Sashe 136
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗagata sama ya yi tare da maida ita bayansa, ya goyata kamar yadda suka zo, dan wannan yarinya ba iya tafiya da kafafunta zata yi cikin bishiyoyi da ciyayin nan ba, sai ta ɓata masu lokaci basu isa in da za su je ba, kuma dama shi Kamran yana jin daɗin goyata idan zasu je yawonsu, saboda hakan zai sa su yi tafiya mai nisa ba tare da ɓata lokaci ba.
Nufar hanyar komawa suka yi, ta kwanta shiru a bayansa tana rawan sanyi, ta wani ƙanƙame mashi wuya. Shi kuma sai tafiya yake yi.
Ko da suka isa bakin ramin nasu sai ya sauketa, miƙo mata wani irin nau'in fruit nasu dake a cikin dajin mai kama da ruman mai kuma kama da Apple haka yake ya yi, ya miƙo mata tare da cewa. "Ina sonki sosai Pretty, ki koma ki cire kayan jikinki ki canza wasu kada sanyi ya kamaki, nima zan je gida, sai gobe, kada fa ki sake fitowa, gobe za mu je yawo sosai".
(Ko a ina ya samo wannan fruit ɗin?🤔 Kila a hanya ya ciro da suna dawowa)
Karɓar fruit ɗin ta yi tare da cewa. "Nima ina sonka Kamran, amma fa gobe kazo da wuri ka ji?".
Jinjina mata kai kawai ya yi, sam baya son rabuwa da su, ji yake yi a wannan yanayi kamar kada ya koma gida, amma ina babu dama, ba hali dole ya koma idan yana son cigaba da kasancewa da su.
Shiru ya É—an tsaya ya kasa tafiya.
"Kamran lafiya ka tsaya shiru? Ka tafi mana". Ta faÉ—a tana kallon face É—insa.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan ƙaƙalo murmushi kaɗan. "Babu komai Pretty, kawai ina tunanin rabuwa da ku ne, bana son komawa gida na barku".
Shiru ta É—an yi itama, jikinta ya yi sanyi, har ga Allah bata son rabu da shi ita ma, amma ya zasu yi? Dole su rabu, idan ba haka ba su jawa kansu rabuwa ta har abada.
"Nima bana son ka tafi Kamran, nafi son kullum ka kasance a tare da mu, idan ka tafi bana jin daÉ—i, ina jin kamar bani da lafiya, duk sai in ji wajen zamanmu ya yi mun zafi babu daÉ—i, shiyasa ka kallah ina fitowa waje in zauna idan baka nan, bana jin daÉ—in zaman cikin ne". Tana magana kamar zata yi kuka.
ÆŠan rungumota a jikinsa kaÉ—an ya yi tare da shafa kanta dake ta zubar da ruwa. "Idan nazo gobe zamu yi magana, yanzu kinga kije ciki kada sanyi ya kama mana ke, ki canza kaya kin ji ko? Ki gaishe da Sweetie sosai".
Rungume shi ita ma ta yi kafin ta sake cewa. "Goben fa kada ka daÉ—e, kazo da wuri".
Okey ya amsa mata da shi, sannan ya saketa tare da ce mata ta shiga ciki. Ba musu ta shige ciki, sai dai ta shige ne tana ruwan hawaye, kuma ya lura da hakan, kawar da kansa kawai ya yi, saboda dalilai guda biyu, na farko baya son ya cigaba da tsayar da ita cikin ruwan nan ga kuma É—anyen kaya a jikinta, sanyi zai kamata, na biyu kuma baya son kara jan lokaci da su kada mamma ta tashi daga barci ta farga baya nan, hakan yasa ya kawar da kai tamkar bai ga tana kuka ba, amma ya ji zafin hakan sosai a cikin zuciyarsa, sai ya ji kamar shi ma ya yi kukan ko zai É—an ji sanyi a ransa.
Haka ya juya jiki ba kwari ya nufi nasu gidan, yana tafiya yana tunanin hanyar da zai bi ya isa ga mutanen dake wajen dajin nan, sannan yanzu kuma tunanin mahaifinsa ta yawaita mashi a cikin zuciyarsa, ji yake yi lokaci ya yi da yakamata ya tambayi Mamma ina babansa? Tun da yanzu ya gano cewa ba iya macece kawai take haihuwa ba, dole yana da baba, to ina baban nasa? A gaskiya yakamata Mamma ta gaya mashi in da mahaifinsa yake, kullum da wannan tunani yake kwana kuma yake tashi, sai dai ya rasa ta ina zai fara tunkara Mamma da zancen. Tashin hankali kenan.
Tafiya yake yi sam bashi da wani kuzari a jikinsa, da haka ya isa gida. Yana zuwa ya wuce nashi makwancin, kayan jikinsa ya fara kwaɓewa tas. Yana da kyan jiki kam kamar madara duk da Mamma ta fishi haske nesa ba kusa ba, da alama babansa ya yo a kalar fata, fari ne fa shi ɗin ma, amma a gaban mamma gaskiya ba fari bane.
Canza kaya ya yi tare da kwashe waɗan nan ya kai su in da suka dace, ya sanya kaya masu nauyi sosai saboda sanyi, sannan ya kwanta ya ɗauko Alqur'ani da ya ɗauka wajen su Pretty ya fara dubawa yana karantawa, bai leƙa Mamma ba. A lokacin ita kuma ta tashi daga barcin tana cikin madafarta, tana aiki, tasan da cewa ya fita bayanan, domin tana farkawa daga barci makwancinsa ta fara leƙawa dan ta duba shi, sai ta taras baya nan, so bata wani damu ba, dan dama da lallami ta lallaɓa shi ya dawo, so ba zata takura mashi ba.
