← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 58

Sashe 3

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*6*
Idona nafara rabawa kana kallona kasan tabbas bani da gaskiya, tun kafin Ya Hydar yace komai najiyo muryar ummi cikin kuka! ta biyo bayana tana faman yi masa compalain akaina, "Yaya kaga anty batula dan tsabar mugunta tun asuba muke haɗa break fast ɗinmu bata, tashi ba amman yanzu daga zuwanta ta ɗibar mana fanke ta kuma zubar wa da ameera mai a ƙafa" taƙarasa maganar cike da jin haushina.

Tsaki! yaɗan ja kaɗan kafin ya duba a gogon hannunsa na zallar azurfa kana ya ɗan dubeni kaɗan cike da kallonsa na raini sannan yace "ke kam wace irin wawuyar yarinya cene?"........"dan ALLAH...ya"...bai bari na karasa maganar tawaba ya bugamin wata gigitacciyar tsawa!!! wadda ta sakani sakin flate ɗin a ƙasa batare dana shirya ba.
Tun kafin naji hukuncin dazemin nafara zubar da hawaye masu gudu! ina faman makyarkyata, cikin haka ummam'mu ta fito daga ɗakin abba hannun ta ɗauke da kwanukan daya kammala break dasu, rissinawa yay tare da gaisar da umma cikin mutunci....itama anata ɓangaren amsawa tai tare da cewa "harkata tashi kenan?", Babana, bara nai sauri na haɗa maka break nasan bazaka ci wannan jagwalgwalon yaran nan ba" "No umma ki barsa Wlh muna saurine sabida akwai wani team da zamu turasu wani daji domin su basu taimakon gaggawa kawai idan na dawo nayi".....murmushi umma tayi tare da cewa 'To ALLAH ya taimaka amman daka tsaya ko tea na haɗa maka kasan bana son kana zama da yunwafa" wani wawan takaicine ya kamani ace ƙaton gardi kamar ya hydar aita lallaɓasa yaci abinci amman ni dan jaraba daga ɗiban fanke amfara taran ɗan adam akaina, muryar shine ta katsen tunanin dana ke seji nai, yana cewa umma..........
"Karki damu umma insha ALLAH zan samu nasha cofee a office" yaƙarasa maganar cike da wata irin izza wadda ta zame masa jiki....na fuskanci ma sun manta dani a wajan wani daɗine ya kamani wunzur nai zan gudu sedai kash na makara domin kuwa seji nai yace "ki ɗauki abunsu ki mayar musu, sannan ita da kika ƙona ki bata hakuri" da sauri na sunkuya na ɗebe fanken daya zube na mayar cikin flate ɗin.
Sannan na mike zan nufi kicin É—in seji nai umma tace "ki aje musu kizo ki gyaramin bedroom É—ina sannan ki wanke bayi" babu damar musu dodon nawa yana wajan.....shima sejin muryarsa nai yana cewa "idan kin gamawa umma kije ki gyaran part É—ina kuma na dawo zaki san sauran" yana gama faÉ—in haka ya juya cike da jarumta ya bar wajan... ina jin su ummi suna cewa. "ya hydar adawo lafiya" banji ya amsa ba nikam bai samu wannan matsayin ba haka nai kicin ina kumbure-kumbure.
Dan tsabar rashin mutuncin yaran nan ace gas har biyu akicin amman kowanne seda suka É—ora abu akai babu wani space da suka bari bare na samu damar É—ora koda tea ne, haka naja na fito waje ledar ruwan pure water na É—auka na sha sannan nayi cikin É—akin umma.
Daman bata ɗakin tana cikin falon abba dan haka kaina tsaye nai cikin bedroom ɗin batare dana tsaya gyaran falonta ba kan gadon ta na hau na taka na miƙa hannuna saman wadrov ɗinta ALLAH ya taimakeni na samu abinda nake nema.
Kilishine acikin leda cikin sauri na jawosa tare da zama akan gadon ina budesa sarai daman nasan anan take ajiyarsa kuma badan kowa take boyesa anan ba sedanni saboda tasan halina kamar kura nake muddin zanga abu mai kama da nama tofa sena ci kona waye.
Ya Hydar ke siyo mana shi kullum idan ze dawo daga aiki kowa da É—aurinsa amman ni dan jaraba senabi na wasu na ci sabida son danakewa kilishi kamar raina.ban wani bata lokaciba ware naci iya cina har wani lumshe ido nake haka na zauna seda na kusan share kilishin nan sannan na rage kaÉ—an na mayar mata dashi.

