← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 58

Sashe 22

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai tsaye ɗakinmu na koma seda na tube rigar jikina sabida nasan ɗakin nashi yayi ƙura kada na ɓata kayana masu kyau.
Wata jar t.shirt É—ina na É—auko mai hannun Vest tare da gajeran wandon jeans É—in hanif.
Dan masifa da ƙyar na tusa wandon ajikina sabida yadda ya matseni ina gama sakawa na fita waje da ummi naci karo tana ɗebe kwanukan wanke-wanke.
Dariya ta saki tana nuna ni "oh yau menake gani anty wlh kamar iyamura jibi bom-bom É—inki kamar doya".
Tafaɗa tana toshe bakinta wata uwar harara na zabga mata tare da nufar part ɗin ya hydar seda na dauki kayan gyaran danake buƙata sannan na ƙarasa cikin falon nasa.
Bawani dattin kirki se ƴar ƙura da yayi kaɗan.
Ina gama gyara masa bedroom na shiga toilet na wankesa tas sannan na fito falo shima na karkaÉ—e dattin kan kujerun sannan na sharo carpet É—in, ruwa na zuba a bokket na tsoma mopa na hau yin moping.
Hatta ga t.v stand seda na goge tass sannan na ƙara kaɗe ko ina da ina na wajan yayimin yadda nakeso
Turare ne kawai ban saka ba lokacin dana gama na ɗaga idanuna na kalli a gogon ɗakin ƙarfe uku saura cikin gajiya na miƙa hannuna alamun miƙa sannan na ɗauki kayan gyaran nai waje.
Abakin rariya na zubar da ruwan sannn nai cikin ainihin tsakar gidanmu.
Adai dai saitin É—akinmu ina kokarin shiga ciki.
Mukaci karo dashi ya dawo daga masallaci danga hannun rigarsa nan a nannaÉ—e.
Cikin sauri nai É—aki aguje ganin wani kallo daya aikomin na zakici ubanki.
Faɗawa kan gado nayi batare da wani yunƙuri ba bacci ya kawomin cafka dan jin yadda jikina yake amace.
Can cikin baccina nafara jin muryar amira sama-sama tana min magana.
"Anty wai kizo inji umma tana falon ta".
Saka filo nayi na toshe kunnena sabida baccin yay min daÉ—i.
Can kuma senai saurin tashi tare da dira nayo waje tunawa da dukan datai min É—azu danayi.
Batare da ɓata lokaci ba nayi cikin falon nata ina faman tura bakina gaba.
Cikin sauri kuma nayo baya zan fito sakamakon ido huÉ—u da mukai dashi zaune yana danna wayansa.
Maryam ma tana gefensa itama wayarta a hannunta.
Tsintar muryar umma nayi tana cewa.
"Jaririya ina gyaran É—akin dana saka ki?"
Ƙifta idanuna nayi tare da cewa.
"Ummafa tun É—azu na gama yanzuma bacci nake waccan Æ´ar ta tasoni".
NafaÉ—a ina sakin wata shu'umar hamma wadda tazomin batare dana shirya mataba.
Saka hannu na nai ina dafe bakina tare da ɗagawa na banƙaro kirjina gaba alamun miƙa.
Ina É—agowa muka haÉ—a idanu da anty maryam wadda taketa faman zubamin harara kamar zata dukeni.
Shikam da sauri naga ya mayar da kansa ƙasa yana faman runtse idanunsa kamar marar lafiya.
Muryar umma naji tana magana.
"Maryam ku hanzatar shiga an kammala gyaran part É—in".
Bata kalli umma ba bare ta tanka mata illama mayar da kanta ƙasa datayi.
Da sauri naga ya É—ago fuskarsa tare da zuba mata harara sannan naji yace.
"Mungode umma" gami da tashi ya nufi hanyar fita.
"mtsww! naja tsaki tare da cewa.
"Kema dai umma kina magana ana maki banza sekace wata sa,arta"
Ina gama faÉ—in haka nai hanyar bedroom É—inta.
Karaf maganar ta doki kunnensa dayake kokarin fita waje.
Baƙaramin mamakin ta yayi ba wasa wasa yaga yarinyar bata da ɗaukar raini kuma batada tsoro tinda har take mayar wa da maryam martani watakan dai tana kishin mahaifiyarta kenan.
Da sauri ya zubar da maganar yayi part É—insa cikin azama.
Itama maryam ganin ya miƙe yasa itama tabi bayansa zuciyarta ɗauke da ƙudirin cin uwar batula idan sun haɗu.
"ALLAH ya kyauta".
Cewar umma tare da barin falon ta nufi É—aki wajan batula.
Ina kokarin kwanciya naji umma tace.
"Bafa bacci ke gabanki ba maza tashi kije É—akinku ki tattare kayanki tsaf kinga goben da wuri zaku wuce".
Matso hawaye nayi tare da kallonta.
"Umma waini dasu kawai zamu tafi kamar wata Æ´ar mage babu mai rakani.
"A,a da zainab da ummi da amira zakuje mana kafin nima nazo idan kin kwana biyu".
TafaÉ—a da zumar rararrashi dan yadda nai kicin-kicin da fuska jira nake kawai ace kiris na fashe.
Sannan idan kin gama gyara kayan naki kije ki ɗora musu abincin dare idan kin kammala ki zuba a kwando ki miƙa musu.
Tana gama faÉ—amin tayi cikin bayinta.
Tashi nayi sabida yanzu bana son yi mata musu tare da nufar dakinmu nahau kintsa kayan nawa duk jikina yayi sanyi.
********************

