← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 58

Sashe 19

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*32 - 33*

Miƙa nayi gami da turo kirjina gaba ina saka hannuna tare da toshe bakinsa sakamakon hammar data tawo mani wadda ban shirya mataba.
Wata irin mahaukaciyar yunwa nakeji wadda ta addabeni.
Tunda rabona da cin abinci tun jiyane ƙamshin dana jiyo a kicin yasa na nufi kicin ɗin da ɗan saurina domin naga mi ake dafawa na ɗiba na ci.
Jikina har rawa yake na saka kaina cikin kicin É—in.
A tsaye na tsaya ina kallon yadda ummi take juya cips É—in dankalin dake cikin nonstick hamma na kumayi a karo na biyu.
"Ummi tai maka ki É—an sammun dan ALLAH wallahi wata mahaukaciyar yunwa nakeji".
Da azama naga ta juyo tare da sakarmun wata ƙatuwar harara sannan ta juya tana cigaba da juyin dankalinta.
Ban tsaya anan ba ganin zata ɓata min lokacina yasa nai saurin nufar wajan flate flate ɗinmu tare da saka hannu najawo ɗaya tare da spoon naxo gabanta na tsugunna zan kwashi wanda naga tana kwashe wa.
"Wallahi kada ki É—iba na abba nefa ke se aikin bacci bazakizo ki saka hannu muyi aikiba se angama kifi kowa loma".
Ban kulata ba na saka hannu na ɗibo gami da nufar ƙofar fita.
Da sauri ta cillomin cokalin datake kwasar dashi tare da cewa.
"Wallahi baxaki kuma dawowa ɗiba ba kuma wannan ma insha ALLAH sekin ƙware"
Gwalo nai mata tare da saka kaina nabar kicin É—in batare dana tanka mata ba.
Kai tsaye ɗakinmu na nufa na aje sannan na kuma fitowa na nufi kicin ɗin cup na ɗauka tare da zuba ruwan tea wanda yaji citta da kayan ƙamshi na sake fitowa tare da nufar ɗakin namu.
Zama nayi akan gado na É—ora flate É—in akan cinyata tea É—in na gefe ina ci ina korawa da ruwan tea É—in.
Seda na kammala tsaff sannan na fito na aje su a kicin.
Da umma naci karo zata shiga falon abba.
"Jaririya kin kammala karyawar?".
"Eh umma na gama amman wallahi kiyiwa wannan yarinyar magana umma hardafa ƙwaɗomin cokali".
NafaÉ—a ina nuno ummi dake kicin a zaune tana faman juya dankalin.
Murmushi umma tayi gami da cewa.
"Hmm kunfi kusa".
Tana kokarin shigewa tace wa ummi.
"ki kwantar da hankalinki ummi gobe iyanzu tana kokarin wucewa fa gidanta".
Tana gama faÉ—in haka tai É—akin abbanmu.
Ummi bata ce komai ba. nikuwa ɗakin umma na shige ina tura baki gaba tare da ƙoƙarin in zubo da ƙwalla.
Agaban madubin umma na tsaya tare da tube rigar jikina.
Zanin rigar naja na É—agoshi saman kirjin nawa.
Sannan na saka hannuna na tube brata, É—an zame zanin jikin nawa nai kaÉ—an.
tare da tsirawa kirjina idanu.
Wata ƙwallar takaici ce tazomin ganin yadda saman yayi jaa kaɗan wallahi muguntar daya min ce jiya tasaka abuna yay haka.
Kallo nabi sa dashi babu ta inda mutum zece min abina yay kama dana ɓera duba da yadda yake acike tam tsam kamar ze tsagamin kirjina gashi a tsaye yake babu ta inda ya ranƙwafa.
Irinsa ake cewa mai ƙasan tasa amman shine wannan mai fuska kamar ta tumatur ɗin ze wani cemin mai kirji kamar na ɓera.
Cikin banɗakin umma na shiga ruwa mai zafi na haɗa tare da ƙarasa zame zanin jikin nawa na soma wanka.
Fatar jikina ruwa baya tsayawa akanta sabida yadda take sheƙi kamar ta tarwaɗa gami da santsi ni kaina jin dadin yadda fatar jikin nawa tayi nake.
Ina gama wankan na fito na saka towel na goge jikina dashi sannan na dauki man shafawa na soma shafawa kwalli na zizara tare da fita waje.
ÆŠakinmu na koma na É—auko doguwar riga na saka sannan na kuma komawa É—akin umma tsayawa nai agaban madubi ina duba zubi da tsarin halitta ta tare da godewa, sarki buwayi gagara misali.
Babu laifi ni dai baza,a sakani ajerin mata masu tsahoba amman kuma bana daga cikin jerin gajeru ina da ƙiba dai dai misali wadda tabi jikina ta murjeni.
Kirjina acike yake sosai sannan kuma.mazaunai na suma suna da cika dai dai misali.
Ni baƙa ce sosai domin bani da haske kona misali.
Ina da idanu manya masu haske sannnan hancina ba dogo bane bakina yana da É—an tudu irin na tsiwa da rashin kunya.
Ina da cikar gashin ka babu laifi danni ba ƙwaƙwido bace ba.
Sam bana kama dasu ummi ni bamma san kamannin wa nayo agidanmu ba gwarama baƙar fatar wannan ta abbanmu ce.
Amman kyau kam su ummi duk sun fini musamman ma amira wadda takasance kamar jinin larabawa.
Haka xalika su hanif dasu ummi duk fararene nice kaɗai baƙa.
Shiyasa idan ya hydar namin ba,a har kuka nake.
Dan shikam narasa wannan tsananin kyau irin nasa wanda idan ina kallonsa har raina kyan kowa nake.Aɓangaren hali kuwa zance ni batula bani da ɗaukar raini sannan kuma bani da hakuri ina da ƙiwar aiki gani da son jiki amman ina da raunin zuciya gami da shagwaɓa, ina da son ƴan uwana da mahaifiyata sannan ina da riƙon abu ban fiye mantuwaba shiyasa duk abin da momy taiwa umma yake kaina ban manta ko guda ba.
Umma data shigo yanzu itace ta katsemin tunanina tare da cewa.
"Maza kije part É—in yayanku ki gyara musu shi dan abbanku yace su taho nan kada su kuma kwana a hotel É—innan kafin goven ku wuce can É—in.......!!!
Chapter 19 · 0% Book details