Sashe 154
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyowa Leesharh ta yi suka nufi dawowa cikin babban parlourn, Sharifat ta sanya takalma mai tsini wato high heel sosai, sai kwas, kwas, kwas take yi a white tiles na parlourn, ita kam Leesharh plat shoe ne a kafafunta, suma plat shoe É—in Sharifat É—in ce ta bata kyautarsu kala goma sha biyar, ciki harda high heel guda biyar, amma bata saka high É—in ba, sai ta É—auki flat ta sanya, duk da haka ta yi kyau sosai.
Suna ƙarisa zuwa cikin parlourn Sharifat ta tsaya tana ƴan waige waige.
"Lafiya Sharifat kika tsaya?". Leesharh ta tambayeta tana binta da kallo.
"Naji kamshin perfume É—in Yah Ramish ne shi ne nake neman ta ina yake?". Ta bata amsa tana nufar wajen kofar dining room.
Da farko kamar Leesharh ba zata bita ba, amma tunawa da ta yi tana matukar son taga Ramish É—in yasa ta yi saurin rufa mata baya, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, yau zata kalli wanda ta zo yin aiki a kansa, fargaba da faÉ—uwar gaba ne cike tab a ranta, ta takure jikinta waje guda saboda rashin gaskiya da kuma tsoro.
Ganinsa yasa Sharifat ta saki wani cool murmushi kamar budurwar da ta ɗauki shekaru tana begen ganin saurayinta sai yau ta gansa, kunsan ba ƙaramin daɗi zata ji ba, to haka ita ma Sharifat ɗin ta ji daɗi sosai har yasa ta saki murmushi ba tare da ta sani ba.
Ita kuwa Leesharh ganinsa yasa ta haɗiyi wani irin wahalallen yawu duk da bata da tabbacin cewa shi ne, amma lallai ba shakka ta ji a jikinta shi ɗin ne kamar yadda masu nikaf suka gaya mata cewa in dai ta gansa to zata ji a jikinta cewa shi ne, haƙiƙa kuwa ta ji hakan, nan take bugawar zuciyarta ya karu, faɗuwar gaba da fargaba suka karu, kanta har wani irin sara mata ya yi, a take a wajen ta ji wani irin karayar zuciga a kan wannan aiki, ji ta yi ina wlh in dai wannan shi ne Ramish to ba zata iya bin diddiginsa ba, wannan ganinsa kawai yana sanyata faɗuwar gaba, iya faɗuwar gabar kuma kawai ya isa ya kasheta, ai wlh idan bata yi hankali ba da kanta zata tonawa kanta asiri, bare ma ace su haɗa ido da shi, wannan tun bai yi magana ba zata ruɗe ta fara ce mashi ba laifinta bane turota aka yi, ta tonawa kanta asiri, har wani irin zufar tsorata da ganinsa ne ya fara tsastsafo mata, yau almost 2 month kenan tana gidan tana son ganinsa, ta jima tana begen ganinsa, yau ta gansa kuma sai ta fara danasanin ganin nasa da ta yi, duk sai ta ji dama ace bata gansa ba da ya fi mata alkhari, yanzu ganinsa da ta yi zai sanya mata fargaba, yanzu zata kasance kullum cikin fargaba da tsoron ranar tonan asiri, dama gata duk a firgice.
"Yah Ramish sannu da hutawa". Cewar Sharifat da take tsaye a kusa da shi.
Ba tare da ya buÉ—e idanunsa ba, ya kuma É—auki tsawon minti É—aya kafin ya amsa mata da. "Yauwa lil sis".
Sosai Leesharh ta kara jin faÉ—uwar gaba da jin voice É—insa, yana da sanyin murya sosai, sai dai muryar tasa akwai kaifi sosai a cikinta, daga ji kasan manyan maza ne suke magana.
