Sashe 8
Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakuri na bata sabida ni yanzu dik jikina yay sanyi haka naja jikina na koma É—aki ina faman jin kunyar abin da nai.
Su ummi babu abin da suke se tsalle suna murna wai harda cewa suma tun yanzu zasu fitar da ankon bikina haka dai sukaita shirman su ina jinsu.
Ana sallar isha'i ABDUL yay min waya akan cewa yana kofar gida.
Seda na shirya tsaff sannan na nufi É—akin umma na sanar da ita.
Korata tayi tare da cewa na fice na bata waje tunda bana jin magana ita a son ranta na zauna nai karatuna mana amman tunda banga hakan ba ita babu ruwanta gaba ni zanyi kuka da kaina.
Haka na share hawayena tare da fita waje a É—akin abba na waje na shigar da abdul ummi ce ta kawo masa ruwa suka gaisa har yana tsokanarta.
Munyi maganganu sosai dashi na mutunci sannan yace ze tafi.
Har waje na rakasa sannan na koma cikin gida bamma je naiwa umma seda safe ba sabida tsoron abinda zeje ya dawo.
Haka na tafi É—aki na kwanta dik jikina yay sanyi bada ban ma ina fashin sallah ba da nafila zanyi kona ji dadin raina.
***************************
*ABUJA*
Baban abuja suna gama waya da abba ya dubi babban É—ansa wanda yafi soyuwa aransa fiye da kowa a Æ´aÆ´ansa tare da ce masa "Babana kaji abinda yake faruwa da gidan abban naka ko?" ALIYU wanda kansa yake sunkuye agaban mahaifin nasa shine ya É—ago yana cewa "A,a BABA ban fahimta ba wallahi" yana kaiwa nan yaja bakinsa yayi gum.
"Hmm wannan yarinyar ce ta wajen kabiru ta sami miji fa kaga yau ma sunxo neman auranta nidai nace wa kabirun babu wata matsala kawai su bayar ai komai lokacine, ni bada ban ma tafiyar dazakai ba aida ka kaini kanon sabida maganar wallahi" baban abuja ya ƙarasa maganar yana kallon ɗan nasa tare da jin mexe ce masa.
"Baba wai wace yarinyar ce acikin Æ´aÆ´an abban naga dik yarane ina suka isa wani aure yanxun" murmushi baba yayi tare da cewa "to faÉ—ima mana babar yarsa ai kaga daÉ—an aukinta ko?".
Wani shu'umin murmushi Hydar ya saki wanda yake dauke da ma'anoni da dama tare da cewa "aifa to ALLAH sanya alkairi" bai kuma cewa komai ba ya miƙe tare da cewa.
"Baba mu xamu wuce ai mana addu,a dan ALLAH" murmushi baba ya saki shima sannan yace "ai addu,a kullum muna cikin yi maku ita.ALLAH ya tsare kadaibi a hankali da ƙasar daba takaba babana. yanzu dai se ƙarshen shekarar zaka dawo kenan ko?" amman ni banji dadin wannan tafiyar taka ta gaggawa ba naso kunje kano can dangina sunga matar taka wallahi" baba ya karasa magana cikin wani yanayi.
"Karka damu baba insha ALLAH damun dawo zamuje wata shida kawai zamuyi fa mu dawo" yakai maganar yana duba a gogon hannunsa.
Cikin sauri sukai sallama da mahaifin nasa tare da barin wajan ya nufi cikin gidansu.
Sallama yake da momy mahaifiyarsa sannan yace ze shiga suyi da sauran ƴan gidan amman fafur momy taƙi yarda wai baxe jeba salon ai masa barbaɗe ba. (kujifa)
Æata rai yay sosai "haba hajiya wai miyasake kikeson shiga tsakaninmu da dangin mune wai?" mi sukai maki yadace ace zanyi tafiya wadda take da hatsari amman ace baxan sanar da matan mahaifina ba sabida wani zarginki nacan!!
