← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 58

Sashe 50

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka bar maryam durkushe tana kuka ga gawar Æ´arta a yashe a gefe.

Dagudu rauda tafita......

*84 - 85*

Cike da tsananin tashin hankali raudah ta nufi part É—in baban abuja tundaga bakin qofa farko tajita a rufe da alamun baya nan tun safe ya fice kuma daman mostly yana yin irin wannan fitar.

Baya ta juya ta nufi part É—in yayansu sallama take shuru ba,a amsaba haka ta nufi bedroom cikin fitar hayyaci.

Kwance yake akan sopa idanunsa a lumshe jikinsa sanye da jallabiya marun, se carbin dake hannunshi wanda daga ganinsa lazimi ike.

HankaÉ—o kofar tai tare da shiga kanta tsaye da gudu taje garesa tana cakumarsa "yaya yaya katashi Æ´an sanda agidannan suntafi da fatima" takai maganar tana jan hannunsa.

Cike da mamaki ya buÉ—e idanunsa ya dire akan qanwar tasa tare da furta"wace fatiman a ina wai?" yakai maganar cikin mamaki, kuka take a wannan karon "yaya fatiman abban kano matarka, momy ta É—auko mata Æ´an sanda wai ta kashe jaririyar da anty maryma ta haifa shekaran jiya" tana gama gaya masa tai hanyar waje zata gudu.

Cak ya riqe tsintsiyar hannunta yajata a matuqar firgice sukabar É—akin qafarsa ko takalmi babu, direct hanyar gate suka nufa tundaga bakin gate É—in farko hankalinsa ya soma tashi sakin hannun rauda yay ya fita abinda ya É—aure masa kansa shine.

Hango gayyar jama,ar dayay a wajan wanda idan ba idonsa ke gizoba harda Æ´an jarida, "Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un" yafurta hakan cikin tashin hankali.

Duk mai ya kawo hakan? yana kuma ina wannan qazamin lamarin ya faru.

Da sanyin jiki ya qarasa waje inda wani ɗan jarida yay sauri kara masa abin magana. "Yallaɓai saninka babban mutum agarinnan kuma babban soja wanda ya riqe mukamai da dama sannan kuma mahaifinka yanada kuɗi, mizakace dangane da yadda mahaifiyarka take zargin amaryarka dayin ganganci da jaririyarka da aka haifa a shekaran jiya mizakace dangane da wannan lamari dan yanzu haka duk zancan ya karade duniya " doke ɗan jaridan yay cike da tashin hankali ya nufi wajan qatuwar motar dake shaqe da jami,an tsaro acikinta.

Lokacin yayi dai dai kuma da sanda ƴansandan mata suka taso qeyar batula agaba da ankwa a hannunta gabanta da bayanta duk jami,an tsaro gakuma ƴan jarida suna ɗaukar hotonta dana ƴansandan gaba ɗaya ya rasa mai yake masa daɗi da gudu ya nufi motar amman kafin yakai har sun ɓacewa ganinsa.

Cikin tashin hankali ya tsugunna akan qafafunsa yana karanto addu,ar data zo bakinsa Æ´an jarida sunmasa caa haka qaninsa É—an É—akin mama umar ya É—agasa yay cikin gida dashi.

Shigarsu cikin gidan yayi da lokacin da wata mace Æ´ar jarida take É—aukar muryar maryam wadda take kuka kamar ranta ze fita.

"Eh nice mahaifiyar jaririyar kuma mata ga CAPTAIN ALIYU MUHAMMUD UBA MAGINI, daman can bata qaunata shine na aje yarinyar dan na É—auko mata pida aÉ—aki tana kuka kafin na dawo nazo na tarar da ta shaqe mata wuyanta wanda haÉ—a idanun damukai da ita ya saka tasaki Æ´ar tawa aqasa har kanta ya fashe da hancinta, tayi ganganci da É—iyata ta kashemin ita ina roqon manya dasu shiga cikin wannan lamari itama a kasheta kamar yadda ta kashen beby" wannan maganar ta maryam ita ta daki dodon kunnensa da sauri ya rintse idanunshi yana furta addu,a acikin bakinsa.

