← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 58

Sashe 40

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawani irin tsoro wanda ya bayyana har kan fuskata na qarasa gaban qofar bayan na mayar da wayar baba cikin skirt ɗina na ɓoyeta ta yadda momyn bazata kulaba.
BuÉ—e kofar nayi tare da rage tsahona kaÉ—an "momy gani" nafaÉ—a ina mai saukar da qwayar idanuna a qasa.
"bakiji kiran danake maki bane ba tun É—azu?" ta tambayeni muryarta cikin sanyi babu wannan faÉ—an nada.
"Eh naji momy wallahi kaina kemin ciwo shine na kwanta amman kiyi haquri dan ALLAH" Nakai maganar ina mai langwaɓar da kaina gefe nai suffar abin tausayi.
"Amman miya hana kizo kice zakisha magani wato dan kinga yau Alhaji ze dawo shine zakizo ki kwanta salon kijamin faÉ—a ko?"takai maganar tana zabgan harara, sunne kaina nai aqasa ina mai sake bata haquri cikin rawar jiki "momy ubangiji ya baki haquri naga idan na zauna a falon wataran ceman kike na sakaku agaba shiyasa na kwanta a dakin amman kiyi haquri" naqarasa faÉ—a ina share hawayena.
Tsaki taÉ—an ja marar sauti sannn tace."dalla taso wazaki ma daÉ—in baki wuce muje ki qarasa jeramin kayan abinci a daining É—in falon alhaji" tana gama kayan haka tai ciki tana sakin mitar tata data saba.
Hamdala nai jin bata ji maganar danake ba tare da kara danne wayar ajikina sannan na nufi bayanta har nakai wajan kicin É—in sekum na koma dakina aguje na yayo hijab na fito na biyota sabida tuna gargaÉ—insa na cewar idan na fita koda falon momy ne babu hijabi ALLAH ya isan sa, ina tafe ina tuna wannan maganar tare da cewa wallahi bada ban nasan hukunci da haqqin aure ba da babu wata dokarsa dazanbi amman babu damar hakan sabida daka sani ka take gwara baka sanin bama baki É—aya.
Cikin hanzari na fara kaiwa da komowa a tsakanin part É—in baba dana momy inkai wannan injera inkai wancan injera haka naita faman abu guda har zuwa wani lokaci.
Bayan na kammala naje ɗakinta seda nai nocking bayan ta bani damar shiga na raɓe daga gefe gami da sada kaina qasa sannan nace mata nagama abin da tasakani.
Babu yabo babu fallasa tace to naje na É—auki magani akan furji sannan na bude lokar kicin ta gefe na É—auki abincin ranata a kwano sena naci, godiya nai mata kamar wata almajira sannan nabar É—akin.
Seda na É—auki abinci sannan naje na dauki maganin duk daba yunwa nakeji ba amman nasan idan taga ban É—auka ba yanzu zatace sharri zan haÉ—a mata dannaga baba ze dawo shiyasa na dauka nakai É—akina na adana sannan nafice wajan baaba
Cikin farin ciki najawota gefe na bata wayar tata sannan nai mata godiya tare da ce mata insha Allah zan bata kuÉ—in kati, da sauri baban tace min ita dan ALLAH tabani badan nai mata wata hidima ba.
Murmushi nayi mata sannan na kuma yi mata godiya kana na koma part É—in momy.
Jin anata kiran sallar la,asar kawai sena nufi bayi nai alwala na fito na data sallah, seda na É—ora harda azkar É—in yammaci sannan na kuma kowama bayi na haÉ—a ruwa mai É—umi na tube kayan jikina.
ÆŠan shafo wajan da momy ta kwaÉ—amin ludayi nai wanda harya É—an kumbura kaÉ—an sannan na soma wankana ina mai jin tausayin kaina.
Towel na É—auro bayan na gama wankan na fito sanin babu wanda ke shigomin É—akina yasa na tube towel É—in jikin nawa na nafara goga mai a fatar jikina wadda taketa faman sheqi domin duk bautar da momy ke sakani baya hanani yin wanka da gyara jikina dan watarana ma da kanta take cemin naje nayi wanka idan taga banyi ba, dan a É—an zamana a gidan na fahimci momy irin mutanan nan ne masu tsananin tsaftar gaske.
Atamfar holand na É—auko mai kalar yellow na saka riga da skirt sannan na kafa É—aurin kallabina na É—auki sarqa da É—an kunne na saka tare da yafa wani yellon mayafi wanda ya shiga da kayan jikin nawa.
Turare na fesa sannan na É—auki hanyar fita daga É—akin batare dana gyara katifata ba sabida tun É—azu naji dirin motar su baba.
Abakin qofar na zira takalmina flate sannan na qarasa falon momy.
Tunda nataho momy wadda take zaune riqe da waya a hannunta ta zubamin idanu ko qiftawa batai sanye take dawani ɗanyen boyel ja da baqi wanda yakusan zautar dani dan seta komamin kamar wata balarabiya dan tsabar kyau wallahi baxaka taɓa cewa tahaifi yaya ba, kuma anan seka marsu tai mugun fitowa dashi hatta kallonsu na qasan idanu ashe iri ɗayane.
Har na qarasa gabanta na zauna a qasan carpet momy bata daina bina da kalloba.
Itakam anata bangaren tsananin mamakin yadda batula tai mugun kyaune ya kamata daman haka yarinyar take da kyau da É—aukar ado wanda tashi guda kyanta yake bayyana idan tayi ado yazama dole ta takama wannan adon burki kafin ya rufta da ita.
Dan yadda taga jikin batula yana kaÉ—awa ta ko ina tabbas zatai saurin É—aukar hankalin É—an nata wanda hakan ze jawo mata gagarumar matsala!!
Seda ta numfasa sannan ta dubeni "Ke! waya baki damar kwalliya agidannan nanfa gidan bauta ne ba gidan Æ´anci ba" takai maganar tana zafgan harara.
ÆŠauke kaina nai ina ayyana lallai barewa bata gudu É—anta ya rarrafa ba tabbas wannan hararar ta ya hydar bai É—auka abanza ba ashe gado ce.
"Ke"! naji takuma daka min tsawa "bada ke nake magana ba kona fara wasa dake! takai maganar idonta cikin nawa.
Nima yau sam bana jin daɗin jikina tunda kuma mukai waya da abba yau ƴan shagwaɓar tawa suke kusa dan haka cikin sangarta nace.
"Nifa momy ba kwalliya naiba kuma naga kowa agidannan yau yana farin cikin zuwan baba shiyasa nima na sauya"! sakin bakinta tai tare da kama haɓa "iye yaushe yazama baban naki ki duba a ƴaƴan gidan nan kaf akwai baqi dazaki ce kinga baba yadawo babo ba baba ba munafuka mai baqar fuska" kallonta nai can qasa yadda baxata jiba nace."insha ALLAH ajikokin ki se ansamu baqi tunda baki haifi baqin ba ai shima kuma bakin halitta ce daga ALLAH" na tsinci bakina da faɗar hakan batare dana bari tajiba, tsaki naji ta kuma ja tare da ɗaga wayarta sannan ta ajeta a gefe ta fita.
Zama nai gami da makawa tv idanu ina daÉ—a nanata wannan tsana mai tarin yawa da momy take min.

