← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 58

Sashe 20

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*34 - 35*
Tura bakina nayi gaba tare da ƙara danno shi sosai kamar cokali.
Sannan na sunkuyar da kaina ƙasa batare dana cewa umma kanzil ba.
"Jaririya magana fa nike maki"!!.
Umma ta faÉ—a tana kallona.
Banyi maganaba amman zuciyana kamar ze faso waje haka yake beating.
"Nace kije part É—in É—an'uwanki ki masu gyara anjima kaÉ—an zasu shigo nan, su kwana kafin gobe ku wuce".
Kicin-kicin nayi da fuskata kamar zan haÉ—iyi zuciyana baki É—aya sannan nace.
"Haba ummah yanzu tsakani da girman ALLAH kosu amira baza,a saka gyaran part É—in ba seni, haba umma ni bayana ciwo yake min".
Salati umma ta saki tare da kallona cikin tsananin ɓacin rai.
"Batula dan ubanki nike maki magana kina bani amsa any how?".
"Haka nai maki tarbiya, yoko wuta nace kishiga dan ubanki bazaki shigaba bare gyaran É—aki".
Ta ƙarasa maganar cikin tsananin ɓacin ran da bantaɓa tunanin umma nada shiba.
Tura baki nai gaba tare da kokarin futa daga É—akin.
Kafin ma nakai bakin kofa sejin saukar wayar caza nai a gadon bayana kota ina.
Cikin wani irin furgici na juyo na cakumeta ina sakin ihu!
"Umma zan gyara dan ALLAH kiyi hakuri wallahi bazan ƙara ba".
Babu ji babu gani take faman lafta min wayar ajikina.
"Dan ubanki gwara na illataki waya gaya miki har da ɗan dazan haifa ya kawomin raini watakan dan kinga ina barinki shine xaki fi ƙarfina ko".
TafaÉ—i hakan gami da sake kawomin wani dukan a dai dai saitin idona.
Da sauri na kuma zunduma ihun dayayi dai dai da lokacin da wayar ta caki idona.
"Wayyo abba wayyo! amira ummi kuxo wallahi umma kin fasamin idona zan gyara! zan gyara wayyo ALLAH nah".!
Fusgo hannuna tayi tare da turani cikin ɗakin sosai ta saka ƙafarta a zuciye ta turo kofar da ƙarfi ta rufeta.
"Wallahi yau sena cire miki fatar jikinki da duka, yaushe zakiyi hankali har nace kije É—akin mijinki ki gyara masa kimin musu dan gidanku".
Umma takai maganar tana jefani gefe.
"Wallahi zanje na gyara nifa ba wani abu nace maki ba dan ALLAH kiyi hakuri umma na tuba dan girman ALLAH kimin hakuri baxan kuma ba".
"Kima kuma mana aike naga magana bata maki aiki se duka".
Ta kai maganar tana kara bani wata abayana, cikin sauri nai zullo tare da kokarin futa waje.
Ina ihu mai ƙarfi na neman taimakon na waje.
A tsakar gida kam duk su ummi sun tsaya cirko-cirko suna jin ihun batula amman tsananin tsoro ya hanasu ƙara sawa cikin ɗakin.
Gashi kuma abba baya gida bare ya shiga.
Da sauri ummi ta É—auko waya zata kira anty zee duk jikinta rawa yake abinka da É—an uwa se ALLAH.
Sun san tunda yau umma ta saka hannu ta doki yayar tasu tabbas batula tayi laifine domin ita umma sam duka baya daga cikin tsarinta ko laifi sukai sedai tai masu faÉ—a badai duka ba.
Cikin sauri ummi take laluban wayar anty zee zata gaya mata kozata kira umma ta bata haƙuri sedai kuma kash!
Wayar taƙi shiga sam gaya nan kuma a ɗaki umma tana ta faman laftar batula kamar babu gobe......
Wani irin masifaffan mayen ƙamshine ya karaɗe tsakar gidan nasu tun kafin mai ƙamshin ya kawo kai ya shigo kafin daga bisani.
Muryar Aliyu ta karaÉ—e cikin gidan cikin tsadaddiyar muryarsa.