A É—an tsorace Sharifat ta sake cewa. "Yah Ramish ya baka je wajen walima ba?". Ta yi maganar tana É—an É—ari É—ari, domin tasan halinsa baya son tambaya kuma baya son yawan magana, idan magana ta wuci biyu zuwa uku to baya amsawa koda kuwa Ummie ce ta yi maganar.
Ai kuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa bai amsa mata ɗin ba, kamar babu shi a wajen. Ganin hakan yasa Sharifat ɗin ta ce da Leesharh su tafi kawai. A hanzarce Leesharh ta juya ta yi gaba, har mamaki ta bawa Sharifat ɗin na yadda ta juya a hanzarce kamar wata maras gaskiya. Amma bata kawo komai a ranta ba, sai ma tunani da ta yi na cewa kodai tsoron Yah Ramish ɗin ne yasa ta birkice haka? Bayanta ta bi kawai suka fita parlourn suka nufi elevator dan su sauƙa kasa.
Sai dafe saitin zuciyarta Leesharh take yi, dan ji take yi tamkar zuciyar tata zai fasa kirjinta ya fito waje, a gaskiya ta tsorata da ganin Ramish, wannan ma fa ba ido cikin ido ta kalle shi ba, akwai aiki kenan.
Hall É—in kai tsaye suka nufa, yau gidan ya kara cika da jami'ai kala kala saboda ministocin da manyan bakin da suka halarci walimar, an kara tsaro sosai da sosai.
Suna zuwa Sharifat ta wuce saman stage wajen Æ´an uwanta ta zauna a kusa da Guyson, ita kuwa Leesharh ta nufi wajensu Radia dake can gefe guda wajen shirya drinks. Tana zuwa ta tsaya idanunta suna a kan stage da Sharifat ta hau.
Izuwa yanzu ta shiga ruɗani sosai, faduwar gaba kuma yana neman kasheta har lahira, ba komai kuma ya hassasa mata hakan ba face ganin, Rizwan, Bilal, Dr Raj da ta yi a saman stage ɗin, ta ruɗe ta yadda har ta kasa iya banbance kamanninsu da Ramish da suka baro a cikin gida, yau rana ta farko da ta fara ɗaura idanunta a kan Abu Abdussalam bawan Allah, tana jin labarin kirkinsa bata taɓa ganinsa da ido ba, ta haura wata biyu a gidan, to yau dai ga shi nan a tsakanin ƴaƴansa.
Da ka gansa ba tambaya kasan yayan Mommar Zunaira ce, yana kama da Guyson sosai, sai ka rantse da Allah Guyson ɗan cikinsa ne ba ɗan kanwarsa ba. Ya sha farar arab jallabiya mai tsada da alkyabbarsa, rawani ya yafa daga kansa zuwa kafaɗunsa, daga sama har ƙasa fararen kaya ne a jikinsa, ɗan gara alkyabbar jikinsa ma akwai ratsin baki kaɗan a jiki, half cover shoe ne a kafafunsa masu bala'in tsada, suma launin fari, waɗan nan family yau sun haɗu iya haɗuwa. Sai dakon jiran Ramish suke yi, shi kuwa basu san ma ya tuɓe ya sanya kayan shan iska yana zaune abinsa ba, yama mance da wani zancen walima da ake gudanarwa a cikin gidan.
Leesharh dai yau fargaba da faɗuwar gaba ne suka kusa yin ajalinta, duk in ta ɗaga ido ta kalli Dr Raj and Bilal sai taga kamar Ramish ɗin take kallah, ta kasa iya ɗaukar try ɗin drinks ɗin ta kaiwa mutane, saboda kerma da hannayenta suke yi, tana tsoron ta ɗauki try ɗin ta je ta ɓarar da shi, glass cups ɗin su tarwatse a wannan haɗaɗɗen tiles ɗin, ga shi kuma yadda aka jera cup's ɗin wasu kan wasu ɗorin ɗosalo tamkar yadda ake jerawa a party na manya manyan shugabannin manyan kasashen ta duniya, sun yi kyau a ido kam, amma ɗaukarsu sai ka shirya, sai mai nutsuwa. So ita dai Leesharh ta kasa iya ɗauka, domin fargaba da faɗuwar gaba sun ja mata kerman jiki.
