Sashe 178
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waje Sharifat ɗin ta nufa, ita kuma Leesharh ta nufi cikin toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah, bayan ta idar ta sanya hannu ta taɓa aljihun wandanta dan ta tabbatar maganin yana ciki.
Jin cewa yana ciki yasa ta saki cool murmushin da bata san lokacin da ya fito ba, faÉ—i take yi a cikin ranta shikenan da ta zuba mashi maganin nan masu nikaf zasu haÉ—ata da babanta ta yi magana, yau tsawon shekara kusan biyu bata ji muryarsa ba, tana kewarsa sosai, tun lokacin da aka kaita prison ta kashe mamanta, tun ma kafin lokacin take kewar muryarsa, sun É—an kwana biyu basu a tare, shiyasa take É—aukin jin muryarsa, take begen hakan.
Sallamar Sharifat a cikin ɗakin yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. Ɗago idanun nan nata ta yi tare da saukesu a kanta, rike take da katon luxurious tray, shake yake da kulolin abinci masu bala'in kyau da tsada, ga cup dake shake da cappuccino, sannan ga cup na coffee mai zafi a gefe, duk suna rufe da ƴan ƙananan plate na set ɗin cup's ɗin. Sai sauran snacks dake saman wani luxurious plate.
Zubawa trayn idanu ta yi tana kallonsa sosai, ayyana yadda zata zuba mashi maganin a ciki kawai take yi. Muryar Sharifat É—in ce ya katseta da cewa. "Let's go Leesharh".
Miƙewa ta yi suka jera a tare.
Allah sarki tausayin maraicin Leesharh da Sharifat take yi yasa zata tabka kuskure ba tare da sanin ta ba, burinta ta ja Leesharh É—in a jiki ta yadda zasu saba sosai, duk dan ta mantar da ita damuwar da take ciki na rashin iyayenta, tana son su saba sosai su zama kamar Æ´an uwa, shi ne harda gayyatota ta rakata wajen Æ´an uwanta. Hmmm bata san aiki dama ta zo yi a kansu ba, rashin sani ya fi dare duhu.
A tare suka tafi, cikin dabara Leesharh ta ciwo maganin daga aljihunta, ko tsoro bata ji ba, kamar mai son gyara zip ɗin wandonta haka ta yi ta buɗe ɗan gwalbar ganin. Sai da suka shiga wajen wannan ɗan hanya in da ta yi karo da mai aikin ɗazun ɗin nan, kun san wajen akwai ɗan duhu. Saboda jajircewa da karfin hali haɗe da ƙoƙari irin nata, ga taurin zuciya da rashin tsoro, cikin dabara ta kai hannu ta bude plate ɗin cappuccino ba tare da Sharifat ta jita ba, sai hira Sharifat ɗin take zuba mata, tana bata labarin kyan Yah Ramish ɗin.
A hanzarce ta zuba maganin kaɗan a ciki, ta sake zubawa a cikin coffee ɗin ma kaɗan sabosa ƙoƙari irin nata. Tana yi kirjinta na dukan tara tara, ita kuma Sharifat sai surutu take zubawa suna tafiya a hankali cikin natsuwa, saboda girman tray ɗin yasa bata ji an taɓa komai ba.
Kaɗan kaɗan ta zuba maganin kamar yadda suka umarceta, ta yi maza ta dunƙule kwalbar a hannunta kasancewar sun fito wajen haske. Fargaba da faɗuwar gaba ne ya kusa kasheta, zuciyarta sai bugawa da karfi karfi yake yi, da kyar ta haɗiyi yawun wahala, wani irin jan numfashi da ta yi har sai da tasa Sharifat ɗin ta ɗan ci birki tare da tambayarta lafiya kuwa?.
