← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 58

Sashe 10

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Hanif ya nufi mahaifiyar tasa tare da miƙa hannunsa ya jawo nata tare da mata inkiya akan ta fito waje suyi magana( namiji kenan dik ƙanƙantarsa yafi mace hankali) cikin kulawa umma tabi yaron nata tare nufar hanyar falo.

Kafin ma su ƙarasa fitar sega amira mai bin amir ta shigo aguje! hartana bangaje jama,ar wajan cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltawa cikin kuka! tace "Ummah kinji bala,in daya samemu umma anfasa bikin anty batula!!.

Sabida dik zance ya baza gida cewar anfasa bikin batula wasuma har suna cewa momy ALLAH sarki ashe tausayi ne yasa ta faÉ—i dan wasu basu san an daura da hydar É—inba daga cikinsu kuwa harda su amiran.

Dishi-dishi umma ta soma gani kafin idonta ya sami damar rufewa ruff' bata kuma sanin inda kanta ike ba se a bakin gadonta danginta dik sun zagayeta suna mata Sannu.

Raba idanunta tasomayi ɗaya bayan ɗaya tana son gano wani abu acikin ɗakin nata, cikin sauri anty zee ta ƙaraso tana mai jan majida wadda Daga gani taci kuka! ne ta godewa ALLAH.

"Yaya Aisha sannu, yaya kike jin jikin naki?" da kallo tabi Anty zee kafin tace "Zainab hakika yau zuciya ta gaza ɗaukar wannan mummunar ƙaddarar data riskeni ashe ni Aisha zanga irin wannan rana ranar tonon asiri mai yasa wasu mutanan basuda imanine mai yasa komai za,ai baza,ai akammu ba se akan fatima wadda batan mai hakan yake nufi ba" takarasa maganar tana mai sakin wani irin kuka mai cin rai.

Saka hannun ta tai tare da share hawayenta kana tace "Zainab ina batula wani hali batula ke ciki kinemo min ɗiyata" Cikin dauriya anty zee tace "ki kwantar da hankalin ki har yanzu batula batasan abin da yake faruwa ba, tana can part ɗin baya nai mata dubara na barta da anty beby maƙociyata kuma na rufo part ɗin har zuwa a samu nutsuwa" "ina baban su yake?" cikin damuwa anty zee tace "yana can cikin gari shida sauran ƴan uwansa gidan iya amman naji ance jikin nasa da sauki kema dan ALLAH ki kwantar da hankalin ki, komaifa yazo da sauƙi tunda ALLAH ya sauya lamarin an mayar da auran akan ALIYU"

Dasauri Umma ta miƙe tare da saka wani irin kuka mai ban tausayi tare da cewa "a,a nikam zainab kice kawai an kasheni mai yasa abbansu ze amince da wannan auran bayan yasan abin da ke ƙasa, kekina tunanin har abada Hajiya Zainab zata so zuri,armu ne? nida an barmin ɗiyata ahaka har ALLAH ya kawo mata ɗauki amman wallahi nasan jaka zasu mayar min da yarinya" umma ta ƙarasa maganar tana sakin kuka!

Daƙyar anty zee take bata baki da haka har ALLAH yasa tai shuru se ajiyan zuciyar datake saki jifa-jifa hakama sauran danginta na jiki sukaita bata baki tare da misalta mata ƙaddara kala-kala wadda take riskar bawa har ALLAH yasa ta ɗan daina kukan nata amman bakin ta yagaza cewa komai.

Daga ɗakin da aka kwantar da momy kuwa da ƙyar da siɗin goshi aka samu numfashinta ya dawo kuma tana dawowa hayyacin nata ta soma koke-koke gami da tsinuwa ga dik wanda yake da hannu akan wannan aure kishiyoyinta su mama dasuka zagayeta suna bata baki akan tai hakuri haka dik ta bisu da zagin cin mutunci wai ai hadin bakine su ai da ƴaƴansu mana, ganin cin zarafin yayi yawane yasa suka tattara suka barta ita da ƴaƴanta.

