Sashe 35
Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na saka rigar wadda taimin das ajikina dayake doguwace, dayake babu madubi a ɗakin yasa na ɗauki ɗan ƙarami na jikin powder ɗina na nufi gaban window na ɗora ɗaurin kallabi sannan na koma na ɗauki mayafina wanda yayi kala da shaddar jikin nawa tare da ɗan fesa turare mai daɗin ƙamshi nayi waje tare da nufar falon ina takuna ɗai-ɗai kamar yadda anty zee taimin lecture atun farkon maganar aurena da abdul kafin ta dawo kan wannan. Har ƙasa na ƙarasa gaban momy na gaisheta amman tai kamar bata jini ba sema ƙara haɗe ranta datayi tam kamar bata taɓayin dariya ba janai da baya kaɗan tare da zama na tanƙwashe ƙafata a gabanta ina zubawa t.v idanu. Banfi minti ɗaya da zamaba sega rauda ta fito daga ɗakinsu tana hamma wanda da alama ko yunwa ce ta korota, tana ganina ta faɗaɗa far'arta gami da matsowa gareni cikin kulawa ta fara min magana "Lah sister fatimah yaushe kika zo?" amman mu bamu saniba wallahi" tafaɗa cikin tsananin zumiɗi gami da kawomin hannunta kamar zata rungumeni. Ƙaƙalo far'ar dole nima nai tare da bata amsa da "jiya"sannan naja bakina na tsuke, dannifa sam bana ƙaunar halaƙa da duk wanda ya raɓi momy sabida bata ƙaunar uwata nafaɗi maganar cikin raina kamar kuma tana ji sena ɗan tura bakina gami da watsa mata wani irin kallo ta wutsiyar idanuna. Cikin tsananin farin ciki ta mike "sis bara na kira na'eem wallahi itama bata san dake aka zoba dammu kam momy bata gaya manaba haka kuma big bros" da ido na bita tare da kauda kaina gefe ina wasa da fulawar jikin carpet, ina kallon momy tana aika mata da harara sabida lokacin ita momyn tana yin wayane. Acikin minti kaɗan segasu kamar wasu ƙananun yara sukawani ɗanemin jikina suna shirme waisu acewarsu murna ce, wadda da can basusan hanyar gidan ubana ba seyanzu za,aimin bariki toni har yanxu banga wajan zama agidansu bama bare su saka rai daxan saki jikina dasu. "Sis fatimah! naji muryar na'eem cikin farin cikina tana min magana mai kama da kawo gulma. "Wallahi munyi farin ciki da aurenki da yayanmu dan ALLAH kada ki kula momy duk abinda zatai maki amman idan anty maryam tai maki wallahi ki zageta muma haushi take bamu yadda zakiga tana wani ɗaure face idan muna waje". Tana kaiwa nan ta juya tana kallon momy kotaji mitace ganin hankalin momy baya kansu yasa ta juyo tacigaba da bani labarai marasa kan gado da tsari danni shi kansa baya gabana bare wata matarsa. Taɓe bakina nayi tare da ɗan jan tsaki mai sauti tare da cewa na'eem ɗin "to naji" iya abinda na gaya mata kenan na kalli raudah saboda nidai araina naji nafi sonta sabida ita batada rawar kan na'eem sannan kuma uwa uba batada surutu, "Pls sis zanyi break wallahi rabona da abinci tun jiya" tun kafinma na dire abinda zance naga na'eem ta miƙe a miliyan wani lungu naga ta nufa cikin minti kaɗan segata da katon flaks na tea a hannunta bayanta kuma wannan yarinyar ta jiyace wadda ta kawomin kayana ɗaki rike da ɗan kwando agabana suka aje nan danan rauda tajawo cup ta haɗamin tea mai kauri tare da zubomin farfesun kaji duk ta ajemin agabana. Bisimillah nayi zan ɗauka nakai bakina naji saukar muryar momy akaina kamar dirar rodi "Na'eem watakan dan kina gadara kayan gidan