Sashe 115
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sannunki da zuwa Hauwa ya gida ya yara?". Ya faÉ—a yana bata full attention É—insa.
Murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mashi da komai lafiya lou.
Shiru ya ɗan tsaya tare da zuba mata idanu yana ta kallonta. Maman Zainab kuwa sai ta taɓe baki tana ganin abin kamar a Tv a gabanta, ita kuma Aunty Hauwa sai wani irin murmushi take yi mashi.
"Yanzu zaki tafi ne na kai ki gida?". Baban Zainab ya tambaya.
Wani irin zaro idanu maman Zainab ta yi, abin da bata taɓa ji ba, ba kuma ta taɓa gani a tattare da shi ba, kai ina bata yarda ba, a mafarki ta ɗauki abin, dan haka sai ta kai hannunta saman face ɗinta ta ɗan mari kumatunta wai idan mafarki take yi ma ta farka.
Amma ina sai ma ji da ta yi Aunty Hauwa tana cewa. "E zamu iya tafiya a tare duk da ba yanzu naso tafiya ba, amma tun da zaka mayar dani ai komawa ta kamani".
"To muje ko?". Ya faÉ—a yana mai cigaba da kallon face É—inta sosai, sai wani uban murmushi take yi.
Maman Zainab bata ankara ba tana can tana tunanin mafarki take yi ne ko ba mafarki ba kawai sai ganin Aunty Hauwa ta yi sun jera da baban Zainab sun nufi wajen parlourn.
Ai bata san lokacin da ta bi bayansu ba, a harabar gidan ta ce. "Hauwa menene haka kuma?".
Dakatawa daga tafiyar da suke yi Aunty Hauwa ta yi tare da juyowa ga maman Zainab É—in, É—aure fuska ta yi sosai kafin ta ce. "Wacece kuma Hauwa? Ni kike kira ko dai wata?". Tashin hankali da ba'a sanya mashi date kenan!!.
Wani irin zaro idanu waje maman Zainab ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, cikin tashin hankali ta ce. "Hauwa ban gane me kike faɗa ba? Ban gane me kike nufi ba? Ko dai kunnuwana sun dai'na ji ne? Ko dai har yanzu a cikin mafarki nake ne?".
Kallon baban Zainab Aunty Hauwar ta yi tare da cewa. "Abu Zee mu je ko? Bani da lokacin A'isha ni kam".
Da okey kawai ya amsa mata ba tare da ya kalli in da maman Zainab ɗin take tsaye ba, kamar bai taɓa saninta ba a duniya.... Tashin sense kenan yau ake yinta a wannan gidan.
Gaba Aunty Hauwa ta yi tana wani rangwaÉ—a tare da kara gaya mashi su je ita fa bata da lokacin maman Zainab a yanzu. Rufa mata baya ya yi da nufin su tafi É—in.
Ai tsabar kishi da bakin ciki yasa Maman Zainab bata san lokacin da ta yi kukan kura ta damko wuyar Aunty Hauwar ba, idanunta sun rufe, wani irin bakin cikin take ji kamar zata haÉ—iyi zuciya ta mutu, wani irin cin amana ne wannan mai azaban raÉ—aÉ—in zafi haka?.
Cikin sauri baban Zainab ya fara ƙoƙarin kwatar Aunty Hauwar daga shaƙar da maman Zainab ta yi mata, da alama mafa baban Zainab ya manta wacece maman Zainab. Tirƙashi.
Maman Zainab kuwa ta shaƙeta da iya karfinta na karshe tana faɗin wlh sai ta kasheta, azzaluma maciyi amana, su taso a tare su yi karatu a tare, komai a tare suke yi ne zata nemi ta ci amanarta haka? To wlh ba zata barta ba, kasheta zata yi sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta................
Tashin hankali, akwai babbar cakwakiya na kin ƙarawa a wannan gidan, kenan Aunty Hauwa amanar maman Zainab ta ci? Ta kaita wajen malami da sunan samun mafita kenan kanta ta shiryawa hanya mai kyau ba maman Zainab ɗin ba?🤔 Ita kuma maman Zainab cikin rashin sani ta bashi maganin kaunar Aunty Hauwar da hannunta ya sha?🤔 Ga shi har da ƴaƴanta su Khadijah ta bawa suka sha dan rashin hankali da rashin tunani? To kenan ya makomarsu take su kuma? Suma zasu bi ayarin Aunty Hauwa kamar babansu kenan? Bala'in nan, wannan shi ne bala'i, akwai yaki gagarumi a cikin wannan gida, ya makomar maman Zainab? Farkoma ya makomar auren Aunty Hauwar? Da ni da ku dai duk mun san tana da aure? Alamu kuma sun nuna baban Zainab dai ya kamu da sonta, kuma ga dukkan alamu ita ma hakan take so, to ya kenan batun nata mijin?🤔 Ina su maman Haidar? Zasu yarda da hakan kuwa? Kada ku manta sun yi mashi mata fa a cikin family, lallai akwai rikici da rikita rikita, yau akan Aunty Hauwa baban Zainab ya mari Maman Zainab, tab duniya kenan, amana ta yi ƙaranci, ni dai PRINCESS TEEMA na haɗa kayana sai mun haɗe daku gobe dan jin yadda wannan bala'in yakin da ta tinkaromu zata kaya!! RAWANIN ZALINCI ya fara ɗaukar tafasa ma ba zafi ba, Zalunci ta ko'ina😥💔
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 13/8/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________34🔥
Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta damko wuyar Aunty Hauwar, idanunta sun rufe, ita dai ta kashe Aunty Hauwa kawai hankalinta ya kwanta.