"Aiko babu komai mun haÉ—a iri dasu nan kina da Æ´aÆ´a mu goma su suna da Æ´aÆ´a wajan ashirin aikam mun zama É—aya babu yadda zamuyi dole dai jininmu ne dan ALLAH hajiyata ki daure ki cire komai aranki kinga mune manya acikin gidannan yakamata kina sauke wani abun aranki.
Duk kuma se jikinta yay sanyi sanin halin É—an nata da kafiya da son Æ´an uwansa dan haka setace "to naji yaya zanyi tashi kaje ai wallahi su hajiya salma ( mama ) sunmi illah babba" babu wata illa hajiya kece baki gane ba har yanzu wlh su mama basuda matsala"
Kaga rufen baki malamin gaskiya tashi kabani waje.
Kuma kai sauri ka koma part É—inka kutafi dan nasan yanxu MARYAM (amaryarsa) tana can tana jiran ka, "dik jiran da zatai ai seta bari nagama da AHALINA dai ko" yafaÉ—i maganar cikin zuciya tare da dire mata bandir É—in Æ´an dubu dubu yabar wajan yana cewa 'hajiya ai mana addu,a".
"ALLAH ya tsare" ta faÉ—a tare da É—aukar kuÉ—in tana murmushi.
Haka dik yabi sauran part É—in yay masu bankwana tare da basu kuÉ—i sannan yabar gidan Æ´an uwansa harda kuka! Æ´an sauran É—akunan.
Direct part É—insa ya koma yana zuwa ya tarar da maryam ta cika tai fam! zatai masa magana ya É—aga mata hannu haka tai tsitt ganin babu fuska.
Driver ne ya shigar musu da kayansu boot daganan sukai airport karfe 12 rana jirginsu ya É—aga kalaba.
Semuce ALIYU & MARYAM semun ganku wataranaðŸ˜
*KANO*
BAYAN WASU KWANAKI!.
Duk yadda naso ganin umma ta saki ranta taƙi daga ƙarshema denamin magana tai.
Sedaga baya kuma ta sakko muka koma kamar da.
Abdul yazo sun gaisa da umma. yau kwana biyar kenan da zuwan Æ´an uwan sa gidanmu kuma alhamdulillahi su abba sunyi binciken su babu wata matsala a tsakanin mu da abdul.
Nan da kwana uku ma zasu su kawo kuÉ—i da saka ranar auranmu duka.
Wannan lamari kamar a mafarki nake ganinsa ikon ALLAH.......!!
*13*
Cikin HUKUNCIN ALLAH komai yana tafiya yadda ya kamata., yau tun safe umma takira anty zee, bayan tazo nan suka hau aikin kayan soye-soye wanda ni sedaga baya ummi kecemin wai gobe INSHA ALLAH ƴan uwan ABDUL zasuzo kawo kuɗina da saka rana wannan lamari ba ƙaramin mamaki ya baniba, dik da nasan da hakan amman ban kawo cewar umma zata tsaya yin wannan hidimar dominsu ba sabida yadda tun farko naga ta ɗauki zafi da harkar.
Amman kuma se gashi yanzu naga ta sakko anata sabgar shagalin da ita.nima tun abun yana É—auremin kai har kuma senazo na saki jikina harma na tsoma nawa hannun a murjin dubulan É—in da anty zee keyi a bakin kicin É—inmmu.
Cikin hirarsu naji anty zee na cewa umma wai ina labarin ɗanta Hydar da amaryarsa kuwa? umma kada baki tai "hmm zainab kwanci tashi babu wuya a wurin ALLAH kingafa wai bikin nan kamar yau mukaje shi amman har anyi wajan wata huɗu fa, ninaji jiyama agidan alhaji ƙarami anata maganar cikin matar tasa" wata irin zabura nai kamar ni akaiwa tare da zarowa umma ido......
"Umma ciki fa daga yin auren yanzu harta samu ciki,innalillahi ni wallahi umma bana ƙaunar cikin nan sabida wahalar danaji ance anasha wajan haihuwa" naƙarasa maganar idona yana kawo ruwa.