Da qyar umar yajasa kamar raqumi suka isa falon momy gawar Æ´ar yashe a qasa da sauri ya nufi gaban Æ´ar tasa qafarsa hartana rawa tabbas dagaske Æ´arsa da aka haifa masa ta rasu......!!

Ummi kizo ki É—aukomin radio ta mana kinsan yanxu ake labaran hantsi muryar umma kenan wadda take zaune a falonta tanawa amira tsifar kai sukuma su amir suna zaune suna home work yarfe hannunta tai daga cikin abinda take yankan salak É—in sannan ta miqe taje É—akin abba ta É—auko radion ta kawowa umma.
Cikin sa,a umma ta kunna jim tai sannan tacewa ummi matso kiji wani labari kuma bara muji kai amir yimin shuru umma ta faÉ—a.

Cikin sa,a lokacin ake watsa labaran kuma yayi dai dai da lokacin da maryam take magana..miqewa tsaye ummi tai ko ina na jikinta yana faman rawa ( my fans wallahi wannan page ɗin kuka nake ina rubuta makushi ina kuka ya ALLAH karabamu da sharrin maqiyan fili dana boye ya ALLAH ka rabamu da sharrin dukkan abin halitta ya ALLAH kabamu kariyarka a koda yaushe amin 😭😭🙏 ) itama amira miqewa tai kanta duk a hargitse a tare suka kalli mahaifiyar tasu "umma bakiji wannan labaran ba wallahi kamar daga gidansu yaya hydar fa" umma wadda duk jikinta rawa yake ita ta dubi ƴaƴan nata cikin fitar hankali amman bakinta yagaza tace komai.

Wayar ummace ta ɗauki qara cikin sauri hanif ya ɗauka yana ganin anty zee ce ya ɗaga danyaga mahaifiyar tasu kamar bata cikin hayyacinta murya cikin kuka tafara magana "yaya Aisha kunna redio shikenan batula sun haɗa mata sharri munshiga uku!" tana faɗin maganar tana kuka sakin wayar hanif yay ya zauna daɓas a qasa yana kuka ilahirin falon ansara mai bakin magana kamar mahaukaciya umma ta yayibi hijabi tai hanyar waje.

Da gudu suka bita "umma ina zaki tafi kuma"suka ce mata cikin kuka! "ku barni abujan zantafi naga halin data ke ciki"takai maganar tana tsananin kuka babu yadda basuyi da itaba amman fafur taqi yarda ALLAH yasa hannunta da pos da gudu ummi tabi bayanta ganin ta tari abin hawa yasa ummin tabi bayanta tun a motar umma take gursheqen kuka ( uwa kenan ALLAH yasaka wa da duk wata mahaifiya da alkairi🙏 ) cikin qanqanin lokaci suka kai tasha bayan wani lokaci suka sami mota cikin ikon ALLAH motarsu ta ɗaga.

Da baya amira taja ta É—auko wayar umman wadda take a qasa hanif ya yada tanemo no É—in abbansu ta kirasa cikin kuka take bayyana masa komai, shima alokacin yana cikin gari suna qoqarin tafiya shida Æ´an uwansa ne sabida mama takira iya tun É—azu ta gaya mata daman yay shurune bayason umma taji sabida tanada hawan jini sedai kash alqalami ya bushe dan umma tuni ta wuce a yadda amira ta shaida masa.

Haka ya saki wayar cikin tashin hankali ya shaidawa Æ´an uwan nasa suma duk jikinsu yay sanyi haka suka rufu sukabi motar driven alhaji qarami suka É—auki hanya.

Cikin mintituna kaÉ—an duk wasu dangin umma sun cika gidanta sabida yadda zancan ya bazu tuni anty zee ta sauka agidan umma itama tana haÉ—a.kayanta zata bita seda akai ta bata haquri da qyar aka ce tazauna wajansu amira kafin aji mike wakana yanzu.