ubankine yasa kika ɗauko mata kayan abincina batare dakin nemi izinina bako?" takai maganar tana karasowa gabana. Sunkuyar dakaina nai ƙasa ina runtse idanuna duk tsoro ya kamani. Mikomin hannunta tayi "bani bread ɗin hannunki aiba kabirune ya kawo ba dan uwarki aisha!!. Cikin mamaki naɗago kaina ina kallonta da idanuna wanda ya sauya kala nan take haushi takaici baƙin ciki sune suka kamani nan take. Amman babu damar nai wani abu akai domin ance wata fuskar tafi gaban mari! Tsintar muryar raudah nayi cikin damuwa kamar ita akama abun tare da cewa..... "Haba momy idan baki ragama sis fatimah ba aimu kya mana kara na sunan ƙanin mahaifinku dan ALLAH momy muna sawwaqewa zuƙatanmu duniyar ma nawa take, bareni wallahi bantaɓa ganin abban kano ko umman kano sun maki koda kallon banxa ba amman ke kullum kika zauna sekin aibatasu agabanmu haba momy ai bai dace ki zagi iyayenta agabanta ba kada gaba kizo kina danasanin hakan....!!Tas!Tas!! kakejin ƙarar sautin marin da momy ta wanke rauda dashi sannan tahau bala'i "To uwata dan ubanki harkin kai matsayin daxaki yimin faɗa!! har kin isa nai magana ki kawomin wa,azi!! tafaɗa cikin tsawa da gudu naga na'eem ta mike tana kuka tabar wajan itama raudan kuka ta saka tare da barin wajan cikin sanyin jiki. "Allah yabaki hakuri momy" tafaɗa tana shigewa ɗakinsu. Wani tunanine ya ɗarsamin araina wato lallai momy itake son rabamu da ƴaƴanta ashe duk ba haka sukeba su zuciyarsu mai kyauce itace kawai matsalar tinda ga ya hydar ma baya da matsala a iya jiya zuwa yau na fuskanci hakan.. Nima miƙewa nai tare da son nabar wajan sejin saukar muryata nayi "ina zakije ƴar gwall!maza ga hanyar ɗakina can kije ki gyaramin shi ki wanken ki gogen tiles sannan kizo kije part ɗin baba suma ki gyarawa maryam ɗakinta idan kin gama kije cikin masu girki ki zauna dan bana son ganin wannan baƙar fatar taki mai kama data shuni, kuma wallahi ko ɗigon haƙoranki nagani a waje da sunan dariya kinawa baba sena yanke maki baki! takai maganar cikin hargagi. Ƙarasowa nayi sum-sum na wuce na nufi hanyar data nuna min inajin zuciyata babu daɗi, wallahi bada ban umma tayi mugun jamani kunne akan koda kwana bata nemana ba da yau ɗinnan zakara ze bani sa,a! kash to ke batula idan ma kin fita waxe baki na mota ina kuma kika san hanya yadda garinnan babu lafiya, uwa uba ma kuma a yanzu waye ze barki ki futa dan kinsan wannan mai fuskar ƙwaran baze bar masu gadi barinki fitaba zuciyata ta bani wannan amsar. Dawannan tunanin na ƙarasa shiga bedroom ɗin nata ina mai bawa kaina hakuri sabida nasan ba komai ke ɗorewa ba watarana se labari to gwaea tun yanzu inke bawa zuciyata hakuri da juriyar danne dukkan abinda momy zatamin danna san komai akwai lokacinsa. Babban ɗakine wanda ya laƙume ƙaton gado na royal mai kalar ruwan toka se siff ɗinsa da ƙaton ɓadubi se wajan adana takalma mai ɗan karan kyau. Babu wani dattin kirki acikinsa sema wani ƙamshi mai daɗi dake tashi anan na kuma tabbatar da cewa lallai dole ya hydar yazama mai muguwar tsafta sabida yadda na kula momy tana ɗaya daga cikin mata masu tsananin tsaftar gaske. Yaye bedshit ɗin nai tare da ɗauko wanda nagani daga gefen cavet ɗin mai kalar blue na warwaresa tare da shinfiɗawa akai sannan