← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 58

Sashe 5

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda yay minti biyu batare daya cemin komai ba sannan kuma can naji yace "Dan ALLAH batul kimin afuwa wallahi abubuwane sukai min yawa kinsan dady ya dawo yau kwana biyu kenan,but shine yasa duk kika jini É—if kuma wallahi dik tunanina akanki yake sorry my love" murmushi nayi tare da cewa "kai masha ALLAH kai mashi sannu da zuwa dan ALLAH.....

"Ok in sha ALLAH" yafaÉ—a tare dajan numfashi kaÉ—an.

"Toya ake ciki?" nafaÉ—a sa'ilin danake saka kaina bisa pillow É—in dake kan gadona.

"Normal wallahi ina ganinma fa nan da next week insha ALLAH dady zezo wajan abbanki kan, maganarmu"...wani tsalle na daka tare da matse wayar akan ƙirjina ina mai zaro idona waje"Dan ALLAH da gaske kake?" sautin murmushinsa naji sannan yace "Wallahi tallahi ba wasa a wannan maganar haba batul ai ina sonki kuma na gaya maki ni auranki zanyi ba wasa ba Wallahi kojina ma da kikai shuru kwana biyu ALLAH duk busy yadda zanyi naiwa dady maganarki ne ya ɓoyeni"......"kai ALLAH nagode maka" nafaɗa ina mai daka tsalle akan gadanmu.

Dariya ya saki kaɗan sannan ya cigaba da bayyana min yadda yake matukar ƙaunata acikin zuciyarsa.

Ni kaina na yarda da yadda ABDUL yake mugun sona sabida yadda muka shaƙu dashi sama da shekara biyu muke tare tun ina s.stwo a sec muke tare ai dole na shaku dashi ba kaɗan ba.

Hira mai tsayawa arai muka sha nida ABDUL anan yake cemin "kinga yanzu idan dady yazo wurin abba aka saka mana rana shikenan kinga mundaina zancen waje ko?" kuma sannan yanzu zan dinga zuwa gida nima nazama ɗan umma na hakika.....amman zan gayawa dady arabu da maganar school ɗinnan taki idan kikazo gidana kya cigaba dayi" yaƙarasa maganar cikin nunan tsananin kulawa.

Cikin jin dadi nace "ALLAH ya nuna mana lokacin my love danni har kasa naji na matsu lokacin yayi" "karki damu komai ze setting very soon" yafaÉ—a yana sakin lallausan murmushi wanda nake jiyo sautinsa ta cikin wayar damuke yi.

"To shikenan bara na shiga ciki mugaisa da hajiya kinsan tashin nawa kenan fa zuwa anjima masake waya kidai zama cikin shiri insha ALLAH cikin satin dazamu shiga zezo".....rufe fuskata nai alamun jin kunya sannan nace "tom nagode ALLAH ya kaimu.....cikin jin dadi mukai sallama da ABDUL sannan na aje wayar a gefena ina mai imagining É—in yadda zan zama amarya nan da É—an wani lokaci wayyo daÉ—i shikenan zan tafi gidan masoyina.

Nidai ina wannan shirman nawa banyi aune ba sejin bugun ƙofar ƴan makaranta nayi tunda su hanif ba secondry sukeyiba...da sauri nakai dubana ga agogon ɗakin ƙarfe ɗaya da rabi.

Jikina duk babu kuzari na nufi waje tare da bude musu kofar ban tsaya akansu ba nai wuff na nufi kicin, cikin sauri nake kokarin dora taliya tunda naga ita zatafi min sauri dayake ina cikin farin ciki shiyasa banfi minti 20ba na kammala musu taliya da mai da yaji kwasheta nayi na zuba a flaks sauran kuma na juyo musu a ture tunda nikam na ƙoshi da kilishi.

Tana turiri na miko musu ita amman yaran nan fafur sukace bazasu ciba su ai ba ita umma tace nai musuba ban kulasuba na dire musu ita a center É—akin nabar wajan.

