← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 180

Sashe 132

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kai Mammie yanzu waye yake da lokacin yin wani abu wai shi aure? Ki bari idan lokacin yi É—in ya yi zamu zo, but now ayyuka sun yi mana yawa, bamu da lokacin kanmu ma bare na wata mace, just ki bari kawai.........".

Cikin hanzari ta katse shi da cewa. "Naki na bari É—in, sai fa anyi, bari ma zan turo maka hoton Chuchun sai kaga yadda ta girma ta kara kyau, nasan ma kana ganinta zaka ce ka yarda kawai daddynku ya É—aura maka aure, dan ta girma, kuma nan da two weeks kawai na baka kazo ka ganta da idonka".

A takaice ya amsa mata da. "Okey Mammie yadda kike so hakan za'ayi, yanzu dai aiki nake yi, anjuma zamu yi waya, dama nakira ne na ji ya kike? Tun da kina lafiya shikenan".

Da haka suka yi sallama, wani irin murmushi mai wuyar fassaruwa ta saki tare da miƙawa wannan kuyangar wayar, sannan ta gyara ta ɗan kishingiɗa a saman wani throw pillow dake kusa da ita, ta kai hannu ta ɗauki tuffa guda ɗaya, a hankali ta fara jujjuya tuffa ɗin tana sakin murmushi, sai Allah kaɗai yasan tunanin me take yi.

A can cikin gid kuwa, kwance Auta da Gimbiya Chuchu suke a saman bed ɗin Akka, dogayen riguna iri guda ne a jikinsu, kayan ya yi masu kyau sosai, babu ɗan'kwali a kansu, kamar kullum ɗauri biyu suka yi wa arab hairnsu, sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, sai labari Gimbiya Chuchu take bawa autar a kan yadda suka yi da Yah Jawad, sai murmushi auta take yi mata.

Jin wani daddaÉ—ar kamshin perfume ya daki hancinsu ne yasa suka É—an É—ago kai a tare suna bin kofar shigowa da kallo.

Yana tsaye ya harÉ—e hannu a kirji yana ta kallonsu, Allah ya gani yana kaunar kannen nan nasa sosai, ko su Sarina da suke uwa É—aya uba É—aya ma baya jinsu sosai a ransa kamar yadda yake son Chuchu da Zunaira, saboda kyan halinsu, sam baya shiri da Sarina, ya fi kaunar Fanan a kan Sarina, ita ta cika rashin ji ne sosai shiyasa.

Cikin hanzari suka miƙe zaune a tsakiyar gadon. "Yah Jawad good evening". Cewar auta.

Ɗan sake fuskarsa kaɗan ya yi tare da ƙarisowa cikin room ɗin yana amsa mata gaisuwar. Saman bedside drawer ya zauna tare da tambayar su ina Akka?.

Still auta ce ta bashi amsa da Akka tana fada, suna can suna zama ne a kan yakin da King Zuhair yake son su yi da wancan masarautar, so Akka tana wajen, kunsan halinta sarai ba wasa, Akka bata son wargi, akwai zafin nama, tana can tana bada shawarar ayi yaki, nan ko takobi ba iya riƙewa zata yi ba, sai baki .........😅

"Auta jeki room nawa ki kwaso mun wayoyina dukka kin ji?". Ya faɗa yana dawo da kallonsa kan fuskar chuchu da ta yi ƙasa da kai, ko gaisuwa bata ɗaga mashi ba, ta tsorata ne dan tana tunanin ya ji hirarta ita da auta, idan ya ji tasan zai hukuntata, saboda ya ce kada ta gayawa kowa ya bata punishment, amma ta zo ta bawa auta labari har da cemata ai ta tsani Yah Jawad ɗin nan, to tana tsoron ace ya ji ne, dan basu san tun yaushe ya shigo ba, ita kuma a gaskiya ba zata iya ɓoyewa auta komai ba, komai aka yi mata sai ta bata labari, haka ita ma autar take, komai sai ta gayawa Chuchu ɗin.

Saukowa kasan gadon auta ta yi tare da nufar kofar fita tana faÉ—in okey.

A hanzarce ita ma Chuchu É—in ta sauko da nufin ta fake da raka auta ta gudu.

"Come here". Ya faÉ—a a sanyaye.

Jiki ba kwari ta juyo ta dawo. Da hannu ya nuna mata saman bed ɗin ta kusa da drawer da yake kai a kan ta zauna. Ba musu ta zauna tare da takure jikinta waje guda ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Yau ba zaki gaishe ni bane Jannat?". Ya yi maganar yana mai da kallonsa a kan Æ´an yatsun hannunta dake ta faman Æ´an kerma.

"Ka yi hakuri na manta ne good evening". In a cool voice ta yi maganar.

Hannu ya kai ya riƙo ƴan hannayen nata cikin nasa. "Meyasa kike jin tsorona har haka Jannat?".

Girgiza kai ta yi tare da cewa babu komai.

"Meyasa kika gayawa auta na baki punishment? Kuma meyasa zaki ce mata kin tsaneni? Me nayi maki da zaki tsaneni?".

Yadda ya yi maganar ƙasa ƙasa kamar wadda aka yi wa dole yasa ta yi saurin ɗago kanta.

"Meyasa kika ce kin tsaneni e Jannat?". Ya sake jefa mata tambaya a karo na biyu.

Kai ta fara girgiza mashi tare ce mashi..........

