← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 58

Sashe 42

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ALLAH cikin ikonsa har muka koma momy bata dawoba daman kuma yau É—in girkinta ne dan haka muka kuma bajewa a É—akinsu rauda muka zuba hirar duniya.
Anan take cemin gobe zataje saloon na'eem kuma zataje gidan qawarta tana sauka, rau rau nai da idanuna sannan nace masu dan ALLAH su tambayarmin momy nima na bisu kaina yayi datti.
Dariya rauda tayi sannan tace ai bakida matsala tunda baba yana nan nasan zata barki.
Miqewa nai nayi musu sallama tare da nufar É—akina..
Bayi na faÉ—a nai alwala nazo nai isha sannan na kwanta bacci.
Cikin baccina naji kamar anan magana akaina ina bude idanuna waÉ—anda suka cika da bacci naga momy.
Riqe da qugunta tana faman zabgamin harara.
"Ke haɗomin kayan da alhaji yabaki dan ubanki ina kikaga wajan zama agidan nan bare har awani baki lefe to wallahi karɓesu zanyi"! cike da sanyin jiki na miqe na tsugunna nabata haquri.sannan na haɗa kayan tsaf nina dinga haɗa jakunkunan ina kai mata bedroom ɗinta har na gama jerasu sannan na komo ɗaki na kwanta na cigaba da baccina sabida ni daman ban saka akaina ba ɗanta ma ban damu dashiba bare wani lefen sa.
Da asuba na tashi nai wanka nai sallah sannan nai azkar É—akinta na nufa sanin tana part É—in baba kaÉ—e mata dattin gado nai sannan nai mata mopping wucewa toilet nai na wanke matashi tas sannan na koma kicin na sharosa na kunna gas na É—ora ruwan zafi.
Lokacin dana fito qarfe bakwai dan haka senahau sharar falo kuÉ—i nagani zube akan kujera na haÉ—esu tas na aje mata akan t.v stand sannan na haÉ—a ruwan mopping É—in falon na fara seda na gama komai tsaf sannan naje É—akinsu rauda ko juyi basuyi ba kallon agogon É—akin nayi qarfe takwas da wani abu nai murmushi tare da haskoni agaban umma ada sannan naja masu qofar nayi kicin.
Ruwan dana É—ora akan gas naga ya tafasa dan haka na saukesa na zuba a tea flask sannan na É—ebo dankali nafara ferayewa ina gama ferayar na yayyan kasa yadda zanji dadin suya sannan na zuba mai a kasko nasoma soya dankalin ina gamawa na sauke man na kashe gas É—in sannan na É—auko albasa da taruhu na gyarasu nan na mayarda miyar sourse mai kwai wadda za,a iyacin dankali da ita.
Lokacin dana gama aikin qarfe taran safiya na É—ibi nawa na jere masu nasu daman haka ta umarcan tun jiya sannan na fice nai É—akina.
HarÉ—e qafa nai inacin dankalin ina kora ruwan liptom cike da kuzari na kammala cin abin sannan na kai kwanukan kicin zama nai abakin katifa ta na soma tsefe kitson kaina wanda har wajan goma ban gamaba seda na gama sannan na kaÉ—e É—akin nawa na gyara se kawai na wuce bayi na haÉ—a ruwa mai zafi nai wanka batare dana wanke kaina ba sanin zamu fita anjima.
Rigar atamfa nasaka da mayafinta sannn na nufi falo tarar da momy zaune taci kwalliya nai tana danna wayarta.
Bayan na gaisar da ita cike da tuhuma tacemin ina na aje mata kuÉ—inta tsaye na miqe naje gaban stand na dauko na bata su sannan na koma na zauna tare da zabga tagumi.
Nidai naga momy tana ta É—aga waya bini bini cike da murna akan fuskarta.
Seduk abin ya dauremin kai ana haka naga su rauda sun fito cikin shiri hannun na'eem da keyn mota gaban momy suka tsugunna sukai mata sallama tare da kallona sis taso mu wuce nidai naga momy bata tanka mana ba.
Bayan datace semun dawo abakin part É—in baban abuja na tsaya nace masu bara naje na gaisar dashi dariya rauda tai "hmm waya gaya maki baba na tashi yanzu ai se 12" wara idanuna nai sannan na'eem taja hannuna mukai parking space.
Wata farar venz ta bude muka shiga ban gama tsinkewa ba seda naga yarinyar taja motar tare da nufar gate nan danan aka bude mana muka fice nan muka É—auki hanyar inda zamuje.
Gidan anty hafsa muka fara zuwa mai bin ya hydar wadda bama shiri da ita.
Amman abin mamaki yau itace harda tsokanata kuma sosai ta sakarmin fuska mukaita hira da ita daman ashe itama tsoron uwarta ya hana ta kulani.
Bamu muka bar gidan ba se qarfe É—ayan rana bayan munci munsha takuma sadani da kayan kwalliya masu uban yawa wai naiwa É—an uwanta ado.
Ahanya nake cewa su rauda wai yanaga momy bata min magana ba dazamu taho? dariya suka saki tare da cewa yau ai sister momy tana cikin busy ne yaya hydar zedawofa yau, wai anty maryam ce batajin daÉ—i shine ake tunanin ko haihuwa ce amman shi naji ance ze koma bayan ya kawota, dariya nayi tare da cewa haba shiyasa naga momy yau anata far,a ashe É—an lele ne ze dawo.
Suma dariyar suka kumayi cike da surutu na'eem tace ai muma se É—azu mukaji yana gayawa momy ina tunanin tafiyar sama taka tazo masu amman da ai ba yanzu ze dawo ba.
Haka mukaita hiranmu har muka qarasa wajan saloon É—in, ni aka farawa gyaran kan sannan akai masu suma nan muka kuma rankayawa mukai gidan qawar rauda.