Sanin yau abbanmu baya fita da wuri se wajan 12:30 kuma nasan umma bazata fito tabarsa ba harse ya shirya sannan ta rakasa ta dawo nan shiyasa na fito falon umma, ruwa na ɗauka a fridge na kuma sha sannan naja ƙafata da ƙyar jin cikina ya cika na koma cikin bedroom ɗinta na kwanta a gado,ni daman bani da wani aiki daga ci se barci batare da wani jinkiriba kuwa ALLAH ya taimakeni baccin yay awon gaba dani.
*****************************
itama umma acan bangaren abba ashe tana rakashi, bayan ya kammala shirinsa baccine ya kwasheta tunda su ummi sun tafi gidan anty zee shiyasa ita umma duk tai zaton batula ta gama mata gyaranta harta koma dakinsu.
Har umma na dariyar zuci tana cewa ja'ira tana can tana baccin nata. dan haka itama ta kwanta kanta tsaye tana cewa tunda gidan dagani se waccan sakaran da azahar ma É—ora girki.
Umma bata farkaba se wajan 2 salati tai tare da shigewa bandakin dake cikin room É—in abba alwala tai tare da yin sallar azahar sannan tai wunzur tayi kicin sanin duk inda batula take yanzu zata fito tana kukan!yunwa shiyasa bata damu data tasheta ba tacigaba da sabgar dake gabanta.
Bata gama girkinba se gab da la,asar nan ta kuma sakin girkin ta nufi daki domin tai sallah tunda taga lokaci ya gabato.
Da sauri kuma seta juya zuwa dakin yaranta domin ganin meyasa har yanzu batula bata farkaba daman tasan halinta sallah ba damunta taiba amman yunwa ai ta farkar da ita...abin mamaki bata dakin nasu haka umma taja ƙafa ta kuma komawa dakinta.....abin da ya bata mamaki shine gani datti acikin falon da sassarfa taja ƙafarta zuwa bedroom ɗinta tofa anan ta cika da mamaki.
Domin hango batula tai a kwance akan gadonta tai É—ai-É—ai tana faman zuba baccinta cikin farin cikin gaske...cikin takaici umma ta nufi toilet É—inta da sauri ta É—ibi ruwa mai yawa a kofi ta nufi gadon kai tsaye ajikin batula ta juye ruwan tare da binta da wani shegen duka!!
Firgigit! na mike ina ɓare baki zan saki ihu sabida iya zafi dukan ya shigeni gakuma sanyin ruwan data watsamin har kunnena...ganin umma akaina yasaka na mike zumburr zuwa ƙasa ina faman raba ido.
"Dan ubanki ina aikin dana saka ki?" zare ido nai tare da kallon agogon dake manne a dakin cikin sauri na furta "inalillahi umma na shiga uku ya hydar ya dawo?" sabida tuna aikin daya sakani É—azu.
"Ban saniba maza tashi kiyi sallar azahar sannan kizo ki kwashen tuwo idan kin gama kiyi la'asar seki gyaran ɗakina shasha sha kawai".......sake zare ido nai tare da cewa.....umma kin manta da ya hydar shima ya sakani aiki kumafa banyi ba na ƙarasa maganar cikin kukan tsoro jin cikina ya wani kaɗa sanin halin dodon nawa......!!

