← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 58

Sashe 9

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba É—aya kaina ya kulle da wannan lamari dik jikina ya jike da zufa shin wani abunne wannan da uwata take tsoronsa gareni har tasa take boyen shi? bani da mai bani amsar hakan dan haka shiyasa naja kafata na koma da baya har na futa.

Babu yadda ABDUL bai dani akan yazo ya gaida umma ba a yau amman naki basa dama saboda bana jin dadin jikina sam.

Hirarma tayau gata nan dai haka mukai muka gama.

Kuma ikon ALLAH koda na koma ciki banga wani tashin hankali a fuskar umma ba dan haka nima na saki raina na manta da wannan maganar danaji sunayi tunda nasan may be bata shafeniba.

Alhmdh yau laraba yau aka kawo kudin aurena da saka rana ta da ABDUL wai abin da yabani mamaki shine yadda abba ya amince a wata gudan da suka zo dashi kamar ya gaji dani wallahi har kuka nai dan haushi.

Haka dangi suka cika gidanmu kamar ana biki anata shagali nidai ina daga ɗaki nidasu mufida ƴaƴan gidan yayan abba alhaji ƙarami se tsiya sukemin nidai bance musu komai ba haka nai kwance ina tunanin ABDUL ɗina.

Gidanmu bai bar ganin jama,aba seda aka ci sati guda ciff da kawo kudina sannan aka tsagaita da zuwa murna abinka da É—an dangi.

Babu laifi suma Æ´an uwan ABDUL sun nuna min so domin kuwa dik yanzu ina kiransu a waya muÉ—anyi hira dasu.

Kuma har Æ´an É—akin suma ya kawomun su mun gaisa nima kuma naje gidansu da daddare harda ummi da amira suka rakani naga hajiya mahaifiyarsa sedai dady ne baya nan yay tafiya kuma wallahi seson barka domin na sami goma ta arziki agidan sosai.

ikon ALLAH dik ƴan gidan baban abuja sun kirani a waya sunmi ALLAH sanya alkairi amman babu ɗan ɗakinsu ya hydar ko guda akiran nawa abin ya bani mamaki kuma na jinjina wannan ƙiyayyar amman ban damu ba saboda nasan daman momy bazata barsuba.

BAYAN SATI UKU.

shirye-shirye ya kam kama ta kowani ɓangare nifa senace ma har ƴan gidansu ABDUL sunfimu zumuɗin wannan lamari duba da yadda naga suna addabata da waya akan yadda za,a gudanar da events ɗin bikin da sauran abubuwan ni watarana ma abin har kunya yake bani wallahi.

Idan ka dubeni bazaka iya kauda kanka ba sabida yadda naci uban gyaran amare awajan HAJIYA ZARAH mai kayan mata takanas anty zee ta É—aukomin ita tun daga garin GUSAU tazo da kaya kala-kala na gyara ko ina domin jin dadin ango cewar ta ita da kanta anty zarahn.

Agidan anty zee na tare gaba É—aya wuni ake ana faman yimin dilka da halawa da sauran gyara ni kaina idan na kalli kaina farin ciki nakeyi sabida yadda na koma kamar wata black amerincan.

Babu yadda ABDUL ya iya sabida anty zee ta dakatar dashi zuwa wajena domin kuwa idan ba,ai wasaba ze iya ɓata mana aiki dan wannan gyaran na musamman ne dole se anaja baya baya da namiji sabida tsaro.

Kullum mukai waya dashi seyay min complain akan yana missing É—ina wataran har gwalo nake masa haka zeji haushi ya kashe wayar amman dayake maye ne gobema seya kirani.

Yau Alhamis yau muka fara events É—inmu anyi kamu washe gari juma,a akai mothers day, nan ma babu laifi anyi casu Æ´an uwa sunmi rawar gani musamman ma yadda naji ana zuzuta É—akina yadda abba ya zuba kuÉ—i abin seson barka sabida daman tun ana sauran sati biki sukai min jere anan rijiyar zaki.

Gidanmu babu masaka tsinke sabida yadda dangi sukai masa caaa!!

Danni kam da gyar na kutsa É—akin umma sabida yadda nakejin gajiya kamar na mutu ga uban ciwon kai.