Jirgin shabiyun rana suka biyo duk maryam ta É—aga masa hankali da kuka jiki babu daÉ—i driver ya É—aukosu zuwa gida.
Part É—in momy suka sauka bayan ta cikasu da kayan ci dana sha kala kala shikam miqewa yay zuwa part É—in Mahaifinsa seda yayi masa barka da zuwa suka É—an zanta sannan ya fito ya nufi bangarorin su mama suma ya gaisar dasu.
Part É—in sa ya koma yayi wanka yayi sallah sannan ya zira jallabiya ya nufi part É—in momy, bakaramin mamaki yayiba ganin maryam ta ware sunata hira itada momy.
Zama yayi akan kujera tare da É—ora qafa É—aya kan É—aya.
"hajiya wai ina yaran nan ne?" cike da far,a momy tace "sun tafi gyaran gashi ne" tana gaya masa haka ta juya ga maryam suna hiransu.
"Fatiemah fa naga tunda nazo ban gantaba" yafaÉ—a yana kallon momy danshi danda yay fushi da ita sabida maganar data gaya masa jiya amman kuma seyaji ya kasa daure hakan
Wani sakaran kallo ta watsa masa mai kama da baka da hankali sannan tace "to maye haÉ—inka da ita zaka wani ce tana ina to ta bisu"! takai maganar tana maka masa wata banxar harara!.
Tsit maryam tai tana son ganin action É—in daxe É—auka.
Itama momyn zuba masa idanu tai cike da harara tana kallonsa.
Wani irin firgicine ya dirar masa mai cike da rudani kamar ba Aliyu ba ya miqe tsaye jikinsa har yana mazari "what!! momy ban gane ba?" yakai maganar yana zube hannayensa akan kujerar da momyn take kai.
"Eh abinda kunnenka yaji shinake sake gaya maka nace ta bisu itama ta wanke kan nata kaga yau kusan watanta guda da sati guda kanta akwai datti" takai maganar cikin bawa abun rashin mahimmanci.
Chapter 42 · 0% Book details