← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 58

Sashe 12

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya dafe kansa wanda yake barazanar tarwa tsewa dan tsabar bakin cikin daya taso masa nan danan jijiyoyin kansa suka miƙe sukai ruɗu ruɗu batare daya cewa baban nasa komai ba yafara taune leɓansa daman wannan ce sarar hydar idan ransa ya ɓaci.

"Ko baka jini bane?" baban abuja ya kuma maganar daga cikin wayar.

"Naji baba" abin da ya iya cewa kenan bai kuma cewa komai ba.

"Kakuma jawa mahaukaciyar uwarka kunne akan wannan auran zata iya rasa tata igiyar idan batai wasaba, ni yanxu ina airport na wuce gida nida sauran iyalina ka shaida mata idan harta wuce gobe bata dawo ba to daganan ta wuce gidansu" cikin sauri ya runtse idanunsa yana faman furzar da huci mai zafi.

"Yanxu baba ke faɗan wannan maganar ga momy?" yafaɗa a zuciyarsa tabbas wannan bakaramin abin kunya bane shekara da shekaru ba,a taɓa jin irin haka garesu ba se yanzu.

Agaskiya baiji dadin wannan furucin na mahaifinsa ga momy ba domin dik tsiya uwa uwace uwarka dik yadda take kana sonta dan rai ya ɓaci bai zama lallai ya
jefeta da wannan maganar agaban ɗanta ba ( hattara maza masu aibata matanku agaban ƴaƴanku idan ranku ya ɓaci wannan ba dai dai bane take note.).

Gabaki ɗaya ransa ya ɓaci da wannan furuncin na mahaifinsa ga momy har yagaza cewa baban nasa komai se faman taune leɓensa dayake yi shikaɗai yasan yadda ransa ke faman tasafa babu abin da zuciyarsa take se faman zafi da tafasa.

"Baka jina ne kai shuru? ko kana goyon bayan abin da tai mana ne kaima?" cewar baban abuja ta cikin waya.

"Baba ALLAH ya baka haƙuri zan sheda mata in ALLAH ya yarda" abin da ya iya faɗa kenan da ƙyar ta cikin ƙasan maƙoshinsa wanda shi kansa baban nasa da ƙyar yaji mai yace masa.

Da sauri ya katse kiran yana mai dana sanin kiran mahaifin nashi dayayi acikin ransa.

Tabbas baiji dadin abinda baba yay ma momy ba kasancewarsa ɗa.mai son mahaifiyarsa shiyasa yaji dik ya muzanta wannan daliline ya hanasa furta komai acikin falon, hatta ga haukan da waccan yarinyar tai dan shi aganinsa batula ta sami taɓin hankaline.

Shi se yanzu ma yakejin babu dadin barin maryam daya yi taxo wannan biki gashinan anyi abin kunya agaban suruka.

Futa yayi daga gidan iyan ma gabaki É—aya direct zuwa yay ya kama É—aki a hotel seda ya É—an samu nutsuwa sannan ya É—aga waya ya kira momy yaji suna ina.

Da ƙyar ya shawo kanta akan masifar datakeyi sannan ya gaya mata saƙon baban abuja babu yadda ta iya haka ta amince akan gobe zata nufi birnin tarayya.

Maryam kam babu kunya tana jin momy na waya da hydar ta mike gami da É—aukar troly É—inta tacewa momy itakam yau wajan mijinta xata kwana, albarka ta saka mata tare da haÉ—ata da drivern gidan aminiyar tata akan yakai ta wajan mijin nata.

Abdul kam tun daga masallacin ɗaurin aure da mahaifinsa yasa ƙartin nan su fito dashi ya faɗi har yanzu bai tashiba likitocine akansa sunma ce nan da wasu lokutan idan bai farfaɗoba sedai a fita dashi waje dan zuciyarsa ce tai mummunan bugawa.....wata sabuwa😳.

Motarmu na parking a kofar gida umma ta buÉ—e ta fita nima binta nayi aguje.

Gidan namu shuru duk Æ´an uwan sun watse sabida daman an sanar dasu lokacin da zamu tafi cikin gari akan za,a rufe gida shiyasa bamu tarar da kowaba amman gidan namu a wanke yake tass kamar ma ba,ai taro ba.

Da sauri umma tai cikin É—akin ta tana share hawaye.

Nima take mata baya nayi adai dai bakin kofar falo na tsaya ina kallon umma wadda tai zaman dirshan aƙasan carpet tana kuka!

Nace mata "umma!

"Ki daure ki futar dani a duhu akan asalina umma koni ba ƴarku bace? koni shegiyace.? umma maye asalina umma maye yake bibiyarku? umma maye kuke ɓoye mana yakamata ku bayyana mana komai ummata"

Da sauri na ƙarasa gareta aguje ina mai sakin kuka!

"Batula keba shegiya bace kuma keba Æ´ar kowa bace face yarmu ta cikinmu......amman yau zan fitar dake daga duhu zan gaya maki abin da ke bibiyarmu kinji É—iyata fatana kiyiwa abin fahimta mai kyau......!!!