Ikon ALLAH acikin É—akin umma harda momynsu ya hydar da matarsa anty maryam da Æ´an gidan baban abuja dik sunzo baki É—ayansu ni wallahi bamma saniba ashe sunzo.

Ƙarasawa nai na gaida kowa na ɗakin amman momy bata amsa min ba wanda daga ganin face ɗinta kasan seda akai babu dadi sannan tazo bikin.

Da yake nasan matar ya hydar a hoto shiyasa na ƙarasa muka gaisa da ita kuma babu laifi ta sakar min fuska itakam dan har tsokanata take daga ƙarshema tace na samo mata kunu dan ALLAH zata sha.

Fita nai waje tare da umartar ummi takai wa anty maryam kunu nikuma nai ciki tare da kwanciyata a É—akinmu gobe É—aurin aure da dinner daga nan kuma se gidan ABDUL.

Tunda na tashi yau nakejin babu dadi ga ciwon kai nidai haka naja jikina nai wanka ina fitowa na koma kan gado na saka kuka wiwi.

Seda anty zee tajani mukai É—akin umma nan ma rungume umma ina mata kuka nan fa Æ´an uwa sukaimin ca mai tsokana nayi mai hoto nayi.

Babu abinda momy take se jan tsaki daga karshema ta saka matar É—anta da sauran Æ´aÆ´anta agaba suka bar dakin gaba É—aya.

Sukam su mama dasu akaita bani baki har anty zee ta janyeni mukai can cikin gida domun ta shiryani.

************
Acan cikin gari kuwa unguwar yakasai babban masallaci ya cika taff da É—an adam! liman ya tashi domin sheda daurin auren FATIMA KABIR UBA YAKASAI DA ANGONTA ABDUL.......!!

Dakata malam!! dakata!! cewar wani babban mutum kenan dayake kutso kai cikin masallacin.

Da sauri ABBA! BABAN ABUJA! ALHAJI ƘARAMI dama sauran ƴan uwa suka mike tsaye suna bin mutumin daya shigo cikin masallacin da kallo batare dasunce komai ba.

Wallahi!! tallahi indai nine uban daya haifi ABDUL to ban amince da wannan aure ba....!!

Bazan taɓa yarda ba!!!! da sauri abba ya ɗago kansa yana zubawa mutumin ido cikin tsananin tashin hankali.

Eh kabiru kalleni da kyau kada kaga kabar unguwarmu kadawo nan tofa ka tuna shi wannan abin dake bibiyar AHALINKA har abada zeta binka ne aduk inda zaka kasance!!! dan haka babu wannan aure sam É—ana baxe auri Æ´arkaba!!!

zaman dirshan abba yay tare da saka kuka ABDUL cikin sauri yayo kan mahaifinsa yana tambayarsa amman inna tuni yasaka wasu ƙarti sunyi waje da ABDUL ɗin.

Shima tuni ya take musu baya yabar jama,a da tambayar abin dake faruwa.

Cikin fushi baban abuja ya kalli liman tare da cewa.....

Meyasa wasu mutanen kan son tozarta Æ´an uwansu musulmine?

Innahlillahi wa'innah ilaihirraju'un.

Liman sake shaida ɗaurin auran nan ya koma kan ɗana nina san *KO BABU SO* atsakanin ALIYU DA FATIMA tofa akwai *ƘAUNA* ta jini ɗaya!!!

kuma mu zamu É—auki kaddarar data hau kan fatima dik da haka domin hannunka baya rubewa ka yanke ka yar.

Cikin minti goma dubban jama,a suka shaida ɗaurin auren CAPTAIN ALIYU MUHAMMADU UBA YAKASAI DA FATIMA KABIR UBA YAKASAI cikin sadaki mafi daraja da Najeeb abokin hydar ya wakilci abokin nasa ya bayar wanda shi yana can ABUJA bai san wainar da ake toyaba😳😳

Da ƙyar su baban abuja suka ɗaga abba sukai mota dashi yana faman gunjin kuka sabida yasan tashin hankalinsa lafulane akan na matarsa da ita kanta ƴar tasa wadda bata san wace ƙaddara ce ke yawo ajikinta ba.

Acikin minti goma da wani abu har labari yakai cikin gidan su batula dama cikin unguwarsu baki É—aya.