"Toyan zu uwar,,mu dake muke magana dazaki tsomamin baki"! shuru nai ina binta da ido danni dik zancen cikin nan na anty maryam matar ya Hydar ya tsoratani ba kaɗan ba danni naƙi jinin haihuwa saboda tun wahalar danaga umma tasha a haihuwar amir shikenan naji tafita a raina dik da ba,a gabana tayi ba amman ai naga yadda take fama.
Dariya anty zee ta saki tare da cewa "yaya aisha kwana nawa ne itama ta shiga daga ciki ɗin maye na ɗaukar zafi haka" ta ƙarasa faɗa tana dariya "bazaki gane ba zainab yarannan kamar sukai kansu gidan miji haka sukeji amman dan munafurci jibeta harda wani rau-rau da idanu zatai kuka!!" umma ta ƙarasa maganar tana nuna'ni da hannunta.
"ALLAH umamah tsoro naji nagafa yadda kikaita shan wahala acikin amir" nafaɗa ina sunne kaina a ƙasa. "hmmm to ita dai gaskiya maryam ɗin naji ance da sauƙi bata wannan laulayin amman naji ance hajiya zainab. tacewa hydar ya dawo masu da ita gida".
Shewa anty zee ta saki tare da cewa "ALLAH ya kyauta ai yanzu daman hakane daga anyi aurannan kamar jira ake sekaji ɓur!" haka dai sukaita hirarsu nidai jikina dik yayi sanyi da wannan lamari damma naji ance anty maryam ɗin bata laulayi ai da sauki.
Bamu muka kammala ba se daf da magariba.
Ina tashi nai wanka tare da cin abinci tunda ina fashin sallah.
Fita nai zuwa É—akin umma anan na tarar suna magana da anty zee bayan sun gama sukai sallama mu'muka É—aukar mata kayanta muka rakata zuwa titi tunda yaranta dik suna gida acan tabarsu.
Adawowar mu ummi kecemin "yanxu fa anty batula kema haka zamuna rakaki idan kinyi aure ko" dariya na saki tare da bata amsa "to kika sani ma ko tare abba ze haÉ—amu tunda naga ya shamsu na gidan kawu kamar yana ciki fa" tura baki tai gaba tare da cewa "ALLAH ya kyauta mukam aure semun zama DR. insha ALLAH" to ALLAH ya amsa".
nafaÉ—a lokacin da muka kai zuwa kofar gidanmu.
ÆŠakinmu Ummi ta shige nikuma nayi É—akin Ummah domin na shaida mata anjima fa ABDUL yace idan yazo ze shigo cikin gida su gaisa.
Dakatawa nai abakin kofar bedroom ɗinta jin kamar tana wayane kuma da alama wayar tana da muhimmanci tunda naji muryar umma ƙasa-ƙasa.
Ganin ina ɓata lokacina yasa naɗan ja ƙafata kaɗan na ƙarasa cikin room ɗin ni anufina zata iya hangoni ta dakata dayin wayar tunda ina saurine naje na ƙarasa kintsawa.
Wayar umma tana a handsfree ne shiyasa na nutsu sosai jin murya na cikin wayar kamar na santa.
Tabbas ba muryar kowa bace ba face ta Ya Hydar kuma dagaji suna magana akaina nane. tsaida raina nai tsamm jin yana ce mata.....
"Ki kwantar da hankalin ki umma insha ALLAH komai ze tafi yadda baki tunani ba tunda kuna addu,a ai"
"Amman Aliyu kana kallonfa wannan maganar bazata iya kawo mana cikas ba?" insha ALLAH umma babu komai karki damu daman dai da abban ya ƙara bari nan gaba kaɗan se ayin hakan yafi amman tunda rabonta a kusa yake ai semuyi mata fatan alkairi".
"Hakane kam ALLAH ya zartar mana da alkairi amman wlh ni hankalina ya gaza kwanciya" umma ta faÉ—a kamar kuma tana kukane lokacin"
Sosai naji muryar ya hydar yana yiwa umma magana cikin tattausan LAFAZI tare da gaya mata wasu maganganu wanda kunnena yagaza jinsu.