na shirya pillow case ɗin suma cikin tsari, cikin lokaci kaɗan na gama gyara mata gadon nata tsaff harda yimata wani shegen decoration danaga ummi nayi a gadonta. Wani ɗan lugu na juya na ɗauko tsintsiyar laushi da abin kwasar shara nazo nafara gyara mata cikin ɗakin seda na sharesa tas na kwase ɗan dattin naje na watsar sannan na nufi toilet ɗin nata sabida bana son nai mopping sannan na shiga banɗakin zan lalata sharar danayine abanxa Baƙaramin mamaki nayiba lallai inda kuɗi yake akwai kallo jibi yadda iya banɗakin momy ma ya laƙume waɗannan kayan wanka masu kyau da tsari kamar baza,a mutuba lallai inda ranka kasha kallo nafaɗa ina kallon jaguzin cikin bayin wanda yake ɗaukar idanun ga wasu irin madubai da aka jere tarkacen kayan wankin baki akansu juya nai sosai cikin mamaki komaye na kai madubi bayi oho,ganin zan ɓata lokacine akan wannan shirman yasa na mayar da hankalina ga fara gyaran bayin seda na gama tsaf na goge dukkan maduban da glasan wajan sannan na fito waje bayana ke faman amsamin na rashin sabo ga hannuna duk ya ƙage sabida sanyi. Seda nai minti biyar sannan na tsoma mopar a boket na fara mope ɗakin nata cikin tsautsayi ruwan santsi ya kwarfemin ƙafata banyi aune ba seji kake fam!Na kife a wajan wata ƴar ƙara na saki gwanin tausayi gawani irin zafi daya ziyarci ƙuguna haka na miƙe da ƙyar na gama na haɗa kayan nakai inda zankai nayi hanyar fita. Cikin ladabi na ƙarasa gabanta yanzu tare suke dawata mace da alama kaya ta kawo mata dannaga matar tanata fito da kayan jiki na mata kala-kala gaisar da matar nayi sannan nacewa momyn na kammala. Dawani irin kallo ta dubeni sannan tace naje wajan firjin can ta nunan da hannu wai na ɗauki biredi da tea nasha sannan na wuce part ɗin maryam na gyara mata. Cikin miƙa wuya ga abinda ta umarcen dashi na tashi naje gaban firjin wata ƙwallace tazomin ganin ɗan shayin dabefi amir ya kurɓeba babu yadda na iya haka na ɗauka na wuce ɗakin da aka saukeni na zauna awajan zamanma seda nai ƙara sabida yadda ƙuguna ya amsamin dan baƙaramar buguwa wurin yayiba. Cikin ƙanƙanin lokaci nagama da tean wanda ko gefen cibiyana bai jeba na tattare cup ɗin na kai karamin kicin ɗin falon danaga na'eem ta ɗaukomin break fast ɗin ɗazu. Gabanta naje na tsugunna tare da ce mata momy na gama cikin tsawa tacemin wai ubana ne ze rakani part ɗin maryam cikin hargitsa na ɗago kaina na kalleta tare da kawar da kaina gefe ina jan hucin takaici tare da danne abinda yazomin wuyana, murmushi baƙuwarta tai tare da cewa "hajiya zainab kimata a hankali kinsan ƴaƴan namu se hakuri" wani banxan kallo tabi matar dashi tare da hayowa kaina "Maza ɓacemin daga wajannan kije kinemi part ɗin nasu mana banxa mai surfar kwaki" takai maganar tana hamɓarina da ƙafarta da gudu na miƙe nai hanyar waje na buɗe kofar falon na fita seda naci kukana a abakin kofar sannan naja jikina nai part ɗinsu yaya. Baƙaramin ɓata lokaci nai ina danna ƙofarba kafin azo a buɗemin haɗa ido mukai da anty maryam wadda take sanye da wasu shegun riga da wando na barci iya gwiwa se wata riga mai hannun shimi, raɓeta nai na wuce cikin dauriya. Cikin zafin nama tabiyo bayana tare da fincikoni gabanta har ina dan dukan cikin dake jikinta kadan wanda yake gaf