*20 - 21*
Gyaramin zama tayi sosai ajikinta tare da saka hannunta ta sharemin hawayen dake zubowa akan kuncina,sallamar su anty zee dasu Ummi ce ta saka Umma É—auke hannunta daga kan kuncina sannan ta basu Umarni akan su nemi guri su zauna suma, bayan sun zauna nan falon ya É—auki sautin shuru har na wani lokaci kafin umma ta dubeni tare da cewa.....
"Ina neman gafararki É—iyata kuma ina mai bakin cikin sanar dake wannan labari daman bahaushe yace ranar wanka ba,a boyen cibiya, dafarko nidai sunanan aisha kamar yadda kuka sani, mahaifina É—an garin yolane kasuwanci ne ya kawoshi garin kano anan har Allah ya haÉ—ashi da baba mahaifiyarmu ita kuma Æ´ar nan garin kanoce har Allah ya nufesu da yin aure.
Bayan auran baba da malam mahaifinmu seda suka samu shekara uku sannan baba ta samu cikina,cikin hukuncin Allah cikina yana shiga wata tara baba ta haifeni, tunda na taso na kasance ni mutum ce marar magana da rashin son shiga cikin mutane.
Ajikin gidanmu nan yakasai akwai gidan dayake kallon namu gidan iya tunda na taso nake son iya sabida yadda É—anta kabiru yake kula dani lokacin shi saurayine harya É—an tasa tun bana shiga huruminsa harta kai ga nafara kulashi duk da lokacin bamu san wata aba wai ita soyayyaba amman a hankali komai yafara sauya wa daga wajan mu.
Tofa shaƙuwa iya shaƙuwa na shaƙu da kabiru wanda ya kasance ɗa na uku a wajan iya tunda yana da yayye guda biyu, hatta kai ga ko abinci zanci tofa sena je gidan iya sannan zamuci nidashi har zuwa wasu lokuta masu tsayi, batare da mun fargaba harta kai ga muguwar soyayyar junanmu ta kama mu, duk da lokacin ni banfi shekara goma da haihuwa ba.
Lokacin kuma yayi dai dai da haihuwar zainab ƙanwata wadda na bata shekara goma ciff.
Cikin haka ALLAH yayiwa baba rasuwa mahaifin kabiru kenan malam uba magini tundaga lokacin kuma se ragaramar gidan ta koma kan É—an iya na farko muhammadu shima kuma kabiru a wannan lokacin seyake futa kasuwa yana É—an kasa kayan sayarwar sa har ALLAH yasa ya kammala karatun makarantarsa.
Lokaci na tafiya rayuwa tana kuma sauyawa wanda a wannan lokacin muhd yayo aure ya auro zainab ita ta kasance yaran shuwace a farko a gidan iya ya fara zama sabida lokacin yayi jarabawar tafiya aikin soja kafin Allah yasa komai ya tafi dai dai.
Tunda aka auro zainab matar yayan kabiru seta ɗauki karan tsana ta ɗoramin dan kawai iya tana sona harta kai ga na daina shiga gidan iya sabida yadda zainab take takuramin da baƙaƙen maganganu harta kai ga tana nuna cewar ita datake suruka iya bata mata abin da takemin.
Nikuma ganin irin yadda zainab ta takuramin ne yasa na ɗauke ƙafata cak daga gidan iya wanda hakan ya jawo matsala gagaruma wadda ta kai ga har kabiru seda yaxo yasa babana agaba yana kuka akan rashin ganina da baya yi hakuri babana ya bashi tare da nuna masa cewar hakan yafi dai dai.
Bayan wasu Æ´an shekaru masu tsaho abubuwa sun faru daga ciki kuwa harda gama makarantar danai ta primary wanda acikin wannan shekarar kuma Allah ya dauki ran mahaifinmu mutuwar data kawo mana sauyin abubuwa da dama sabida lokacin baba bata da wani sana,ar daxata rikemu da ita.
Se alamuran rayuwata suka koma hannun kabiru wanda ya zame min garkuwa komai shiyake min a wannan lokaci kuma iya bata taɓa damuwa ko saka ido akan hakan ba,a wannan lokacine kuma shima yayan kabiru alhaji ƙarami yayo aure lokacin ita kuma zainab tana da tsohon ciki ta kusan haihuwa babu laifi matar alhaji ƙarami habiba tana sona domin kuwa har yan ayyukan gida nake zuwa na taya ta wannan abu bakaramin ɗagawa zainab hankali yay ba.
Cikin haka ALLAH ya sauketa lafiya ta samu É—anta namiji mai tsananin kyau na fitar hankali ranar suna yaro yaci sunan mahaifinta ALIYU tunda yaronta ya taso take hanasa shiga cikin kowa wai acewarta iya bata kaunarta tafi son habiba dan haka É—anta ma baxe shiga cikin kowa ba shiyasa tunda Aliyu ya taso bashida wata aminiyar kamar mahaifiyarsa ko cikin jama,a ya shiga yanxu ze hau kukan rashin sabo.

A hankali ahankali abubuwa suketa faruwa daki daki daga ciki kuwa har da irin yadda kabiru yake kwanan murƙususun ciwon mara mai tsananin azaba cikin lokaci kaɗan na fuskaci kabiru mutum ne mai tsananin sha,awa wadda har tasaka yake wannan ciwon.
Babu yadda baiyi da iya akan tai masa aureba amman iya taƙi tace haba kabiru yanxu kai idan aka ce za,a maka aure a wannan lokacin ai se a ɗaukemu marasa hankali to damema zaka ciyar da ɗiyar mutane nawa ma kake da wannan maganganun iya take ribatar kabiru har tasa yabar mitar dayake mata. Ranar wata labara ranar baba mahaifiyarmu bata nan taje yola auran ɗiyar ƙanwar babanmu setace muje gidan iya mu kwana, ina zaune da daddare agidan iya duk abin duniya ya dameni sabida yadda naji kabiru shuru tun da safe bangansa ba iya na tambaya ina yake setace min yana ɗaki baya jin dadin jikinsa.
Zumbur na mike tare da nufar É—akin sa wanda yake soron gidan iyan.
Chapter 12 · 0% Book details