Ina jin amir harda min tsaki! sannan suka dauka suka soma ci alwala nayo tare da fitowa waje "kai amir ni sa'arkuce dazakumin tsaki dan ubanku na dafa na baku ba baiwa ba sannan kamin tsaki?" ganin yau babu umma babu su ummi masu tare musune ya saka yayi saurin cewa "ALLAH ya baki hakuri anty" bance masa komaiba nai gaban wadrov sallaya na dauka na shimfiÉ—a daman da hijabi ajikina dan haka kaina tsaye na tayar da sallah ta.

Ina idarwa anan kiran ƙarfe uku da rabi na la,asar dan haka na tayar da kayata.

Yau kam alhmdh na zauna sosai nayi addu,a akan ALLAH yasa akawo kudin nan nawa lafiya ina kammalawa na fita waje tarar dasu amir nayi adakin umma sun kunna kallo azuciye na fafakesu sukai shirin islamiyya.

Nima yau abinda yasa bazani ba dan umma bata nan ne tunda mune yan ajin sauka kuma abin dadin shine harda su ummi duka zamuyi saukar tare.

Seda na sallamesu sannan na shiga kicin yau nayi niyar bawa umma mamaki shiyasa na zauna sosai na fara haÉ—a kayan dambu mai rai da lafiya.

Ƙarfe biyar saura na sauke turaren tsakin nafara haɗashi da zogalan da sauran kayan haɗin dambun dangin su gyaɗa da sauransu.

ALLAH cikin ikonsa shida saura na kwashe komai.

Daman su ummi se 6 suke dawowa dan haka se kawai na nufi ɗaki na gyara mana shi na shige wanka, na fito daga wanka dagani se ƙaramin towel a west ɗina naji alamun anata buga ƙofar soro daman rufeta nayi sabida ban san mai shigowa ba gashi gida nini ɗaya.

Tsaki naja bayan na lakaci man vasiline zan shafa a jikina...jin wani bugun ne yasa nace nasan waÉ—an nan Æ´an jaraban ne wallahi dan dai kunci sa,atane amman wallahi dase na shirya zan bude muku marasa mutuncin banza da wofi.

Nayi maganar ina hararar gefena kamar da mutum a wajan.

Da sauri na goga man a fatar cinyata sannan na mike a hakan batare dana yafa komai akan towel É—inba na nufi tsakar gidan.

Sabida nasan É—ayan biyune ko ummace ta dawo ko su amir kosu ummi shiyasa natafi inata mita afili.

"Waiku dan ALLAH wasu irin yarane sekun ɓalla masa ƙofane haba idan kunyi hakuri ma ai yanzu zan bude muku kofar nonsense kawai"nafaɗa tare da nufar lock ɗin dana zura wanda ya taimakawa kofar wajan datseta.

Zareshi nayi ina faman hararar wanda ke kokarin shigowa ni duk zatona su ummine.

Sedai kash tunanina ya zarta hakan domin ganin wanda yake ƙoƙarin danno kansa cikin gidanne yasaka numfashina ya tsaya cakk.

Har tasaka towel ɗin ƙuguna yake kokarin zamewa......!!!

*10*
Dasauri naja towel ɗin tare da raɓewa a jikin bango sabida yadda naga yana aikamin da wani irin kallo marar misaltuwa juyawa yayi kaɗan yana ƙoƙarin zaro abu daga cikin aljihun wandonsa na kakin soja.
Cikin azama nai maza nabar wajan har ina haɗawa da gudu-gudu kaɗan ina zuwa ɗaki na faɗa kan gadona ina mayar da numfashi dan tsira daga karɓar hukuncinsa.

Shikam anasa ɓangaren tsaki yaja kaɗan aransa yana mamakin rashin kunyar wannan yarinyar amman ganin tsayawa yay nazari akanta ɓata lokacinsa yake shiyasa yayi azamar barin wajan ya nufi part ɗinsa tare da wayarsa manne a saman kunnensa.

Ganin ina ɓata lokacina ne wanda da alama,ma shi tuni yabar wajan dan haka sena miƙe tsamm tare da nufar wadrov ɗina ta kaya. riga da skirt na atamfar matrix mai kalar golden na ɗauka gaban madubinmu na nufa tare da shiryawa cikin atamfar wadda nishi kaɗan zanyi kayan su yage sabida sunmin kaɗan daman kuma umma tace na bawa ummi amman na hanata.

