Sashe 11
Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ya gama mukaji kuma yayi shuru kafin naga kawu ya miƙe tare da cewa baban abuja "kaga yaya Aliyun ma ya karaso amman jirgin yayi sauri awa uku yanzu yana airport bara na sa aje a daukosa" fita yay nan naji falon yayi tsit kowa yana nazarinsa cikin ransa.
Nikam wata gudawa ce ta zomin jin LAFAZIN kawu tome hakan ke nufi kodai akwai abin da ke faruwa danine dik an sakani acikin duhu wallahi!
Zaman awa guda mukai lokacin ƙarfe biyar na yamma sannan na fara jin tashin muryar kawu alamun ya dawo shigowa ciki yayi ya zauna.
Minti biyar da zuwan kawu naji wani irin sassanyan ƙamshin turare ya bayyana wanda ya samu damar cika ilahirin falon gabana nane naji yayi wani irin bugawa tare da faɗuwa lokaci guda.
Da sauri na ɗago kaina na kalli bakin ƙofar shigowa falon idona ne ya sarƙe dana Ya Hydar cikin shiga ta ɗanyen baƙin boyel mai ƙwabo ƙwabo babu hula akansa amman ba karami kyau yayiba kansa tsaye naga ya nufi wajan da momyn sa take tare da tsugunnawa ya gaida ita.
Tashi yay ya koma gaban iya sannan ya cigaba da gaida iyayensa nan ma sauran Æ´an falon suka fara gaidashi kasancewarsa babba acikin zuri,armu a Maza.
Matsawa yayi ɗan nesa da anty maryam ya zauna tare da tanƙwashe ƙafafunsa waje guda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana matsa wayarsa.
Koda wasa banga alamar ma ya ganni ba sabida nima kara nutsewa nai a gefen anty zee kamar zan shige cikinta.
Baban abuja shiya kuma bude taro da addu,a a karo na biyu sannan ya fara da yimana nasiha itama a karo na biyu sannan ya ce.
"ALIYU! dasauri naga ya hydar ya ɗago ya kalli baban abuja batare daya ce komai ba, "Aliyu ni wanene agareka?" nan ma bai ce komai illah sunkuyar da kansa ƙasa daya kumayi cikin muskilanci yagaza cewa komai.
"Idan har nine mahaifinka kuma na isa dakai to ina son kaimin halacci guda ɗaya ka nuna min kai ɗanane na hakika shine, ka amince min da auran dana ɗaura maka yau da fatima batare da saninka ba, sabida na HUCE zuciyar ɗan uwana, nasan KOBA SO kai da fatima AKWAI ƘAUNA,ta jini ka taimakeni ALIYU kai min wannan halaccin".
Baban abuja yakai maganar adake tare da cewa "wannan shine dalilin kiranka na gaggawa danai domin kasan ance TILASHIN WUYA MAƘOƘO!.
Wata irin zabura nai wadda bansan na yitaba tare da taka mutanen gabana aguje nai wajan abbanmu tare da faÉ—awa kansa ina cewa "abba ka farka da abdul za,a É—auran aure bada Hydar ba Wallahi abba bana son ya hydar NA TSANESHI....!!!
*18 - 19*
"Na tsaneshi abba wallahi bazan zauna dashi ba, bana ƙaunarsa"! naƙarasa maganar ina mai cakume abbammu ina cigaba da gunjin kukan! danake ɗiff falon yayi babu wanda yayi magana hatta ga abban namu wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar wanda ruwa ya cinye nima maida kaina nayi jikin abba ina mai cigaba da kukan danake kan jiki kan ƙarfi.
Seda akai kusan minti goma sannan baban abuja yayi gyaran murya tare da cewa "haba fatima ya ina son toshe wannan ƙullin kekuma kike son bullo mana da wani ballin kiyi hakuri ki zauna da ɗan uwanki nasan ALLAH ze dai dai taku.
