← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 58

Sashe 47

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina kokarin futa yana kunne kai yayi kyu cikin wata milk shadda yanata kamshi da qyar ya barni muka tafi tare yana ta min qorafin wai nai kwalliya salon maza su ganni nidai shuru nai masa har muka isa asibitin.

Da qyar momy ta amsamin gaisuwata sannan naja jikina nai wajansu mama na gaida su na nemi gu na zauna sabida shi ya tafi wajan likita.
Ina kallo momy tana aikan da harara nikam na kawar da kaina gefe ina jin hiran su mamah.

Minti wajan 30 segasu nan da doctorn cikin farin ciki yake shaidawa su momy ta haihu ansami É—iya mace.

Cike da murna suka miqe harni muka nufi É—akin sedai koda naje ni ance munyi yawa duka sedai mutum uku su shiga dan haka sena bar wajan na dawo inda muke na zauna ina jiran idan sun fito nima na koma.

Tundaga nesa nake jiyo kamshin mayen turaren danaji kamar na sanshi amman na manta inda na sanshi sekuma naji kirjina yana bugawa! tare da faduwar gaba.

Ina É—ago kaina kuma karaf muka haÉ—a ido dashi dukda ya rame yanzu amman baxan gaxa gane ABDUL ba sanye yake da kayan likitoci farare hannunshi É—auke dawani files.

Cike da rawar jiki na miqe ina kokarin barin wajan dan karya ganni sedai kash kafin na karasa fita qafata ra riqe harya samu damar cimmani gabana yataho da sauri cikin rawar murya ya furta.

"Batulaaaaaaaa!!! ina É—ago idanuna na gansa gab dani, kafin nai kokarin jada baya naji saukar hannun......!!!

*74 - 75*

Hannuna ya riqemin cikin nasa idanunshi fall qwalla tare da furta "i miss you my beby"!! yafaɗi hakan kamar wanda yay losing control ɗinshi.....cike da qwarin qwiwa da zafin zuciya nakai masa zafafan maruka masu ma'ana har guda uku sannan na dubesa raina ɓace "ABDUL kai dabbane kamanta da ina da igiyoyin aure akaina"! nafaɗa a tsawace tare da saurin ja da baya.
Cike da mayan so ya biyoni yana shafa kuncinshi sannan ya kuma kawo hannunsa da zummar taɓani wannan karon wani mahaukacin mari aka basa wanda ya amsa ilahirin reciption ɗin cike da qwarewa naga ya hydar ya kai masa wata mahaukaciyar shaqa kamar ze rabasa gida biyu nan danan yafara kai masa naushi ta ko'ina batare dayay masa magana ba hancin abdul yafara jini cikin tashin hankali nai waje ina neman ɗaukin jama,a securtyn wajan ne sukayo kansu da qyar aka ɓamɓare ya hydar daga jikin abdul wanda yaketa qoqarin qwacewa kamar mahaukaci.
Ni duk tsoro ya kamani haka naketa jada baya ina gunji kuka kamar babu gobe.