Cikin dakiya ta ce babu komai su je kawai, duk a ruɗe take, gabanta na faɗuwa, sai karanto addu'oi take yi dan ta ji sassauci a cikin zuciyarta...... Kai Leesharh ba dai karfin hali da dakiya haɗe da taurin zuciya ba, kai irin wannan ɗanyen aiki haka? Ko tsoron asirinta ya tonu bata ji yarinyar nan, idan ta sa kanta zata yi abu, to fa sai ta yi. Ashe ba'a banza masu nikaf suka ɗaukota ba, ashe sun san wa suka ɗauko, yo dama Allah na tuba mu jinin ƴan Nigeria ai fin haka ma zamu aikata ba tare da tsoro ko shakka ba, ai mu karfin halinmu tare da jajircewa a jininmu yake, dan haka kada ku yi mamakin idan Leesharh ta aikata fin haka, yauwa jininmu a tafashe yake, babu abin da baza'a samu a Nigeriarmu ba, mu ai ba'a isa a mana gorin komai ba ato...........🥱
(Jinjina gareki Leesharh jikar baba bola Ahmad tinunbu🥱 kina da karfin hali irin na jikokin tinunbu,🔥 kin ci lambar ya bo, dole villa ta san da zamanki, irinki ake turawa aikin soja🥱)
Cigaba da tafiya suka yi. Sun É—anyi tafiya mai nisa kafin su kai bakin haÉ—aÉ—É—en katafaren part É—in nasu.
"Leesharh ki jirani a nan ina zuwa". Ta faɗa tare da nufar cikin part ɗin. Ita kuma Leesharh ta tsaya a bakin stair case da ya yi ƙasa.
Shiru ta yi tana tunanin me zai faru idan bawan Allah Ramish ya sha wannan maganin?. Tana son buɗe hannunta ta kalli maganin, amma tana tsoron yin hakan, dan tana zargin wajen da take ɗin da akwai camera. A hankali ta fara jiyo takun sahun mutun yana haurowa saman stair case ɗin, kuma daga jin wannan taku kasan bana ƙananan yara bane. Wani irin tsoro ne ya kamata wanda yasa ta watsa a guje ta bar wajen, kai tsaye hanyar da suka bi suka zo ta nufa.
Ita kuwa Sharifat ta kaiwa yayan nata cikin parlournsa, yana zaune saman sofa, jikinsa na sanye da hoodie mai bala'in tsada launin milk color, ya sanya hular rigar a kansa, kasancewar hular rigar ta gaba akwai gashi gashi kamar jikin mage, hakan yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ya yi matuƙar kyau sosai a cikin kayan, sai dai kayan kusan kalar fatarsa ce. Kyawawan fararen ƙafafunsa na'a saman haɗaɗɗen carpet ɗin tsakiyar parlourn mai bala'in laushi, ya mike kafafun yana latsa waya, da alama shirin fita ya yi abincinsa kawai yake jira.
A gabansa saman center table ta É—aura tray É—in, cikin girmamawa ta ce "Yah Ramish ga abincin nan".
Ajiye wayar ya yi a gefensa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kai hannu ya ɗauki cup ɗin cappuccino ya fara sha. Ita kuma Sharifat ta zauna a gefensa saman sofan da yake ɗin tana faɗin. "Yah Ramish fita zaka yi ne?". Da alama ta mance da cewa ta ajiye Leesharh a bakin kofa tana jiranta.
Kai kawai ya gyaÉ—a mata alamar e fita zai yi ba tare da ya yi magana ba. Cikin nutsuwa ya fara shan cappuccino. Ita kuma ta mayar da hankalinta kan Tv dake magana.
Tas ya shanye cappuccino kafin ya miƙe ya nufi cikin master room ɗinsa. Dawo da kallonta kansa ta yi tana son ta tambayesa ba zai ci abincin bane? Sai dai kafin ta tambayesa ya wuce cikin ɗakinsa.
Jiransa ta yi har sai da ya fito sanye da haɗaɗɗun takalma a ƙafafunsa, wayarsa ya zo ya ɗauka. "Ki barmun abincin a nan sai na dawo zan ci". Ya faɗa a sanyaye tare da nufar waje da sauri.