Bayansa maryam ce É—auke da troly medium size a hannunta tana faman sakin hararar takaicin zuwansu gidan wanda seda akai Æ´ar tsama da ita dashi kafin ta yarda ta biyosa.
Sanye ike da wani yadin tisue mai ruwan madara jikin yadin gida-gida ne kamar gidan sugar......
Se agogon zallar azurfa dake É—aure a tsintsiyar hannunshi kansa babu hula se sumar sa daya bari a kwance.
Daga cikin jikinsa kana iya hango farar Vest É—in daya saka aciki, se bakin takalmi daya saka wanda daga samanshi yayi machine da kayan jikin nasa.
Kallo É—aya tak! zakama hydar ya shiga xuciyarka sabida yadda yayi masifaffan kyau na amutu.
Cikin sauri ummi amira hanif amir suka xube a ƙasa.
"Ya Hydar barka da shigowa ya rana?"
FaÉ—aÉ—a far'arsa yayi tare da cewa.
"Lafiya"
Bai kuma cewa komai ba yana kokarin shiga falon umma.
"Anty maryam ina wuni?"
Wata banzar harara ta sakar masu tare da bin bayan mijinta.
Daman ita ummi batai gigin gaida anty maryam É—inba sema bin bayan hydar datayi.
"Yaya dan ALLAH ka shiga ka ƙwaci anty a hannun umma wallahi tun ɗazu take dukanta".
Tsayawa yayi cakk tare da lumshe manyan idanunsa batare daya ce komaiba.
Kamar daga sama yace.
"Hala rashin kunya taiwa Umma dai?"
YafaÉ—a yana mai tsare ummi da manyan idanunsa waÉ—an da nan danan suka bata tsoro tafara rawar murya.
"Umm! umm! nidai naji kamar umma tana mata maganar taje tai maka gyaran part ne to banji mitace ba na daiji tana ihu umma ta fasa mata idanunta".
Ta ƙarasa faɗa tana ƙifta idanunta.
ÆŠan tsayawa yayi yana kallon ummi yadda takeyi da baki kamar na batula É—an murmushin gefen baki ya saki kafin yace.
"Good maganin marar kunya kenan".
Yafaɗa yana kai kansa cikin falon tare da jinjina ƙiyayyarta garesa watakan data gyara masa wajan zama gwara an duketa.
Tun kafin yakai ga shiga center É—akin yaji ihunta yana neman saka masa toshewar kunne.
Cikin sassarfa ya nufi ainihin bedroom ɗin umma turawa ɗaya ƙofar ta buɗe.
Hango umma yayi ta naÉ—e hannu tana faman jibgar batula.
Lumshe idanunsa yayi kaɗan tare da ƙarasawa gaban umma.
Ya tsaya yana sake jin wani irin yanayi mai wuyar misaltawa acikin xuciyarsa.
Tsintar muryarsa umma tayi yana cewa.
"Umma ai hakuri baxata kuma ba".
Da sauri nima na juyo idona ina kallonsa fuskata duk ta jiƙe da hawaye.
"Barni da ita Aliyu wallahi bata da mutunci yarinyar nan"
TafaÉ—a zata kuma kawomin wani dukan.
Babu kunya nai taku ɗaya biyu segani akan kirjinsa na wani rungumesa ƙam kamar zan tsagasa biyu.
"Dan ALLAH yaya kace mata tayi hakuri zanfa gyara".
NafaÉ—a ina sake cusa kaina a tsakanin kirjinsa.
Gabaki ɗaya na jiƙa masa gaban rigarsa da ruwan hawayena.
Shikam anasa ɓangaren cikin azama ya ɗan janyeni daga jikin nasa jin wani shegen felling ya kamasa.
Lumshe idanunsa yayi hannunshi dafe a saman kaina.
"Umma kiyi hakuri" ya faÉ—a yana É—an cije lip's É—insa kaÉ—an.
Dasauri umma ta yada wayar hannunta zuciyarta fal mamakin rashin kunyar batula.
"Wallahi kima sakeshi kije ki gyara musu É—aki dan bazanyi kaffara ba"
Tana.gama faÉ—in haka ta fuce tabarmu......!!
Chapter 20 · 0% Book details