Ban sami zarafin cewa komai ba illah sake rungume abbanmu danayi ina cigaba da kuka!marar dalili wannan wani irin lamarine mai rikitarwa yake kusantoni ni batula? shin ina abdul waima shin a wani matsayi aurena da abdul yake yaya akai aka fasa aurena da abdul waɗannan tarin tambayoyin sune suka taru sukaima zuciyata ƙawanya wadda nagaza kasa boyesu a gaban kowa.
Da sauri na saki abbanmu tare da jan ƙafata kamar wata gurguwa na nufi gaban baban abuja ƙafarsa na kama guda cikin tsananin tausayin kaina na fara magana wadda nasan mafi yawancin ƴan falon sesunmi hawaye sabida yadda na ɗauki salon tausayin kaina a yayin faɗin maganar.
"Baba dan ALLAH dan Annabi S.A.W katai maka min baba ka mayar da aurena kan abdul wallahi baba ya hydar baya sona nima bana sonshi dan ALLAH baba kada kuyi mana auren dole ba......" Ban kai ƙarshen maganar tawaba naji saukar muryar momy kamar wadda aka angazo tafara cewa "yoke mema babana ze dake kije ki fara bincikar iyayenki shin ke wacece kafin ki fara ƙin ɗan ......"!! Dakata Zainab! baban abuja ya daka mata wata razananniyar tsawa data sakani mikewa aguje nai kan umma ina sakin wani irin marayan kuka!
Duk da haka momy batai shuru ba "haba alhaji kamar waccan shegiyar ƴar agaban kowa ta dinga furta kalmar ƙi ga ɗanka sannan ka barta dan tsabar Aisha ta jiƙaku ta shanye to.wallahi nima bazan yarda ba sedai dik abin da za,ai ayi amman wallahi kowa yasan ALIYU yafi ƙarfin wannan matsiyaciyar yarinyar mai kalar alala" babu abin da baban abuja yake se salati sabida wannan cin ZARAFI na momy yay yawa kowa kallonta yake yadda ta zage se lafta masifa take kamar ta ari baki.
"Kuma kije ki binciki waɗannan tsofaffin iyayen naki mai ya hana a ɗaura maki aure da wancan yaron har aka ƙaƙabawa ɗana kafin kizo kina mana wannan haukan" momy ta ƙara jefamin wannan maganar cikin fusata.
Zata kuma wata maganar ce baban abuja ya daka mata tsawa "wallahi zainab idan kika ƙara magana kowa ya shaida ni muhd na sakeki wallahi! kika kuma magana abakin dukkan igiyoyinki.
Babu shiri ta mike tsaye tare da janyo hannun anty hafsat Æ´arta mai aure ta biyu tana kokarin yiwa sauran magana baban abuja yace "ai da kika tashi zuwa gidana ke É—aya kika zo bada Æ´aÆ´ana ba wallahi kika kuskura kika bari É—a É—aya ya tashi daga nan wallahi abakin auranki nagaya maki" yakai maganar cikin fushi.
Zama tayi tana harare harare cikin sauri umma ta miƙe tare dajan hannuna muka bar falon umma tana tsananin kukan dana rasa na menene anty zee ce ta biyomu itama nan danan su amira suka mike suma suka rufo mana baya batare da ɓata lokaci ba muka nufi mota se gida kuma babu wanda ya gaza cewa kowa komai.
Babu abin da kakeji acikin motar da zamu koma gida se kukana dana umma dana amira dan ita ummi naga ɓacin rai ya hanata tace komai anty zee ce ke bamu baki amman itama kukan take a ƙasan ranta.
Su Batula na fita daga falon shima abbansu ya miƙe yana haɗa hanya ze futa da sauri kawu ya riƙo shi tare da mayar dashi cikin falon ya zaunar yana gaya masa magana mai kwantar da zuciya da haka har ya samu hankalin abba yaɗan dawo jikinsa.
tsananin tashin hankali iya mahaifiyar su abba tajishi wanda harya hanata cewa ƙala a yayin da momy ke tujararta.