Jan abdul sukai suka shiga wata kwana dashi inda na hango sa ya nufoni kamar mahaukacin zaki yaja hannuna qiyyy!! yay waje dani kamar yana jan akuya.
Mota ya bude ya wurgani sannan ya zagaya driver side ya figi motar a miliyan.
Babu abinda nake se zare idanuna haka muka qarasa gida abakin gate ya paker motar batare daya kasheta ba ya kuma hankaÉ—oni yayo waje dani ahaka yayta jana har part É—insa ALLAH yasa babu kowa a compound É—in gidan.
Kan seater ya wurgani tare da shigewa É—akinsa minti É—aya tak ya fito hannunshi riqe da belt qatuwa yana nufoni da ita idanunshi sunyi wani irin jajur kamar zasu fitar da jini.
Tsalle na daka tare da dira qasa kafin nai wani motsin ya kwarfeni da qafarsa ya taÉ—eni na faÉ—i batare da wani tsammani ba naji saukar belt kota ina ajikina
"gwara na kasheki kowa ya huta dan borou'ubanki! harni zaki ciwa amana har kina kokarin haÉ— hannu da wani qato you make me suprise wallahi! yana faÉ—a yana cigaba da laftamin betl É—in afatar jikina.
Tun ina kuka har naga babu wani mai cetona idan ba ALLAH cike da dauriya na miqe tsaye nai tsalle na É—anesa duk da azabar zafin danakeji na cakumesa da yadda baxe iya min komai ba nacigaba da kukana!
HankaÉ—eni yayi daga jikinsa ya wuce yabarmin falon fuww! kamar ze tashi sama.
Ko ina na jikina zafi yakemin haka naja jikinnawa da qyar nai part É—in momy tare da faÉ—awa saman katifata na saka kuka!
Cike da sanyin jiki na rarumo wayarsa daya barmin jiya na shiga contact É—inshi na É—ayar wayar hannunshi nafara rubuta masa letter.
"Yaya abinda kake tunani ba haka bane yakamata idan ranka ya ɓaci kana control mine ɗinka before kai taking wani action wanda ka gani ɗazu.....tiryan tiryan nai masa bayani sanin baxe taɓa saurarata face to face ba, sakamon high temper danaga ya shiga ɗazu, ina gama turawa naja blanket na rufa sabida zazzaɓin daya rufeni.
Shin kodai yaya sona ike? na jefoma kaina tambaya wannan fa abinda dayamin duk alamune na soyayya tunda kishi se a so yake fitowa...kai batula babu wani so mutum da matarsa yana sonta keda aka baki shi sannan ki wannan tunanin tokima dena ganin haka yaya ba sonki yake ba.
Zuciyata ta gayamin hakan.
Wani zafin jiki ne mai tsanani ya kamani haka naja abun rufar na qudun duna ina makyar kyata!

Ko ganin gabansa bayay haka ya koma asibitin yay kuma neman duniya baiga koda securtyn da suka rabasu ba bare yasaka ran zega abdul, naushi yakaima iska tare da kifa kansa saman mota.
Yana wani irin kuka! kamar wanda aka cewa momy ta rasu.
"why fatimah zaki min haka?? why!! why!!! yake faman faÉ—in hakan kamar wani zararre.
"Dana ganki da wani qato qwara na kasheki idan yaso nima na kashe kaina! fatima wallahi nafi qaunarki akan kaina.....wayyo soyayyata!! yafaÉ—i hakan idanunshi na zubda wani irin ruwa mai gudu.
Yau ranar farinciki ce garesa sabida kyauta Æ´ar da ALLAH yamasa amman wannan baqin cikin na fatima ya gushe wannan farin cikin.
Kamar É—an maye haka ya faÉ—a mota ya dafe kansa akan sitiyarin motar yana bubbuga kansa akai sannan ya ja motar da gudun tsiya ya kuma barin hospital É—in.

Duk abinda ake momy basu sanniba sabida yadda suka tarar da maryam babu daÉ—i domin ta samu jijjiga dan hakama Æ´ar tana hannun momy, masha ALLAH yarinya mai kyau mai kama da ubanta sak.

Mamy mahaifiyar maryam tana zuwa lokacin maryam ta farka shuru shuru babu hydar babu labarinsa haka sukaita faman doka masa kira amman shuru.

Cike da bacin rai maryam ta soma kuka tana gayawa mamanta my be yana can wajan wannan mai baqar fuskar sabida taga take takensa kwana biyu.

Zumbur momy ta miqe tare da cewa maryam bara taje gidan idan kuwa yana can setaci ubansa.

Mamy ce ta dakartar da momy cike da nagarta ta soma yi masu nasiha mai ratsa jiki ai idan ma yaje wajanta matarsa ce tana kuma mamakin a ina yarta ta samo wannan bakin halin.

Seda mamy ta gama sannan momy tace itakam tagaji gwara alhaji ya sallameta tai zaman Æ´aÆ´anta amman baxe yuhu ta zuba ido aita wannan abun ba dole hydar ya saki fatimah......