Kafin ta amsa mashi da okey ma ya fice. Sai lokacin ta tuna da cewa Leesharh na waje ga kuma Ramish zai fito, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, dama dayawan lokuta idan ta kawo mashi abinci yin zamanta take yi a part ɗinsa, wani lokaci ma har barci ya ɗauketa, idan da daddare ne ta yi mashi barci a ɗaki sai lokacin da ya gama abin da yake yi sai ya mayar da ita room nata, idan su Bilal sun shigo kuma sai ya ce su mayar da ita. Magana ta gaskiya Sharifat tana son Ramish sosai, shi take burin aura, sai dai shi bai san da hakan ba, kuma babu hakan a gabansa, ita kuma ta kwallafa rai a kansa sosai, shiyasa take son zuwa in da yake, idan tana wajensa mantawa take yi da kowa da komai........,....... Lallai kuwa Sharifat tana kwale kwale, amma kuma idan ta ce shi take so anya zai iya yi wa Abu Abdussalam musu kuwa?🤔 Amma kuma ina tausayawa Sharifat gaskiya, dan son wanda baya sonta take yi, wanda ma bata isheshi kallo ba, kai suma dai da nasu cakwakiyar kunji my people's, mu fita harkarsu, kowa ma da nashi cakwakiyar a littafin nan, yanzu kuma kowa zai fara buga wasansa iya wasa, yanzu game zai fara, zamu ga winners, idan kun ji ana cewa tseren mutuwa to wannan cakwakiyar na cikin littafin nan ne, yanzu dai zamu afka cikin ainahin labarinmu da kuma cakwakiyoyinmu kala kala.
A ɓangaren Leesharh kuwa, tana watsawa a guje ta nufi hanyar koma ɗakinta. Dai'dai zata fita cikin wannan ɗan siririn hanya mai ɗan duhun suka ci karo da mutun, hakan yasa kwalbar maganin hannunta ya faɗi ƙasa ya fashe. Wani irin baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa.
Da kyar ta iya riƙe kanta ta tsaya, goshinta ya bugu da nashi ne sosai. Kirjinta kara tsananta bugu ya yi saboda tsoro da tunanin da waye ta yi karo? Ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, shikenan asirinta ya gama tonuwa, yanzu idan aka ga maganin kuma idan wani abin ya sami Ramish kashinta ya bushe!.
Shi kuwa Obaid da farko ya É—auka da Sharifat ce suka yi karon shiyasa bai yi saurin dalla mata mari ba, sai da ta É—an ja baya ya gane ba Sharifat bace, cikin fusata ya matso tare da sharara mata wani gigitattacen mari a karo na biyu wanda ya sanyata dai'na gane komai.
Wani irin azaba ya ji a ƙafarsa lokacin da ya matsa kusa ya mareta, ba komai ne yasa hanan ba kuma face taka kwalbar maganin da ya fashe ya yi, ƙafafunsa suna da laushi sosai, hakan yasa kwalbar ta yi saurin fasa mashi namar cikin tafin kafar tasa ta shige ciki. A hanzarce ya kai kallonsa kasa kan...............
To fa akwai cakwakiya, Ramish ya sha maganin nan! Ko maganin menene? Ga Obaid kuma ya kara dallawa Leesharh mari a karo na biyu! Da alama asirin Leesharh zai tonu! Dama kunsan Obaid yana zarginta, ya kuma kafe lallai lallai ita mai laifi ce abar zarga, ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, bugu da ƙari ya fasa mashi kafa, akwai cakwakiya ba kaɗan ba, dama da Guyson suka ci karo ne, to da da sauki, amma Obaid fa, tab Leesharh kina ruwa wlh, sai dai muce Allah ya ceceki!..
🕊ï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸
FORESTðŸžï¸ 🔥