*7*
Cikin takaici umma ke dubana tare da cewa "lallai jaririya" dayake yawanci sunan datake gayamin kenan idan kaji ta kira sunana direct to sedai idan wani abunne yafaru gagarumi to anan ne zata kira sunana kai tsaye.
Cigaba tayi da cewa "yanzu ke tsakanin ki da ALLAH abinda kike yana kyautuwa kenan a wajenki?" ace kece babba acikin yaran nan amman kin maidar da kanki tamkar wata sauna" umma ta karasa magana cikin tsananin takaicin abinda nakeyi, cikin kuka! nima nace "haba umma amman duk abin da nai ai bakya haÉ—ani da saunaba wallahi umma na fuskanci bakya sona ko guda" nafaÉ—i maganar cikin sauri tare da nufar toilet É—inta sanin zata iya kawomin bugu!
Tsaki! umma taja tare da fita falo tafara gyaran falon nata tana mitar halin batula wai damma suna mata addu,ane amman dafa abun ƙila seyafi haka ɓaci sam tarasa wannan wace irin yarinyace dasam bata hankali abin nata kullum gaba ikeyi.

Nikam anawa ɓangaren ina shiga toilet ɗin umma agurguje nayo alwala tare da fitowa waje wadrov ɗinta ta kaya na buɗe tare da zaro hijabin ta cikin sauri na tada sallar azahar ina idarwa ana kiran la,asar dan haka se kawai na tayar da abata nayi na huta.
Batare dana tsaya yin wata addu,a ba nabar wajan ko sallayar ban ninkeba waje na futa, ina mai duban falon ganin ta gyara abunta tsaf.
Nima kaina tsaye part É—in yaya nai cikin sauri domin na gyara masa dan nasan yanxu yana hanyarsa ta dawowa.

Cikin sauri na bude ƙofar falon wadda ya xura mata key wanda nasan dan yasan zanyi gyaran ne yasaka yabar key ɗin ajikinta, budewa nai tare da shiga cikin madaidai cin falon wanda tsananin ƙamshin dake tashi acikinsa ya hanani taɓuka komai.
Da ƙyar naja ƙafata zuwa tsakiyar falon ina faman lumshe idanuna jin yadda wani irin sanyin daɗi ke ratsamin ɓargona.
Tsaki!naja kadan tare da cewa "shikam ya haidar dan ALLAH mema zan gyara anan jibafa ɗakin yayai need amman yake cewa a gyara masa" naƙarasa faɗin maganar ina mai hayewa kan seater dake cikin falon can kuma sena mike zumbur nai cikin corridow ɗin falon tare da ɗauko kayan gyara waje.

Sama-sama nagama gyara falon tare da mayar da kayan gyaran inda na ɗaukosu ina mayar da numfashin gajiya kamar wadda tai wani aikin ƙarfi sabida tsabar yadda ganda taimin yawa.
Ɗan ƙaramin kicin ɗinsa na shige wanda yake ɗauke da kayan amfani domin harda furji dan haka kaina tsaye nai wajan gwan-gwanin madara seda na samu ledata mai kyau sannan na ɗiba da yawa dan ƙarfin hali harda milo ina kammalawa na rufe komai tare da futa gabaki ɗaya daga falon zuwa waje rufo masa part ɗin nai baki ɗaya na tafi zuwa cikin gida.

Sauri kawai nake naje na baje akan gado na kwashi gara ni sam bamma san cewar na ɓarar da madarar ba garin ɗiba.

Ɗakinmu na shiga tare da zama akan gadona jin gidan tsitt babu su ummi nifa se hakan yay min dadi yadda ya kamata dan haka se kawai na mike ƙafa ina shan madara ta cikin nishaɗi.
Tuna nine ya faÉ—o min araina na tuna lokutan baya.....!

*TUSHIYA MASOMIN DAWA*

ASALIN MU

TUSHEN LABARIN.

Zamuji kaÉ—an daga cikin tushen su a next page insha ALLAH.

*8*
Chapter 3 · 0% Book details