A karo na biyu baban Zainab ya kara mata wani zazzafar mari, sai dai a wannan karon ko da ya mareta bata saki Hauwar ba, sai ma kara ƙanƙame wuyarta da ta yi, yadda ta ji zafin wannan mari haka ta kara shaƙe mata wuya gam.
Kafin baban Zainab ya samu ya kwaceta daga hannunta har Hauwa ta sume, saboda azaba, tasha shaƙar manya, ga shi cikin fushi aka yi mata shaƙar.
Fara ƙoƙarin dukan maman Zainab ɗin ya yi, amma ina, ai bata tsaya ya daketa ba, sai ma kwasawa da ta yi a guje ta nufi cikin kitchen, muciyar tuƙa tuwonta ya je ta ɗauko, hauka hauka ta nunawa baban Zainab a in da ta fara ƙoƙarin dukan Hauwa dake sume yashe a ƙasa da wannan muciya, ta sumar da ita ɗin ma ba zata kyaleta ba.
Da baban Zainab da ya ga haka sai shi ma ya sanya mata karfi da nufi ya yi mata duka ya kuma karewa Hauwa dake sume faÉ—ar. Amma ina maman Zainab taki yarda ta bari ya sake É—aura hannunsa a jikinta, sai zulle mashi take yi, shi kuma yaki barinta ko sau É—aya ne ta kwalawa Hauwa wannan muciya da ta É—auko.
Daga karshe dai ya yi nasarar kwace muciyar tare da kamata ya turata cikin ɗaki, ya kuma rufo kofar ta waje ya barota a ciki. Kamar zararriya haka ta rinƙa dukan kofar nan da iya karfinta na karshe, tamkar zata ɓalle kofar, hakan yasa Haidar ya farka daga barcin asararsa da yake yi.
Shi kuwa baban Zee bai ma sake bi ta kanta ba, ruwa kawai ya É—ebo a kitchen ya zo ya yayyafawa Hauwa ta farfaÉ—o. A haukace ta farfaÉ—o tana ambatar ta shiga uku yau zata mutu.
Hakuri ya fara bata kamar wani É—anta, harda tsugunnawa a gabanta ya fara rarrashinta. Ji maman Zainab take yi zuciyarta zai iya fasa kirjinta ya fito waje, hakan yasa ta fara neman abin da zata karya wannan kofar da shi ta fito waje, yau ji take yi idan bata kashe Hauwa ba ba ita ba zaman lafiya, kada ku manta dama baban Zainab ya ce tana da balai'n kishi na wuce tunani, bare kuma ace irin wannan cin amana mai bala'in zafin da Hauwa ta yi mata ai dole ne ta haukace masu, kawarta ce fa da suka taso tun yarinta, duk da tun suna yara halinsu ya sha banban, amma hakan bai sa sun rabu ba, kawance ta É—aure har girma izuwa aure, ace rana tsaka ta yi mata irin wannan É—anyen aiki É—anyen cin amana, ai dole zuciya ta sosu over.
Fatana a nan dai shi Allah yasa mata kun ɗauki darasi! Duk abin da yake faruwa da maman Zainab ita ta jawa kanta, kama daga abin da su maman Haidar suke yi mata har wadda Hauwa ta yi mata a yau, duk ita ce da laifi, ta ya za'ayi ki rinƙa sakin baki kina gayawa wata cewa mijinki yana kula dake hundred over hundred? Kuma sai ma ki rasa wadda zaki rinƙa gayawa hakan sai wadda ita mijin nata baya yi mata hakan, a haka kike tunanin zaki samu zaman lafiya? Ke kina tunanin cewa ai kawarki ce, kun taso tare ba zata ci amanarki ba, to ai ga shi nan kun gani ido da ido, ita tana can tana fama sai ta sha rana ta yi kasuwanci tukun nan ta iya biyawa kanta dukkannin buƙatun da take so, ke kuma kina daga kwance ake yi maki komai, sannan kizo kina bata labarin irin daɗin da kike ji ki ce ba zata yi tunanin ita ma bari ta yi join ɗinki kuci daɗin a tare ba? Waye baya son daɗi? Waye yake son wahala? Kin yi kuskure babba idan ma haka kike tunani, wata ma domin hasada da bakin cikin bata samun abin da kike samu ko ba zata auri mijin naki ta shigo kuci daɗin a tare ba zata yi duk yadda zata yi ta rabaki da mijin, idan kuma hakan bai samu ba to zata yi duk yadda zata yi ta ga ya dai'na kyautata maki kin koma wahala kamar ita.
Ai a zamanin yanzun nan duk yadda kuke tare da mutun da ya tambayeki ya mijinki? Alhdulillah kawai zaki ce mashi, daga wannan Alhdulillah É—in kada ki kara kada ki rage, bakinki kanin kafarki, idan kuma kin ki ji to fa ba kyaki gani ba.