Ahau kace momy ta saki wata razananniyar ƙara tare da zubewa a sume saboda jin wannan mummunar jarabar da aka liƙawa ɗanta.......!!tabbas jarabace auran batula da hydar itakam an cuceta!!!

Inalillahi wa'innah ilaihirraju'un cewar.....!!

*MENENE YASA BABAN ABDUL YAƘI AMINCEWA DA AURAN NAN*?

*WACE ƘADDARAR CE TAKEBIN AHALIN ABBA DA UMMA HARTASA SUKA BAR TSOHUWAR UNGUWARSU SUKA DAWO NAN*?

*YAYA AURAN BATULA DA HYDAR ZE KASANCE*?

*TASHIN HANKALIN WAYE ZEFI TASIRI NA MARYAM MATAR HYDAR KONA MOMY MAHAIFIYARSA KONA SA SHI KANSA WANDA BAI SAN WAINAR DA AKE TOYAWA BA*?

*WANI HALI ABDUL ZE SHIGA*?

*YAYA LAMARIN BATULA WADDA BATA SAN KOMAI DAN GANE DA WANNAN LABARIN BA*?

*SHIN TAKA MAI MAI MA MAYE WANNAN ABIN DAKE BIBIYAR AHALIN ABBA WANDA YA SHIGE WA KOWA DUHU HARTASA AKA FASA ƊAURA AURAN ƳARSA*?

MY FANS WANNAN SALON FA NA DABANNE AKWAI HARGITSI ACIKIN PAID GROUP.

AKWAI LOVE AKWAI SARƘAƘIYA AKWAI TAUSAYI AKWAI TSAYAWA ARAI.

AKWAI GWARAMA TSAKANIN BATUL DA ALIYU FA.

YAYA RAYUWAR BATULA ZATA KASANCE NAN GABA AGIDANSU hydar ga ƙiyayyar momy gata kishiya ga uwa uba shi kansa mai kankat ɗin

Tabbas akwai babbar tafiya acikin wannan littafin gaskiya akwai salo kala kala a wannan tafiya kedai hanzarta siyan naki kada ki bari ya huce da tururunsa!!!

*WANNAN SHINE LAST FREE PAGE GAMAI SO YAYMIN MAGANA DOMIN SAMUN CIGABANSA*

*LAST FREE PAGE*

*14 - 15*

"Innah lillahi wa'innah ilaihirraju'un" cewar É—iyar momy ta biyu hafsa mai bima Hydar tare da nufar inda momy ta zube aguje tana faman sakin ihu! wanda shiya jawo hankalin sauran mutan gidan waÉ—anda suka halarci bikin.

Cikin wani irin yanayi hafsat take jijjiga!momy gami da furta "Dan ALLAH momy karki mutu ki barmu wallahi wannan auran ma sunan sa rusash she tunda baza,a liƙa mana ƙarbai ba dan ALLAH momy kita shi pleaseeee!!" hafsat takai maganar tana mai zama a kusa da momy itama cikin haka sauran yaran momyn suma suka shigo gidan aguje nan fa waje ya kaure da koke!-koke.!

Daƙyar wasu daga cikin matan ƴan uwa suka ɗaga momy wadda batasan inda kanta yake ba sukai ɗakin abba da ita tunda shine babu jama,a acikinsa sosai.

Itakam maryam matar hydar bata masan ana yiba tunda tana can gidan wata aminiyar momy tada tura ta can wai ta huta acewar momy É—in.

Cikin tsananin tashin hankali Hanif mai bin ummi ya shigo tare da nufar ɗakin umma aguje yana haki jikinsa sanye ike da farar shadda ƙar wadda Abba ya dinka musu ta ɗurin aure da ƙyar ya sami damar kutsawa cikin ɗakin gadon umma wanda tsabar dangin umma da suka cika wurinne ya sa da ƙyar ya samu damar samun shiga.

Hango ta yay zaune a gefen gado taci uban ado tana magana da wata ƴar uwarta daga ganin umma kai kasan dik wannan dambarwar bata san ana yintaba duba da yadda taci uban ado na kece raini bazaka taɓa cewa ma itace uwar batula ba sabida yadda ALLAH ya bata kyan sura gami da tsari ɗan gaske.
Chapter 9 · 0% Book details