*Masu tambayata cewa sunan Raj na musulmai ne koma krista, sunansa ba Raj ba ne, SURAJ ZUHAIR ABDUL MALIK yake, ƴan uwan nasa ne suka yanke sunan daga DR SURAJ zuwa RAJ, so sunan musulmai ne fatan kun gane?. Duk wani suna da na saka a cikin littafin nan suna ne masu ma'ana mai kyau, sunan larabawa ne, kuma kowanne zan rubuta maku ma'anoninsu, zaku iya sakawa yaranku idan ya yi maku.💘🌼*

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 27/8/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________39🔥

Those who are asking me for complete of RAWANIN ZALINCI babu complete ɗin, yanzu nake posting ɗinsa, hakuri zaku yi ku cigaba da bibiyar su Kamran ɗin nan har muga me Allah zai yi🥱 much love my people's 💘🔥

"Meyasa kika ce kin tsaneni e Jannat?". Ya sake jefa mata tambaya a karo na biyu.

Kai ta fara girgiza mashi tare ce mashi. "A'a ban tsaneka ba Yah Jawad".

"Amma ai na ji da kunnuwana kin cewa auta baki sona, duk cikinmu ni kika fi tsana why?".

Shiru ta yi bata da bakin magana, ta kuma kara yin ƙasa da kanta sosai. "Ɗago idanunki ki kalleni sai ki bani amsa ta ko?".

Bata iya É—ago idanun nata ba, sai dai ta ce mashi. "Ka yi hakuri ba zan sake ba, kuma ni na dai'na tsanar taka daga yanzu".

"To amma me nayi maki da yasa tun farko kika fara tsanar nawa?". Ya kai karshen maganar tare da sakin hannunta guda ɗaya, ya kai hannun nasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna.

Ƙasa ta yi da idanunta tare da yin shiru. "Me na yi maki tun farko Jannat da yasa har kike ikirarin kin tsaneni?".

Ɗan turo baki ta yi kafin ta amsa da. "To Yah Jawad ba kai ne kake saka ni kneel down ba, kuma sai ka rinƙa ja mun ga shi kan......". Shiru ta yi ta ƙasa ƙarisa maganar sakamakon ji da ta yi ya saki ɗayar hannun nata ma, a tunaninta wani laifi ta sake yi yasa ya saki hannun nata zai daketa.

"Shi ne yasa kika ce kin tsaneni ni?". Yana magana yana kara ɗago haɓarta da kyau.

Kai kawai ta gyaÉ—a mashi alamar e. "Okey to buÉ—e ido mu yi magana". Ba musu ta É—an buÉ—e idanun nata, sai dai taki yarda su haÉ—a ido.

"Am so so sorry da punishment da na rinƙa baki, na yi haka ne nima ba'a son rai na ba, amma ki mun alƙawarin abu guda ɗaya, ni ma kuma ba zan sake baki punishment be kin ji?".

ÆŠago idanu ta yi zata saci kallonsa, sai ta tarar da ita yake kallo. "Na yi maka alkawari In Sha Allah". Ta amsa mashi tun ma bata ji me zai ce ba ko akan me zata yi alkawari ba ta riga da ta yi.

Shiru ya yi bai gaya mata alkawarin me yake son ta yi É—in ba, tun da ta amsa mashi da ta yi sai ya kawar da zancen da cewa. "Kada ki sake cewa kin tsani wani daga cikin gidan nan, bama ni ba koma waye, mu ba Æ´an uwanki bane? Idan kika tsanemu to su waye zaki so? Amma tukun nan ma anya Jannat kin san me kalmar tsanar nan take nufi ma kuwa?".

Shiru ta yi tana tunanin ya zata gaya mashi yadda ta É—auki tsana a nata tunanin.

"Me tsanar mutun yake nufi?". Ya jefa mata tambaya yana sakin haɓar tata ya koma ya riƙo hannayen nata a cikin nasa kamar ɗazun.

"Tsana yana nufin kamar idan mutun yana yi maka abin da baka so sai kana jin babu daɗi sai kawai ka tsane shi". Ta bashi amsa a kwakkwaɓe. Sai yanzu ma ya fahimci ita bama ta san ainahin menene ma'anar tsanar ba, haushin mutun shi take ɗauka a matsayin tsana, tsana kuma daban jin haushin mutun daban, mutun zai iya yi maka abin da baka so a lokacin ka ji haushinsa, daga baya idan ka huce komai ya wuce ku koma normal, shi kuma tsana daga zuciya yake, idan mutun ya tsaneka da gaske to mawuyacin abu ne ya dawo daga baya ya soka ko me zaka yi mashi kuwa.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da É—an matsowa kusa da ita kaÉ—an, sannan ya kai hannunsa É—aya yana shafa arab hairnta. "Da ga yau ba zan sake baki wani punishment ba, amma kema ki dai'na yin duk wani abin da bana so kin ji?".

Cike da murna ta ce. "Da gaske Yah Jawad ba zaka sake bani wani punishment ba?".

Kai ya gyaɗa mata alamar e. Cikin sauri ta faɗa jikinsa tana dariya, kamar ba ita bace yanzun nan take ƙoƙarin saka mashi kuka, Allah sarki ashe wannan punishment ɗin da yake bata abin yana matuƙar damunta, yana yi mata ciwon da kullum yana ranta, to yau dai an dena, ai sai murna kawai.

ÆŠan rungumeta kaÉ—an ya yi tare da cewa. "To ai ni kuma baki tambayeni me bana so ba domin ki dai'na aikatawa".
Chapter 132 · 0% Book details