← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 58

Sashe 58

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Satinmu É—aya muka koma sabon gidanmu wanda muka dauki sabon fejin soyayya nida yayana wanda na yarda yana sona bil haqqi da gaskiya.

Momy wata kulawa take bani ta musamman wadda bata iya sati guda batare datazo taga yadda mukeba dayake cikin nawa mai É—an banxan laulayine wataran haka yaya ze tare gabana yay ta min kuka musamman idan ina maka amai.

BAYAN WASU WATANNI

Cikina yay girma ga yaya an kuma kara masa girma yanxu daga wancan gari se wacan haka su rauda suke zuwa tayani kwana wanda baki É—aya ansaka ranar bikinsu harsu ummin gidanmu duk qarshan wannan shekarar zasu É—aga.

Ranar wata laraba ina kwance naji kamar an soken a marata wasa wasa ciwo yacigaba zuwa dare ciwo yay karfi seda rauda ta kula ta kira momy wadda tazo a kidime itada mama, sukai mota dani cikin lokaci kaÉ—an mukai asibiti.

Nakuda kadan nai na haifi Æ´ata mace mai kama dani sak hatta bakin fatar nawane adaran yaya ya dawo yatarar damu acikin asibitin haka ya hadeni da bebyn ya rungume yana murna.

Gidan momy muka dawo da zama faÉ—in irin yadda matar take bani kulawama bata bakine ranar suna yarinya taci *Zainab* sunan momy sosai momy ta rungumeni nida hanifa yar bebyn tawa tana kukan farin ciki marar misaltuwa.

Haka nacigaba da wankana agidan momy bayan arba'in muka daga kano acan nai sati biyu muka dawo gida.

BAYAN SHEKARA BIYU!

Abubuwa sun faru masu yawan gaske daga ciki harda bikinsu rauda tare da rasuwar iya da baba da karin samun É—a namiji danai mai sunan abbana.

Yau tun safe nake zaune bana jin dadi ga mai sunan abba yana damuna da kuka.

Habi mai aikina ce taxo ta shaida min nai baki ce mata nai tace su shigo ciki.

Sallamar wata mace fara cikin gayu bayanta wani namijine daga gani mijinta ne yasa na qara far,ar fuskata na miqa mata little abba nikuma nai ciki kayan sha dana ci na hado masu na aje seda suka huta sannan nace ban ganesu ba?

Matar ce ta kakaro murmushi sannan tace "daman baxaki ganeni ba fatima to maryam ce matar hydar tada" cike da firgici na miqe sannan na koma wajanta na rungumeta na fashe da kuka!

Itama kukan take kan jiki kan qarfi tare da cewa "fatima ki yafan wallahi bayan zamana gidan yari naga rayuwa wanda bada ban hydar yayi shige da fice ba da baxan koma gida ba dan ALLAH kiyiwa hydar godiya da irin yadda ya shiga ya fita harna bar gidan yarin sannan ya miqani ga iyayena akan shidai baxe mayar dani É—akinshiba sedai kuma duk abin da nai masa ya yafemin tabbas samun miji kamar hydar se antona"

"Bayan dawowata gida naga rayuwa wadda tabani darasi da dama ta sauyani wanda na koma makaranta anan ALLAH ya hadin da ABDUL Likitan mahaifina labari na basa sosai kan rayuwata anan yake bani shima labarin irin tasa rayuwar sena gane ashe kece fatiman dayaso ALLAH bai ba yanxu haka tare muke dashi gashinan zaune yace yana qara neman yafiyarki ALLAH kuma yay wa mahaifinshi rasuwa nima yanxu haka watanmu uku da aure dashi, munje wajan momy na bata haquri kuma sun shirya da mamy mahaifiyata daman kece ta qarshe tunda hydar sunyi waya da abdul yace baya gari shine ma yay mana kwatancan nan É—in" takai maganar tana kallon hanifa wadda ta fito hannunta dauke da bobo tana sha.

Komai tsayamin yay araina nan dan naji wata irin nutsuwa ta shigen hm duniya kenan sakinta nai na zauna na kalli abdul wanda yaketa wasa da litle abba a hannunshi sannan nace mata ni kam komai ya wuce awajena haka mukaita hira da ita wanda da qyar na sake da abdul shima muka gaisa amman cikin raina mamakin zurfin ciki yaya nake wanda duk wannan budurin bai gayan ba lallai yaya.

Har dare suna nan haka na shirya masu dinner bayan sunci mukai sallama na rakasu har bakin gate wanda na lura maryam hankalinta yana kan hanifa wadda itama ta maqale mata fafur nai nai da hanifa akan ta saki anty maryam amman taqi haka nakoma gida na barsu musu ita suka tafi da ita gidansu dake asokoro area 3.

Koda na koma gida naiwa yaya waya na sanar masa azatona ze faÉ—a amman senaga yanata dariya tsiya nai masa akan yadda ya rufeni aduk wannan budurin dasukai da anty maryam abinda kawai yacemin shine ai duk abinda kai dan ALLAH tobase ka gayawa kowa ba indai ubangijin ya gani.

Rayuwa me kyau mukeyi nida yaya wanda yanxu haka zumunci muke nida anty maryam wadda taxama kamar yayata afaÉ—in garin abuja dan banida kamarta haka zalika yaya yaxama aminin abdul sosai suke abota.

Babu abinda zance da ALLAH se godiya sabida yanxu komai ya zama tarihi zamana da uwar mijin son barka da Æ´an uwansa ma haka haka zalika mahaifana waÉ—anda suke alfahari dani sosai.

TAMMAT BIHAMDIHI🙏
Chapter 58 · 0% Book details