Cikin fushi baban abuja ya dubi momy tare da cewa "Zainab kin kyauta da duk haukan da kikai agaban surukarki da ƴaƴanki da kishiyoyinki amman kika zauna kike cacar baki akan abinda yake ba haram bane wallahi tur da halinki,amman fa ki sani wallahi!tallahi! auran Ali da fatima kamar rai yake da aljali kokin ƙi ko kinso wallahi seya zauna da ita indai ɗana ne na cikina" baban abuja yakai maganar cikin tsananin fushi.
Dasauri ta miƙe tsaye batare data ce komai ba gudun saki😜taja hannun anty maryam wadda take ta kuka suka bar falon kamar wasu masu iskoki, "anji kunya dai" cewar baba haule ƙanwar abba cikin haushi ta faɗi maganar tare da nufar wajan iya mahaifiyarta tana bata haƙuri.
Haka dik Æ´an falon sukai cirko cirko kowa kagani dai abin bai masa dadi ba da dubara da komai sauran Æ´an falon sukaita bawa iya baki akan abinda momy tayi hatta gasauran Æ´aÆ´an momyn hakuri suke bawa su baban abuja da iya akan abin da mahaifiyarsu tayi kafin ta umarci kowa yay shuru.
Addu,a tayi akan ALLAH ya sanyawa auran albarka dik da dai ba haka aka so taron ya ƙareba amman babu yadda za,ai tunda mai afkuwa ta afku dole tasa alhaji ƙarami ya miƙe tare da bawa kowa umarni akan zasu iya tafiya ALLAH ya kiyaye gaba.
Kowa haka ya bar falon jiki a sake babu dadi. duk da yawancin su sunsan musababin wannan lamarin.
WaÉ—an da suka rage afalon Æ´aÆ´an iyane su abba amman kowa ya futa haÉ—uwa sukai suna bawa abba baki akan yayi hakuri sosai suka nuna rashin jin dadin su ga wannan lamari.
Shikam baban abuja haka ya zauna yana mai ayyana irin hukuncin daya tadanarwa momy mai tsanani.
Momy kam gidan aminiyarta suka wuce itada da surukarta wadda taketa faman zuba uban kuka! seda ƙyar momy ta rarrasheta tare da ɗaukar mata alqawarirrika masu tsauri akan batula sannan anty maryam ta daina kukan datakeyi.
Kowa yabar falon iya hatta gasu abba amman banda Hydar wanda yake zaune a tsakanin kujerar falon wadda ta raba biyu tunda ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa bai sami damar zarafin ɗagosaba har akai wannan dramar aka gama miskilin bai ɗago kansaba.
Duk iya ƙwaƙwar autar manya takasa gane awani condition Hydar yake sam bata fahimta ba haka na bisa da kallo.
Daga can kuma seya miƙe tare da duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa fita yayi zuwa harabar gidan wayarsa ya ɗauka ya danna kiran baban abuja.
Cikin ladabi yake shaidawa mahaifin nasa cewar shifa yau ze koma abuja sabida yana da wani uxuri.
Mamakine ya kama baban abuja tare da girmama irin rashin son magana ta É—an nasa.
"Amman kai yanxu dik abin da akai kagaza cewa komai shine zaka dauki hanya kace zaka koma yau? kodai baka karbi kyautar dana maka bane?"
Murmushi ya saki wanda na kasa fassara na meyene kafin kuma yace.
"To Baba ni maye nawa anan ALLAH ya kyauta" yakai maganar yana cije lip's ɗinsa na ƙasa tare da lumshe manyan idanunsa,yana hango yadda yarinyar take nuna ƙiyayyarsa agaban kowa batare datai shakkaba.
"Ban amince ka koma yau ba. zaka tsaya ne anan har zuwa nan da kwana biyu. kafin agama saita komai idan yaso ka juya da iyalinka"baban abuja ya kai maganar cikin basa umarni.