Sashe 33
Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tabiyo bayana tare da fincikoni gabanta har ina dan dukan cikin dake jikinta kadan wanda yake gaf da haihuwa. "Ke dallah malama ina zakije kin wani zo kin shigemin falo kamar daga gidanku kika zo dashi". ÆanÉ“are hannunta nayi daga jikina saboda idan har na tsaya gabanta komai ze iya faruwa sabida yadda bana jin dadin zuciyata a halin yanzu tsakiyar falon naje tare da raba idanuna ina neman É—akinsa danshi kaÉ—ai nasan xan iya gyarawa muhallinsa ba wata Æ™atuwaba. Inajin yadda ta biyo bayana tana antaya min ashar amman haka na cije naki kulata nabawa banxa ajiyarta nai hanyar room É—in danake tunanin nashine. Cikin zafin nama na budesa tare da mayar da key na datse nan na karasa cikin É—akin mai É—an karan kyau da tsari gadon nafara gyarawa sannan shima baÉ—an shirya tarkacen kasan wajan loptop É—inshi dake a Æ™asa na É—auka na aje masa akan sopa sannan na gyara masa toilet É—inshi na kammala komai na fito na rufo kofar ina jan kafata sabida yadda jikina yake wani ciwon gajiya ga É—akin nashi daÉ—an kura kaÉ—an. Banganta a falon ba hakan yayimin dadi dan haka nayi gaba abina koda naje part É—in momy banga kowa afalon nataba yasa nayi dakina na nufi bayi babu abinda nake buÆ™ata a halin yanxu kamar naÉ—an gasa Æ™uguna da ruwan É—umi dan haka na nufi bayi na haÉ—a ruwa mai É—an É—umi na gasa jikina sannan na É—auro towel na fito waje babu abinda jikina keyi se zafi wanda har yaÉ—an sakamin zazzaÉ“i gashi dai nayi wanka amman har yanxu ban daina jin yadda kuguna da bayana ke amsamin ba kuka na saka tare da hayewa katifar nai ruf da ciki ko towel din jikin nawa ban cireba haka nahau kuka ina dafe Æ™uguna da hannuna. Nidai banji Æ™arar buÉ—e kofar ba sejin mayar da ita danai anrufe bangama dawowa daga tunanina ba naji alamun motsin mutum akaina. Saurin mirginowa nai ina dafe towel É—in jikina da hannuna tare da zuba masa matsakaitan idanuna ina kallonsa dasu waÉ—anda suka jiÆ™e da ruwan hawaye. Batare daya cemin komai ba ya nemi gu agefen katifar ya zauna ya saka hannunshi guda ya dafe kuncinsa dasu ganin yayi haka yasa nima na juya masa baya ina sakin wani irin marayan kuka! "Ni wallahi yaya bazan iya zaman gidannan ba ai ba haka kukai da abbanmu ba idan baxaka iya rikeni ba kawai ka sakeni ka sawwaqemin kamayar dani gaban iyayena tun kafin akashe masu ni"! Nakai maganar ina jan majina kaÉ—an kaÉ—an. ÆŠago rinannun idanunshi yayi ya zubasu akaina batare daya saki fuskarshiba muryarsa can Æ™asan maÆ™oshi yacemin "Kada na kuma jin wannan banzar maganar abakin ki yanzu mi akai maki?" yajefomin maganar face É—inshi babu walwala ko kaÉ—an. Juya masa baya nayi ina cigaba da kukan danake batare dana tankasa ba. "Malama gaba zaki jiyomin ba baya ba ki tambayi maryam ni mace Æ™arya take ta juyamin baya"! yafaÉ—i maganar cikin jan tsaki yana fiddo da wayarsa daga aljihun wandon jeans É—in dake jikinsa. Idon sa naga kan waya bai kuma Æ™ara cemin komai ba baya ga wannan maganar daya furta min. Ringing wayar taketa faman yi wadda ya Æ™aro sautinta kafin naji saukar muryar umma kamar daga sama. Cikin wani ladabi wanda ya sakani a kwana naji yana gaisawa da umma sannan ya É—ora da ce mata É—azu yaga kiranta baya gidane yanxun nan ya shigo gidan. Jinai umma tana ce masa ba komai nan dai suka kuma gaisawa sannan naji ta sako maganata wai hala dai bana shirmen nawa, murmushi mai sauti yayi tare da cewa "haba umma yaufa kwananta guda aiko gama shirya kayanta ma inaga bata gama ba" yakai maganar cikin raha. Ce masa tayi dan ALLAH idan ina kusa yabani wayar mana jim yayi kadan sannan naga ya mikomin wayar yana zabgan harara! Nima juya baya nai alamun baxan ansaba can kuma sena cafka har ina hadewa da hannunshi sannan nahau mata kukan shagwaÉ“a. Nakai minti kusan biyu ina wannan kukan kafin na furta. "Haba umma yanxu daman kun shirya bazaku taho dasu ummi ba amman kuka kasa gayamin har aka sa na saka raina da zuwan nasu". Kwantar da murya tayi nan tafara min magana cikin tattausan lafazi tare da gayamin manyan misalai na hakuri da zaman aure sannan tace na kwantar da hankalina suna nan zuwa ai indai anyi hutu. ShaÆ™ar majina nai tare da kallon saitin dayake ganin baki É—aya hankalinshi ba,a kaina yakeba yana can kan É—aya wayar tasa yana danne danne yasaka na rage volume tare da cewa umma. "Umma nikam idan kunxo biyoku zanyi wallahi umma yau tunda na tashi momy take sakani aiki nan na kwashe komai na gaya mata hattaga ciwon danaji da abinda maryam taimin da ciwon da Æ™uguna yakemin da yadda momy ta bani break fast tas na zayyanewa uwata batare dana ma tuna yana wajan ba nakuma kara da É—aukar alwashin wallahi suka takuramin guduwa zanyi. Umma danne abinda yake taso mata aranta tayi tare da kiran sunan batula da É—an Æ™arfi kaÉ—an. nan tahau yi mata faÉ—a sosai akan kada ta kuma gaya mata duk abinda momy zata mata sannan kuma ai momy mahaifiyarta ce koda babu auren ali akan ta bare kuma yanxu datake surukarta sannan tace mata kada ta sake ta gayawa kowa wannan maganar koda kuwa hydar dinne sannan kuma komai momy zata mata tai hakuri banda rashin kunya.