Acan kuwa asibiti al,amari yayiwa mahaifin abdul zafi sabida yadda likitoci suka shaida masa cewar É—an nasa ya kamu da ciwon zuciya mai zafi wanda idan har ba,ayi gaggawar basa abinda yakeso ba to za,a iya rasa ransa.
Seda yayi kwana biyu bai san wanda ke kansa ba.
Mahaifin abdul iya É—aga hankali ya É—aga hankalinsa.
Gaba É—aya Æ´an gidansu idan banda kuka babu abin da sukeyi waÉ—an da suka cika asibitin.
Mahaifiyarsa kam kukanta yafi na kowa gani take babu mai laifi kamar baban abdul daya hana É—an nasu MURADIN ZUCIYAR SA ( littafina na biyu a cikin jerin littattafaina na social media ).
Wuni sukai acikin asibitin suna faman zurga xurga daga wajan gwanjin jini zuwa wajan da aka kwantar da abdul É—in.
Cikin ikon ALLAH aka samu numfashin sa ya dai daita cikin sauri likitan yazo wajan mahaifin abdul É—in yana gaya masa.
Da sauri shi kuma ya ƙarasa wajansu mahaifiyar abdul ɗin yana shaida musu ansamu numfashin abdul ɗin yadawo.
Hamdala sukai tare da É—unguma cikin É—akin.
Masifa likitan yahau musu tare da cewa su basu waje se zuwa jimawa zasu iya ganinsa yanzu kam subarma ward É—in baki É—aya.
Duk jikinsu a sanyaye haka sukai waje suna faman addu,a ALLAH ya tashi kafaɗun ɗan nasu lafiya ƙannan sa kuma na addu,ar ALLAH ya tashi yayan nasu lafiya.

*****************
Nikam ban samu damar kammala kintsa kayan nawa ba se wajan gab da kiran sallar magariba sabida seda na shirya manyan bags ɗina guda biyar banda ƙananu gashi su ummi sunƙi tayani waisuma a cewarsu zasu ɗan haɗa nasune na tafiyar.
Sauƙinta ma ina fashin sallah shiyasa ban tsayaba har seda na kammala tsaf.
Ina gamawa na turasu daga gefen É—akin namu ina mayar da numfashin gajiya.
Rigar jikina na tube tare da gajeran wandon na É—aura towel na shige wanka.
Ina fitowa na dauro alwala nai zaman azkar sannan na fuce kicin jikina dagani se doguwar rigar ummi ta bacci tunda ni kayana duk na haÉ—esu waÉ—anda zan saka goben kawai na bari a waje.
DaÉ—inta ma naji ance mu a mota za,azo É—aukarmu drivernsa, shikuma shida matarsa a jirgi zasu wuce sabida cikin jikinta.
Dankalin turawa na fere tare da É—aura sanwar fatan dankali mai kifi da É—an kayan lambu kaÉ—an.
Sabida yadda naji gajiya yau bana son dogon girki
Ina gamawa na fuce zuwa É—akinmu na É—an kwanta sabida yadda bayana yake amsawa zuwa bayan isha sena kai musu.
Cikin baccina naji hayaniyar su amira suna wa anty zee barka da zuwa da yake anan zata kwana gobe zamu wuce kuma yau É—in harda yaranta tazo dan naji shewarsu suda su ummi.
Da sauri na watstsake tare da fitowa zuwa falon umma ina faman mutstsuka idanuna.
Sannu da zuwa naiwa anty zee sannan nai waje direct kicin É—in na wuce tare da jera kayan abincin akan ture nai part É—insu.
Abakin kofa na dire kayan tare da juyawa na É—auko flaks É—in tea sannan na saka kaina cikin falon bakina É—auke da sallama.
Kaina a sunkuye yake jin babu wanda ya amsamin sallamata yasa na ɗago kaina da sauri kuma na mayar dashi ƙasa jikina yana faman kaɗawa kamar na mazari.
Sakamakon abinda nagani wanda ya É—agamin hankalina ba kaÉ—anba.
Ganin waɗanda nake rawar jikin dominsu basuma lura dani ba yasa nake kokarin aje kwanukan a ƙasa sedai kash flaks ɗin tean ya faɗi ƙasa har ƙararsa ta bayyana.
Da sauri naga ya juyo yana makamin harara duk idanun sa sunyi mugun jaa.
Cikin sauri nima na tsallake flaks É—in nai waje aguje ina faman dafe zuciyata.
Watakan abinda naga yaya naiwa anty maryam shiya É—agamin hankali har yasakani firgici da É—imuwa.
Bakinsa na gani akan kirjinta gaba É—aya ya nutsa kansa ciki yana faman sha kamar babu gobe.
Itakuma se wani abu take kamar tana cin yaji ban tsaya kallon sauran ba nabar falon.
Duk jikina rawa yake har yanzu ni kaɗai nake cewa daman ya hydar ɗan iskane ban saniba lallai yazama micijin sari ka noƙe.
Da azama nai cikin ɗakinmu har ina tuntube ina zuwa na haye kan gado ina runtse idona gaba ɗaya hoton yanayin nasu yaƙi barin idanuna.
Nidai tun ina tunanin sama sama har baccin daban shiryaba ya kwasheni....!
Chapter 22 · 0% Book details