Waje ta samu ta karshen hall É—in ta zauna, ta rasa dalilin da yasa kawai ta ji hawaye sun fara gangaro mata a saman face É—inta, har wani irin shesshekar kuka take yi mai tsuma zuciyar mai sauraro, ita wannan bala'i ya fi karfin shekarunta, ta rasa ya zata yi, ji take yi kawai kamar ta yi wani laifin da zai sanya a kasheta kawai ta huta da wannan bala'i, tana kewar babanta, tana son sake ganinsa koda sau É—aya ne, idan ta tuna cewa babanta yana hannun masu nikaf, kuma zasu cutar da shi idan bata mayar da hankali ta yi aikinta da kyau ba, sai ta ji wani irin kuka mai karfi ya zo mata haÉ—e da karfin gwiwar zata iya yin komai a kan baban nata, idan kuma ta tuna wanene Ramish da yadda ta kalli suffarsa da kirarsa sai ta ji zuciyarta ya karaya ta fara yi wa kanta fatar mutu. Ta rasa ina zata saka rayuwarta ta ji sanyi.
Sosai take kuka, kasancewar babu jama'a a wajen yasa ba'a san tana kukan ba, can kashen hall É—in ta je ta zauna, wajen babu kowa sai camera dake iya É—aukar hoton wajen, murzan kukanta take yi son ranta wata kila ta huce takaici.
Kamar daga sama ta ga an miƙo mata handkerchief fari tas wanda kamshinsa ya daki kofofin hancinta har sai da yasa ta ɗan lumshe idanunta.
Waye kuma da karfin halin miƙo mata handkerchief? To bari dai mu leƙa KINGDOM OF POWER kafin mu dawo sai mu duba wanene da ƙoƙari ya miƙo mata handkerchief ɗin.
KINGDOM OF POWER 💪🔥💘
Kwance Gimbiya Chuchu take a saman bed ɗinta a cikin room ɗinta bayan an sauko daga sallar jumma'a kenan, ta bawa kofar shigo cikin room ɗin nata baya, tana maƙale da waya a kunne tana magana ƙasa ƙasa kamar wata maras gaskiya, yadda kuka san mai yin soyayya.
A ruÉ—e Gimbiya Zunaira ta shigo cikin É—akin idanunta a cike tab da kwallah, ga farin cikin idanun nata sun É—an yi ja, kwayar Hazel eyes É—in nata kuma ya kara launi sosai, da alama ta É—an sha kuka kafin ta zo room É—in, face É—inta da É—an danshin ruwa alamar ta wanke fuska kafin ta zo.
Tana zuwa ta haye saman gadon tana faÉ—in. "Aunty Chuchu ki tashi na shiga ukuna!".
A tsorace Chuchu ta juyo, dan bata yi tsammanin shigowar mutun É—akin nata ba, kuma bata ji shigowar autar ba, so hakan ya É—an tsoritata.
"Auta lafiya?!". Ta tambayeta a ruÉ—e, ta yi maganar kuma ba tare da ta cire wayar daga kunnenta ba.
Daga ta cikin wayar tata da yake hannunta Rizwan ya tambayeta da lafiya ita da waye?.
A takaice ta amsa mashi da. "Auta ce ta shigo mun É—aki babu sallama ta tsoritani, ina É—an zuwa Yah Rizwan bari mu yi magana da ita".
Da okey ya amsa mata. Cikin hanzari ta katse kiran nasa tare da ajiye wayar a gefe, sannan ta juyo da jikinta gabaɗaya ga autar. Ganin idanun kanwar tata cike tab da kwallah ga alamar ta sha kuka kuma yasa ta zaro idanu tare kuma da kara ruɗewa. "Auta lafiya idanunki suke cike da hawaye? Meyake faruwa ne?". Ta yi maganar tana miƙewa zaune.