Ina daurin kallabina naji muryar su ummi sun dawo kuma kamar haÉ—in baki segasu amir suma.

Yaudai babu laifi nai musu abin kirki danni na zubo musu dambun daban a ture sannan na zubo musu taliyar rana dan baza,a barmin itaba cikin murna amira tace."anty batula sannu da aiki mungode".....itama ummi haka tace abin nasu kamar haɗin baki murmushi na sauke akan fuskata batare dana ce komai ba amman ƙasan raina wani mugun daɗine ya kamani daman haka kakeji idan ƙannan ka suka baka girmanka lallai se yanxu na gane cewar duk babba idan ya kama girmansa tofa tabbas na ƙasa dashi zasu girmamasa amman the more ka zubar da ƙimarka tofa babu wanda zega mutunci ka koda kuwa yaron goyene.

"Ummah dai har yanzu bata dawowa ba ko lafiya?" cewar ummi tana kallona domin jin irin amsar dazan bata."eh wlh haryau bata dawoba kinsan fa umma idan ta haɗu da dangi bata son rabuwa dasu" naƙarasa maganar ina dariya "wlh kam meyafi danginka daɗi" cewar ummi ta sake bani amsa a karo nabiyu. nima kallonta nai tare da cewa "hakane kam amman idan ALLAH yabaka na kirki kamar dangin ummanmu wlh suna burgeni akwai haɗin kai" cikin sauri amira mai kai lomar dambu bakinta tace "wlh anty suma dangin abban namu sunada zumunci kallah fa kikaga yadda muke da ƴaƴan gidan alhaji ƙarami.kawai dai mu matsalarmu ɗayace gidan baban abuja nan ɗinma kawai dan sunga yana da kuɗine yasa suke wannan rashin M ɗin"......."hakane amira amman ko gidan baban ma ai naga ba kowa ke hakaba se wannan tsinannar matar mai fuska kamar gwanda" da sauri ummi ta matso gareni tana kallon ƙofa dan kar umma ta shigo bamu saniba sannan tace..........

"Wlh duk gidan baban abuja ba mai kirkifa ke amira nifa na tsani ƴan gidan ƴan rainin hankaline kamar wasu ƴaƴan minista"......kema dai kya faɗa ummi nifa wlh babu ma sama da momyn nan wlh matar bantaɓa ƙin wani abu kamarta ba sabida yadda bata son umma" nafaɗa ina hura hanci ban jira cewarta ba na kuma cewa"shiyasa kikaga wannan Alin ni bai minba sabida wlh idan na gansa tamkar naga wannan uwar tashine"......"kai amman kuma ai ya haidar shi yana da zumunci kedai kawai kice tsanar mamansa ce taja masa"cewar ummi kenan.

Da sauri amira tace "a,a ya ummi wlh itama momyn su ya haidar bata ƙaunar ƴan gidannan fa kalli kwanaki yadda ta ƙarema umma zagi kuma nina rasa me anty batula tai mata ta tsaneta.kina kallo da rasuwar baban yakasai yadda tai ta bin anty batula da harara ita da wata ƴarta anty hafsa mai bin ya hydar".........wani bakin cikine ya kamani jin amira ta tasomin da mikin zuciyata wlh ba,ataɓa min abinda ya konan rai kamar wannan abin da sukaimin a gidan rasuwar nan ba wai har anty hafsa mai bin ya hydar ce zata kalleni tace min......jin muryar hanif ce ta katsen tunanin dana faɗa sukuma ta katse musu hiran da sukeyi.

"Ya ummi wai inji ya hydar yace bakuji ana kiran sallah ba.anty batula kekuma yace wai kafin yadawo daga masallaci ki samesa a part É—insa".....da sauri na zaro duka idona waje jin wannan kiran daya sameni na emergency kodai ya hydar yaji zagin Æ´an gidansun danakeyi ne? kafin na juyo na tambayi su amira har sun baje daga wurin kowa ya nufi wajan alwala.....!!
Chapter 5 · 0% Book details