****************

Salatin baban abuja shine yasa hydar ya ɗago idanunsa waɗanda sukai kamar gaushin wuta ya zubawa mahaifin nasa, "Wannan cin zarafin ba kowa akaiwa seni tabbas zainab kinci zarafina ƴar ɗan uwana kikaiwa sharrin kisan kai yanzu dame zan kalli dangina wallahi tallahi fatima ko kiyashi baxata kasheba bare ɗan mutum kuma insha ALLAH duk wanda yay mata sharrin nan qarshe akansa ze qare" baban abuja yakai maganar yana ɗaukar gawar tare da umartar ƴaƴansa dasu wuce aje a suturtata! gabaki ɗaya suma kuma ƴaƴan gidan kowa ya lallara awajan daga mai dafe kai sesu rauda dasuke kuka wanda sunsan sharri ne kawai akaiwa fatima amman baxata taɓa aikata hakanba.

Seda umar still ya kuma É—aga hydar wanda yake durqushe yakasa magana sannan suka wuce abakin qofa mama kecewa baban abuja aje asibiti mana cikin masifa ya É—ago ya kalleta babu wani asibitin daxamu je badai Æ´a bace ta rasu to baxamu ko ina ba itakuma zainab avinda takesone ta samu ko to É—anta ze sakarmin Æ´a ayau É—innan nikuma zanyi belin Æ´ar É—an uwana koda kuwa ace duk abinda na mallaka ze qare amman itama ta sani wallahi babu aure a tsakanina da ita daga nan har abada.......!!

*86 - 87*

Yana gama faÉ—in haka yay hanyar waje fuww! da gawar a hannunsa inda duk sauran iyalin nasa suka mara masa baya.

Falon ya rage se iyalansa mata Æ´aÆ´an momy babu abinda suke se kukan jin furucin mahaifin nasu.

Dole tasa umar ya nemo likita aka É—auki hoton jaririyar tare da É—aukar duk wani abu mai mahimmanci sannan aka rufe, bayan nan aka haÉ—a yarinyar aka kaita gidanta na gaskiya se asannan mahaifin maryam ya diro gidan cikin alajabin wannan lamari.

Tunda ake wannan budurin hydar yaqi magana yaqi cewa da kowa komai kuma duk uban kiran da ake masa a waya yaqi ya É—aga bare yay magana shikaÉ—ai yakejin wannan lamari idan ya tuna fuskar yarinyarsa da yadda take kama dashi seyaji wata qwalla ta tarar masa.

Miqawa sirikin nasa hannun yay bayan andawo daga kai yarinyar makabarta sannan yay masa gaisuwa, cikin dakushewar murya ya dubi mahaifin maryam yace masa" ina ganin kawai ku wuce da maryam gida duk yadda shari,ar ta kama bayan angama ta dawo dan nasan dole kotu zasu kai maganar" yaja maganar yana dafe saitin zuciyarsa yanajin yadda take harbawa da qarfin gaske.

Cikin mamaki mahaifin maryam ya dubesa "ai inaganin ALIYU kamar ɗakinta yafi mata zaman lafiya akan gidan namu ko?" kaɗa kafaɗarsa yay alamun ko ajikinsa sannan yace "gaskiya Alhaji baxan boye maka tunda nake ba,a taɓa cimin mutunci kamar na yauba ansan ko ina kana da mosoyi kana da maqiyi miyasa da abin yafaru ni baxa,a sanarmin ba ainafi kowa sanin wani mataki zan ɗauka, duk da fatima matata ce ai ƴar nan da aka kashe tawace kuma inada haqqi akanta zanbar fatima hakane? dole zan ɗauki mataki idan har da gaske ita tai kinsan! miyasa zasu ɗauko mana jami,an tsaro abu acikin gida ba waje ba wanima munafukin ne ya kirawo ƴan jarida! yanxu wallahi shugaban wajan aikinmu shiketa min waya akan yaji maganar agidan redio yanxu kana tunanin mutum dubu nawa ne sukaji wannan maganar an tozartan aure ansaka matata ta sunna ankwa antafi da ita agaban baynan nasi wanda har yanzu babu wata babbar shedar data tabbatar datai kisan wallahi ko mahaifiyata a yanxu baxan iya gani ba bare wata maryam sabida haka tsuntsun daya ja ruwa shi ruwan ze doka yadda suka kai qara sesu san yadda zasuyi amman ni babu ruwana kuma matata yau ɗin nan zan san yadda zanyi tabar sitation na yarda kullum ina kaita kotun amman wallahi indai ni ALIYU ke aurenta to baxata kwana acanba"
Chapter 50 · 0% Book details