🕊ï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼
GIDANSU KHADIJAH😥💔
Maman Khadija tana durkushe a wajen tana kuka Khadija na rarrashinta, bata tashi daga wajen ba sai ji ta yi an sake banko masu kofar gida.
Bata kula ba, haka zalika bata bi ta kan son sanin su waye bane, ita masifar da take a ciki ma ya isheta, dan haka sai ta cigaba da rera kukanta da sauti baya fita sai dai ruwan hawaye.
Banko labulen kofar aka yi aka shigo, maman Haidar ce da Maman Hanif sai Hajiyarsu, Haidar yana tsaye daga bakin kofa, shi ma Sadiq ya fito ya tsaya a bakin kofar É—akinsu yana kallon cikin parlourn, abin da ya fito da shi kuma shi ne irin yadda ya ji sun banko masu cikin gida babu mutunci, so yana tsoron kada su yi wa Æ´ar uwarsa wani abin, shiyasa ya fito, shi dai yana ganin bala'i kala kala bawan Allah, daga nasu maman Haidar yanzu kuma an koma na Hauwa, wannan irin jarbawa sai ka dage zaka iya cinta, Allah yasa maman Zee tana da juriya da karfin imanin iya cinye jarabawarta.
Tana durkushe tana kuka maman Haidar ta fara surfa mata ruwan bala'i a kan ina su Hauwa É—in suke? Ta fito masu da baban Zainab ita kuma.
Wani irin kallon takaici mai haɗe da tsananin ɓacin rai maman Zee ta wurga masu. Cikin ɓacin rai da fusata ta ce. "Saboda ni kuka raina shi ne dan kinga ni kaɗai ce zaki fara mun hargagin banza ko? Meyasa ɗazun da kika samu Hauwar baki yi mata ba kika yi shiru? Yanzu dan kinga bata nan ne zaki ce na fito maku da baban Zainab? To na cinye shi ɗanya, sai ku fasa cikina ku ciro shi!!". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye, idanunta jajir kamar wuta, yau tasha kuka, kuma a cike take har wuya da bakinciki, idan su maman Haidar suka yi wasa tana iya yi masu hauka, dan Hauwa ta sanya zuciyarta yanzu ya fara bushewa ta dai'na ganin mutuncin kowa, zuciyarta ta kusa fashewa ta fito waje. Tashin hankali, yanzu wasan zai fara!!.
"Ke Aisha ni kike gayawa magana yau? Ni nake magana kike mayar mun da amsa? A lallai kam kan mage ya fara wayewa". Cewar maman Haidar.
"Ke ɗin nake gayawa, an gaya maki ɗin, zaki iya yin duk abin da ya zo maki cikin wannan banzar ƙwaƙwalwar taki, sannan kuma ke dama a tunaninki rashin wayewa yasa bana mayar maki da martanin duk abin da kika yi mun ko? Ko kina tunanin ina jin tsoron ki ne? To idan ma haka kike tunani kin makaro, tarbiya da ilimi dana samu daga wajen iyayena ne yasa nake darajaki a matsayinki na yar miji, nake baki girma kamar yayata uwa ɗaya uba ɗaya, nake kuma ganin mutuncinki, amma yanzu tun da abin yazama babu mutunci, to kuwa zaki ga ainahin wacece A'isha! Yanzu baki isa kiyi mun na kyale ki ba wlh, a baya kin ci banza, amma yanzu zan nuna maki ba wai ban iya rashin kunyar bane, tarbiya muka kwankwaɗa muka ƙoshi, a gidanku kuma kuka shayar da ni ruwan kwatar ƴancina, to yanzu na sha na ƙoshi, duk wanda ta shirya mu buga to ta zo mu buga daga nan har illa Masha Allah, in dai bata gaji ba, to nima ba zan gaji ba! Duk wadda ta ce mun kule sai na ce mata cas, na dai'na yin shiru tun ba mutuncin kuke so ba!!".
Shiru ita dai maman Hanif ta yi, dan ita dama ba wai ta cika shiga irin wannan shirgin bane, kawai ba yadda ta iya ne, idan maman Haidar ta yayuɓota dole ta biye mata, ko dan ma Hajiyarsu, idan bata shigarwa maman Haidar ba ya zama dole ta shiganwa Hajiyarsu.
Gadan gadan cikin fushi maman Haidar ɗin ta nufeta da nufin ta kai mata mari. Ai kuwa maman Zee bata yi ƙasa a gwiwa ba ta yi cap ta rike hannun nata.
"Wlh idan kika kuskura kika ɗaura hannunki a jikina sai na rama, ashe rashin kunyar taki sai kinga wargi kike yi, meyasa baki yi wa Hauwa ba? Kika yi shiru ta gama cin maki mutunci baki da wani kataɓus! Meyasa kika ja baki kika yi shiru a gabanta? Sai ni zaki yi wa hargagin banza? To nima na dawo daga rakiyarku wlh!!".
Ƙoƙarin kwace hannunta ta fara yi, amma ina maman Zee taki sakar mata hannun, ji take yi ma kamar ta kife munafuka da mari, so take ta sauke haushin da Hauwa ta cusa mata a kansu.