*76 - 77*

"A,a hajiya zainab kada kiyi haka sabida shi aure tsarin ubangijine wanda yace ze raba qarshansa nadama" maman maryam takai maganar fuskarta cikin nagarta.

"Kai mamy ni wallahi idan an bibbiya bake kika haifan ba har uwar mijina tafiki sona" maryam takai maganar cike da rashin kunya.

Sakin baki mamy tai tana kallon Æ´ar tata sannan ta ce "koÉ—aya ninafi kowa sonki a duniya shinema abinda yasa nake gaya maki gaskiya sabida ramin dakuke qoqarin haqawa mai zurfine daga qarshe kune zaku rufta"

Sannan ta kalli momy "kekuma zainab nai nadamar baki É—iya amatsayin suruka domin banyi tunanin haka kike ba"

Numfasawa tai tare da miqawa maryam É—iyarta daman É—akin babu kowa cikinsa sesu sakamakon su mama sunyi tafiyarsu tun É—axu.

"Ga Æ´arki nan wannan ba maryam É—ina bace maryam É—ina mai hankalice da sanin yakamata sabida haka idan nan gaba kin sauya kya dawo a matsayin É—iyata" tana kuma gama faÉ—ar haka tabar É—akin.

KaÉ—a kafaÉ—arta tai alamun ko ajikinta sannan ta kalli momy "dan ALLAH momy rabu da mamy bata gane bane kedai momy mucigaba da gashi"

Cike da gasgata hakan momyn ta dubi maryam "ai ki barni dashi itafa mamanki taqi gane cewar nifa bawai qarin aurensa na tsana ba kawai ahalin aisha ne bana kauna ni babu ruwana idan ya saketa ya auro dubu ma" tafaÉ—a cikin rashin damuwa.

Wata uwar harara maryam ta makawa momy tare dajan qwafa akasan ranta sannan tabar maganar cike da tsananin tsanar momy aranta.

Tunda yabar asibitin bai koma gida ba yanata yawo agarin abujane ganin kiran batula wadda taga shuru bai zoba yasa yama kashe wayar batare daya duba sakontaba.

Acan asibiti kam momy taga shuru yasa taje ta karbi sallama sukayo gida inda maryam take jegonta a É—akin momy.

Tunda suka dawo basuwa kowa magana ba daman gidan su rauda basa nan har washegari kuma basuga hydar ba itama batula tana can ɗaki ko iya ɗaga hannunta batai sabida zazzaɓi da ciwon jiki.

Se washe gari da baban abuja yaxo ganin jikar tasa yasa aka dubo masa batula cike da jimami mama taje tana shaida masa yadda taga batulan faÉ—a ya rufe momy dashi sannan ya miqe yatafi part É—insa.

Kiran layin hydar yay wanda aka samu ya bude wayar tasa amman bai yi gigin zuwa part É—in momy ba yana part É—inshi a kwance duk da yasan yayi laifi wajan momy sannan kuma yana son ganin bebyn sa.

Amman wannan bacin ran da batula ta sakasa yasa yayi fushi tun jiya daya shigo gidan yaqi fita ko ina.

Yana duba wayarsa wadda take faman ringing yaga number baba" cike da ladabi ya É—auka nan da nan ya rufesa da faÉ—an akan yaje yaga halin da batula take ciki sannan ya kaita asibiti.

Cikin bin umarnin mahaifinshi ya amsa amman kasan ransa haushinta ne fall.

Saukar da qafafunshi yay tare da zira takalmi yabar part É—in yana tafe ahanya yaga shigowar sako tsayawa yay ya karanta wanda batula ce tayo masa na jiya.

Ganin bayanin data masa seda yasaka kafarsa ta kasa daukar sa yakai kusan minti goma a haka sannan ya nufi part É—in a cikin mutuwar jiki

Tundaga nesa yake jiyo nishinta da sauri ya saki qofar ya karaso kaina ina gefen katifa kwance ina faman sheqa amai sakamon zazzabin daya rufeni É—agoni yay cikin wani irin yanayi na karasa aman ajikinshi.
Chapter 47 · 0% Book details