abincin kawai tare da nufar kofar fita waje tana faɗin. "Idan kin kammala cin abincin zanzo na ɗaukeki mu je ki ga wasu gurare a cikin gidan, daga nan sai ki ga parlourn da zaki yi aiki a ciki, sai bedroom ɗin Aunty Sharifat da zaki rinƙa gyara mata, nata ita da Guyson, bedroom biyu ne kawai zaki rinƙa gyarawa, Ummie ta sanar da ni shi ne aikinki".
Nan ma ƙasa ƙasa Leesharh ta amsa mata da. "Okey amma dan Allah ina ce alkibla a wannan gida?".
Da hannu Fadila ta nuna mata gabas tare da sa kai ta fice abinta. Saman carpet ta yi tsaya ta fuskanci alkiblar, sannan ta tada sallah da iya wannan veil na kanta da ta yi rolling.
Bayan ta idar ta yi addu'oi sosai da sosai, lokacin da ta É—auka tana zuba addu'ar ma ya fi lokacin da ta É—auka wajen gabatar da sallar. Bayan ta shafa ta matso kusa da abincin nata, dama yunwa take ji, tun safe bata ci komai ba, sai kuka Æ´aÆ´an hanjin cikinta suke yi.
Abincin ta fara zaɓar wanda zata ci, cikin nutsuwa ta zuba a cikin plate, ba ɓata lokaci hannu baka hannu kwarya ta fara cin abincin. Wani tunani ne ya faɗo mata, tunawa da yadda taga yawan Cameras tun daga kan titin da zai kawoka gidan nan har izuwa cikin gidan ta yi. A hanzarce ta ɗaga kanta sama ta fara neman camera a cikin room ɗin nata, dan ta tsorata, a tunaninta akwai camera, kada ya zamana duk abin da take yi masu gidan suna kallonta.
Ganin bata ga alamar camera a room É—in bane yasa ta cigaba da cin abincinta tana tunanin yadda zata kaya mata a wannan gida.
After some minutes. Ta kammala ci tas, ta ci abincin sosai, sannan ta tattare komai kamar ba'a taɓa cin abinci a wajen ba, ta kwaso kayan abincin ta fito waje. Nan ta bar wayarta a saman bed ɗin tata, ita da aka ce ta ɓoye wannan wayar, kada ta fitar kowa ya gani, ta bari za'a bata wayar amfani a gidan, dan duk masu aikin gidan suna da wayoyi da Ummie ta saya masu wanda zasu iya kiran ƴan uwansu, haka tsarin gidan yake, amma ita Leesharh tun ba'a je ko'ina ba ta baro wayar sirrinta a saman bed wangalam ba sakayawa ta yi waje abinta.... Toh fah, akwai fa ƙura, da alama Leesharh dai ita da kanta zata tonawa kanta asiri a wawtarta da shiriritarta.
Fitowa haɗaɗɗen parlourn nasu ta yi, yadda part na masu aikin gidan yake ma sai ya baka sha'awa, parlourn ne haɗaɗɗe mai cike da komai na more rayuwa, sai bedroom manya manya guda huɗu a cikin parlourn a hawa na farko kenan, a na biyun ma hakan ne har karshe, so ƴan aikin da suke hawa na farko suna amfani da part ɗin, ƴan aiki na hawa na biyu ma haka, in da Leesharh zata yi aiki shi ne ainahin family part, in da ɗakin barcinsu da komai da komai nasu yake kenan, to masu aiki uku ne kacal a wajen, da Leesharh ta zo yanzu sun zamana su huɗu, Fadila da Radia ƴan mata ne da a shekaru ma zasu iya zuwa mate, sai kuma babbar su wadda take kamar matsayin uwa a garesu, ita kam bazawarece wadda a kallah zata kai shekaru 40 haka a duniya, ita take kula da su da kuma aikin da suke yi idan ya yi kyau, sannan tana ɗaya daga cikin masu yin girki a gidan, a hawa na ƙasa ake yin girki ba'a family part ɗin ba, dan Ummie ta ce bata buƙatar kamshin ingredients komai ƙanƙantarsa a hawan nasu, dan haka ba za'ayi amfani da kitchen na part ɗin ba, sai dai ayi girkin a kasa a ɗauko a hauro da shi sama a jere masu a saman table, haka tsarin gidan yake, suna da tsari sosai da sosai, kuma a kan tsarin suke tafiya.
So kowani hawa Æ´an aiki huÉ—u ake É—auka kamar yadda part É—insu yake É—auke da bedroom guda huÉ—u. Leesharh tana fitowa ta ci karo da su Fadila suna kallo Arabians film a makeken Tvnsu da yake a cikin parlourn nasu.
Sannu ta yi masu, Fadila ce ta miƙe ta karɓi trayn kayan abincin daga hannunta tare da ce mata ga waje ta zauna mana.
Okey kawai ta amsa da shi tare da nufar saman sofa ta zauna, ita kuma Fadila ta yi waje da kayan abincin.
Shiru ta yi bata yi magana ba, Radia ce ta ce "Ke baki yin magana ne? Gaki kyakkyawa".