ALIYU ya kaiwa iska naushi tare da furzar da wani huci daya zo masa lallai yazama dole ya takawa yarinyar nan burki danya fara kaiwa bango da wannan tsanar tata garesa, shifa ɗanso ne qarewa ma shi abun sone ga kowa tayaya za,ai yarinyar nan ta kafa masa karan tsana ada baya damuwa da qinta garesa amman yanzu yana aurenta yana kwaɗayin ya haɗa zuriya da ita kodan mahaifansu amman kuma ita daga nata ɓangaren kullum wani boren take kuma bullo masa( kanka ka sani kenan ashe babu daɗi😛😛😛 ) wannan fa dalilin shiya hana yacewa momy ta bata waya idan suna waya sabida baya son abinda ze ɓata mashi good mood ɗinshi tabbas seya horar da ita ya kuma koya mata sonshi da qaunarsa sannnn yaxo ya gasata da wannan soyayyar tasa wadda watarana idan bata gansa ba setai kusan hauka.( ji mugunta 😭😭 ) tabbas seya nuna mata shiɗin zakine kuma gwarzone agida da jeji sekuma ya nuna mata shiɗin cikakken namijine mai isa da izza wadda da kanta seta raina kanta harta kawo kanta garesa shinefa mai gara manyan mata suna kuka wiwi akansa bare kuma wannan ƴar shilar wadda bada ban darajar aure ba da ko kallo bata ishesaba amman yanzu ta dalilin aurensu yasaka tunaninsa yafara sauyawa akanta har yana tunanin haɗa shimfiɗa da ita kuma yana marmarin yaji kalar tata baiwar ta ɗiya mace wadda idan akai sa,a ya dace yasami ɗa ko ƴa daga gareta yana son ALLAH yafara basu ɗiya mace da ita mai kalar fatarta mai kalar shagwaɓarta amman bamai sangartarta ba, ayanzu haka babban burinsa ya gama aikin gabansa cikin satin gaba yahaɗo maryam su dawo gida burinsa kullum yasanya ta a idanunshi ( tofa 😳) lalubo busassun yawunsa yayi tare da haɗiyewa sannan ya furta "i miss you ƴar rigimatah" cikin sanyin jiki ya koma wajan abokan aikin nasa suna cigaba da aikin gabansu.

Har aka kusan kiran magariba banji É—uriyar momy ba danna haka naja qafafuna na nufi É—akina inje inci abinci sannan nai sallah tunda bani da gatan daxa,a kirani naxo naiwa yayan mahaifina barka da dawowa dan gidan gashinan tsitt hatta su rauda basuma shigoba suna can wajan mahaifinsu cikin dadin rai nikuwa wannan mugun ya rabani da nawa iyayen ya kawomin bursuna.

Ina gaf dazan kai cikin É—akin naji wayar momy tana ringing! da sauri na koma baya ina ayya bara na É—auka na kai mata ko ALLAH yasa inga baban abuja na masa sannu da zuwa.

My Boy naga anrubuta da manyan harufa duk tunani nama ko É—aya daga cikin qannan yaya ne dan haka sena É—aga burina na isar masa da cewar tana É—akin baba amman bara na miqa mata dan kar aita kira kuma nasan daga qarshe laifina xata gani tace ina kallo ana kiranta amman naqi miko mata dan tsabar bakin hali.

Da sassarfa na miqa hannuna tare da dannan wajan É—aga kira "assalamu alaikum momyn bata kusa amman bara na kai mata tana part É—in baba" nakai maganar gaba É—aya kuma ajere.
Chapter 40 · 0% Book details