A haukace momy ta diro daga kan gadon da aka kwantar da ita mayafi kawai taja tare da futa tsakar gida zagi da cin mutunci marar adadi gami da tone tonen asiri kala-kala tai tawa umma kuma ikon ALLAH babu wanda ya tanka mata a dangin umma seda ta gaji dan kanta sannan taja Æ´aÆ´anta suka bar gidan.

Kai tsaye cikin gari suka nufa acan ɗin ma taso tai cin mutuncin amman ganin baban abuja a gidan yasa tai muƙus amman fa se faman harare harare takeyi.

Iya mahaifiyar abba ita ta dubi baban abuja tare da basa umarni akan ya kira sauran Æ´an uwa saboda wannnan gagarumin lamari daya kwancewa kowa kai yazama dole ai taron gaggawa dole Zuri,ar malam uba magini ta zauna domin a san yadda za,a bullowa bakin zaren.

Cikin mintuna kaÉ—an dik wasu Æ´an uwa na asalin zuri,ar gidan sun halarta sedai Æ´aÆ´an abba ne basu isoba waÉ—an da yanzune sakon ya tarar dasu.

Shima Hydar baban abuja yay masa waya akan lallai lallai ya biyo jirgi yazo kano ayau É—innan sabida kiran mahaifiyar tasu na gaggawa datace bata daukewa kowa na cikin zuri,ar tata ba.

Cikin damuwa ya dauki driver sa sukai airport dan shikam baya da wani shirin zuwa kano É—in yanzu amman yaya ya iya.

Lokacin da saƙon kiran ya tarar da Umma ba karamin kiɗima tai ba haka ta tattara ƴaƴanta a gaba domin tafiya cikin garin aka bar dangi cikin zulumi.

Tun wajan ƙarfe ɗayan rana nake baza ido domin naga wanda zezo yay min koda buɗa ce irin ta amare amman shuru banga kowa ba tun ina biyewa anty beby muna hira har nazo na ƙosa ga wayata tana dakinmu tsaki naɗan ja kaɗan nasan abdul yana can yana kirana ƙila.

Ganin ƙarfe biyun rana tayi yasa na mike tare da nufar kofa zan fita sabida yadda nakejin zuciyata tana wani irin BUGU kamar zata faso.

Amman ga mamakina kofar tana rufe abin haushi nazo na tarar da anty b tana bacci haka naja na zauna can kuma sena soma kuka wanda ban san na maye ba.

Nan da nan jikina kuma seya soma rawa cikin haka naji muryar anty zee tana magana "batula maza fito ina beby É—in itama?" ban bata amsaba haka na mike da sauri na nufeta "anty zee ina su ummi dan ALLAH haka ake kin barni ni kadai anan bara na je wajan umma" nafaÉ—a ina nufar hanyar waje.

Jawo hannuna tai gami da rikeni batare data cemin komai ba ta sakani agaba mukai waje ta kofar baya ma ta fitar dani ganin motar gidan Alhaji ƙarami yasa naji wani iri araina kenan har anzo tafiya dani lallai amman an shammaceni shine ko hoto ba,a barni nayi da ƴan uwana ba.

Daman mu dik wanda za,ai wa biki a danginmu ta cikin gari ake daukar sa shiyasa ban kawo komai ba har anty zee ta sakani a gidan baya.

Abin mamaki yadda naga Umma a kusa dani a zaune fuskarta dik tai ja alamun taci kuka ta godewa ALLAH.

Gakuma ummi da amira agaba amir da hanif a gefe se anty zee data shigo nan driver yaja motar muka bar layin .

Kaina ya rigada ya kulle shiyasa banga fuskar dazan tambayi mai ake cikiba.

Ga Umma daga na haɗa ido da ita senaga ta sunkuyar da kanta ƙasa tana goge hawayenta?

Tabbas akwai Lauje Cikin NaÉ—i.....!!

muje zuwa.

*16 - 17*
Gabaki É—aya kaina ya riga ya kulle da wannan lamari shin meke faruwa ne? bani da wanda ze bani amsar wannan tambayar ga su ummi naga sun sami wata irin muguwar nutsuwa kwata kwata banga wata alamar murna a tare dasuba.
Ahaka muka ƙarasa cikin gari direct motar a ƙofar gidan Iya naga tai parking cikin sauri anty zee ta fito tare da kamo hannuna cikin nata muka nufi cikin gidan Iya, tun a bakin kofar da zamu shiga cikin gidan nafara jin tashin hayaniya sama-sama baya na duba naga Umma na biye dani dik jikinta a sanyaye:.

Tun daga soron farko muka kuma jin hayaniyar kamar tana kuma ƙaruwa ne ahaka muka kutsa kammu cikin tsakar gidan abin da ya bani mamaki shine Yadda naga su Abbanmu dik a tsaye sunyi cirko-cirko kamar waɗan da aka aikowa da saƙon mutuwa.

Muryar momy ce naji ta karaɗe wajan cikin kuka take cewa "Alhaji ni kake jifa da waɗannan kalaman dannace ɗana baze AURI......."dakata Zainab naji muryar baban abuja ya buga mata tsawar data sakani na koma bayan anty zee na laɓe jin allurar sojan nasa zata Motsa.

"Wallahi tallahi kika kuma magana akan AHALIN ÆŠAN UWANA JININA wallahi tallahi abakin igiyar auranki" naji muryar baban abuja ta karade gidan baki É—aya babban abunda ya sakani zaman Æ´an bori a wajan shine "Wallahi zainab muddin kika yarda Auran Aliyu da Fatimah ya lalace tofa ki sani dai dai yake da lalacewar naki auran" wannan maganar ita ta sakani sakin anty zee nai zaman Æ´an bori ina mai dafe *ZUCIYATA* ( My next love and romantic novel in sha ALLAH) "Wace fatiman badai niba" nafaÉ—a cikin zuciyata ashe ban saniba maganar ta fito fili.

Nidai bana cikin hayyacina har anty zee ta tarairayeni muka shiga cikin babban falon Iya wanda na tarar da duk Æ´an uwanmu acikin sa kowa a zazzaune fuska babu alamun far,a daga gani ana cikin jimami ne.
Kallo nakebin kowa dashi lokacin da nazo zama a ƙasan carpet ɗin falon idona ne ya hangomin anty maryam matar ya hydar tana jan hancinta fuskarta tai kamar tumatur dan tsabar jaa!mamakine ya kamani ganin yadda ta zabgamin wata ƙatuwar harara haka na kau da kaina tare da kallon sauran ƴan falon dik wani ahalina ya bayyana a wajan hatta ƙannan babana mata da ƴaƴansu kowa yana wajan duk inda ka duba zuri,armu ce iya mu imu ƴaƴan iya da jikokinta idan ka cire anty zee kaɗai data kasance ƙanwar ummah.

Umma da amira da ummi dasu hanif suma dik sun shigo sun zauna umma amman ta matsa can kusada matan su kawu dasu inna haule ƙannan abbanmu ta sunkuyar da kanta a ƙasa ta gaza kallon kowa.

Nima sunkuyar da kaina kasa nai ina share hawayena😭.

Seda mukai wajan minti goma sannan su abbanmu suka shigo falon suma suka zauna daga can bangaren babu iyalai masu yawa acikinmu kamar na baban abuja sabida ƙwansu da ƙwarƙatarsu sun hallara a wurin hatta ga mazan dayake sunzo ɗaurin AURE.

Iyama tana daga can gefe É—aya a zaune hannunta É—auke da carbi tsohuwar arziki kenan babu ruwanta da duniya sam.

Se daga baya naga momy ta nemi waje ta zauna itama amman daga can nesa tana faman harare -harare ita É—aya.

Addu,a baban abuja ya fara yi kafin kuma alhaji karami ya dora da nasiha mai ratsa jiki.
Chapter 10 · 0% Book details